An Kashe Yaran Sheikh Ibrahim Khalil a Benue, Gwamnan Kano Ya Yi Magana Mai Zafi

An Kashe Yaran Sheikh Ibrahim Khalil a Benue, Gwamnan Kano Ya Yi Magana Mai Zafi

  • Gwamna Abba Kabir Yusuf ya yi Allah-wadai da kisan gillar da aka yi wa wasu matasan Kano biyu biyu a Makurdi, babban birnin Benue
  • Gwamnan ya tabbatar da cewa gwamnati za ta yi aiki tuƙuru don ganin an kama tare da hukunta waɗanda suka aikata wannan kisan
  • Ya bayyana cewa Najeriya ta kowa ce, kuma kowane ɗan ƙasa yana da 'yancin rayuwa da aiki a kowane yanki ba tare da wata bargaba ba

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Kano - Ana zargin bata gari sun yi wa wasu matasa biyu 'yan asalin jihar Kano kisan gilla a Makurdi, babban birnin jihar Benue.

An rahoto cewa, matasan, Barhama Suleiman da Jamilu Ahmad sun gamu da ajalinsu ne lokacin da suka tsaya shan shayi a Makurdi.

Gwamnatin Kano ta yi martani mai zafi da aka kashe wasu matasan jihar 2 a Benue
Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf tare da Sheikh Ibrahim Khalil. Hoto: Sanusi Bature D-Tofa
Asali: Facebook

Wani rahoto da aka wallafa a shafin Facebook na Hikima Radio and TV ya nuna cewa wasu fusatattun matasa ne suka sassari 'yan Kano har lahira, saboda suna kama da Fulani.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Abba ya yi martani kan kisan Kanawa a Benue

Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf ya yi Allah-wadai da irin wannan kisan gillar da aka yi wa Barhama Suleiman da Jamilu Ahmad a Makurdi.

A cikin wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan, Sanusi Bature Dawakin Tofa ya fitar a shafinsa na Facebook, Gwamna Abba ya ce an kashe matasan a ranar Litinin, da karfe 11:00 na dare.

A cikin kalamansa masu cike da bakin ciki da bacin rai, gwamnan Kano ya bayyana wannan kisan a matsayin "kisan rashin imani, wanda ba za mu lamunta ba."

Ya jaddada Allah-wadansa a kan kisan matasan, yayin da ce gwamnatin Kano za ta yi duk mai yiwuwa don ganin an kama wadanda suka yi kisan tare da hukunta su.

"Cikin bakin ciki muke sanar da mutuwar 'ya'yan Kano biyu. Ba su ji ba, ba su gani ba, aka kashe su. Laifinsu daya ne, sun yi amfani da 'yancin da doka ta ba su na yin rayuwa da aiki a kowanne yanki na Najeriya."

- Gwamna Abba Yusuf.

Abba ya yi alkawarin nemawa matasan adalci

An rahoto cewa gwamnan ne da kansa ya jagoranci babbar tawaga, ciki har da iyalan wadanda aka kashe, zuwa Abuja, inda aka yi jana'izar matasan a masallacin kasa a yau (Talata).

Yayin da yake mika ta'aziyya ga iyalan wadanda aka kashe, gwamnan ya kuma jajanta da babban malamin Musulunci, Sheikh Ibrahim Khalil, wanda shi ne mahaifin duka matasan biyu.

Gwamna Abba Kabir ya yi alkawarin yin duk mai yiwuwa don kamo wadanda suka kashe matasan Kano a Benue
Gwamnan jihar Kano, mai girma Abba Kabir Yusuf. Hoto: @Kyusufabba
Asali: Twitter

Gwamna Abba Yusuf ya bayyana wannan lamari a matsayin babban rashi ga iyalan, da jihar Kano da ma kasa baki daya.

Sanarwar ta kara da cewa:

"Wannan gwamnatin ba za ta huta ba har sai ta nemawa matasan adalci. Muna fatan za a kwantar da hankula yayin da muke aiki da jami'an tsaro da gwamnatin Benue don hukunta makasan.
"Najeriya ta kowa ce. Kowane dan kasa yana da 'yancin ya yi rayuwa, ya yi zirga-zirga, ya kuma yi kasuwanci a ko ina ba tare da fargabar nuna wariya ko barazana ba."

Gwamnatin Kano ta ba da tabbacin kokarin da take yi na kare rayuka da dukiyoyin al'ummarta, a duk inda suke rayuwa.

Karanta sanarwar a nan kasa:

Kano: An mutu wajen tsamo waya daga masai

A wani labarin, mun ruwaito cewa, Mutane biyu, Usman Muhammed da Ibrahim Inuwa, sun rasu a Kano yayin da suke ƙoƙarin tsamo wayar salula da ta faɗa a cikin masai.

Hukumar kashe gobara ta tabbatar da wannan lamari, inda ta bayyana cewa iskar gubar da suka shaka daga masan ita ce sanadin mutuwarsu.

Wannan ba shine karo na farko da irin wannan lamarin ke faruwa a Kano ba, mutane da dama sun rasa rayukansu a irin wannan ƙoƙari na tsamo waya daga masai.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.