Dalilai 3 da Suke Sa Aure tsakanin Jaruman Kannywood ke Yawan Jawo Ce Ce Ku Ce

Dalilai 3 da Suke Sa Aure tsakanin Jaruman Kannywood ke Yawan Jawo Ce Ce Ku Ce

A watan Afrilu, 2025 ne masana'antar shirya fina-finan Hausa watau Kannywood ta sake shaida ɗaurin auren jarumanta wanda ya ja hankalin jama'a a Najeriya.

Fitaccen mawakin nan da tauraruwarsa ke haskawa, Dauda Adamu Abdullahi wanda aka fi sani da Dauda Kahutu Rarara ya angonce da Jaruma Aisha Humaira.

Lilin Baba da Dauda Kahutu.
Yadda auren jarumar Kannywood ke tayar da kura a Najeriya Hoto: Lilin Baba, Dauda Kahutu Rarara
Asali: Facebook

An ɗaura auren Rarara da Aisha Humaira ne a ranar Juma'a, 25 ga watan Afrilu, 2025 a Maiduguri, babban birnin jihar Borno, kamar yadda Leadership ta rahoto.

Wannan shagalin biki dai ya ja hankulan ƴan Najeriya musamman liyafar cin abinci da aka shirya da kuma ganin irin manyan ƴan siyasar da suka halarci bikin.

Wasu daga cikin auren ƴan Kannywood

Wannan ba shi ne karo na farko a bikin aure a tsakanin jaruman Kannywood ke jan hankali ba, domin galibi ƴan Arewa na yawan ce-ce-ku-ce kan rayuwar jaruman fim.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A wannan rahoton, Legit Hausa ta tattaro muku wasu daga cikin aurarrakin da aka yi a Kannywood da kuma dalilan da ke yawan haifar da ce-ce-ku-ce a kansu.

1. Rarara da Aisha Humaira

An daɗe ana jita-jitar cewa akwai soyayya mai karfi tsakanin Dauda Kahutu Rarara da Aisha Humaira duba da yadda suke aiki tare da kulawar da suke ba junansu.

Sai dai duk lokacin da aka tambaye su kan ko akwai alaƙar soyayya a tsakaninsu, su kan ce aiki ne yake haɗa su amma akwai shaƙuwa a tsakaninsu.

Dauda Kahutu Rarara da Aisha Humaira.
Yadda auren jaruman Kannywood ke jan hankalin jama'a Hoto: Dauda Kahutu Rarara
Asali: Facebook

A wata hira da Aisha Humaira ta yi a cikin shirin da Hadiza Gabon ke watsawa a Youtube, ta ce Rarara amininta ne kuma maigidanta ne.

Kwatsam a ranar Juma'a, 25 ga watan Afrilu, 2025 aka ɗaura auren Rarara da Aisha, lamarin da ya ja hankali sosai musamman a kafafen sada zumunta.

2. Maishadda da Hassana Muhammad

Ɗaura auren fitaccen Furodusa a Kannywood, Abubakar Bashir Maishadda na ɗaya daga cikin bukukuwan da suka ɗauki hankali.

Abubakar Maishadda ya auri jaruma Hassana Muhammad, wacce ta fito a fina-finai da dama ciki har da waɗanda angonta ya shirya.

An ɗaura aurensu ne a ranar Lahadi, 13 ga watan Maris na shekarar 2022 a Masallacin Murtala da ke jihar Kano, kamar yadda Daily Trust ta kawo.

3. Ummi Rahab da Lilin Baba

Mawaƙi kuma jarumi a Kannywood, Shu'aibu Ahmed Abbas, wanda aka fi sani da Lilin Baba ya auri Ummi Rahab a ranar Asabar, 18 ga watan Yuli, 2022.

Wannan biki ya tayar ƙura musamman da aka fara zargin Ummi Rahab da juyawa wanda ya raine ta a Kannywood, Adam A. Zango baya.

Lilin Baba da Ummi Rahab.
Auren Lilin Baba da Ummi Rahab ya tayar da ƙura a ciki da wajen Kannywood Hoto: Lilin Baba
Asali: Facebook

A lokacin da zancen auren ya taso an yi ta raɗe-raɗin cewa Adam Zango ya nuna ba ya so, amma duk da haka an ɗaura auren kuma Ummi da Lilin Baba na ci gaba da zamansu na aure.

Waɗannan da ma wasu aurarrakin da aka yi a Kannywood, kamar na Sani Danja da Mansurah Isah da Fati Muhammad da Sani Mai Iska sun ja hankali amma su waɗannan auren ya mutu daga baya.

Dalilan ce-ce-ku-ce a auren ƴan Kannywood

Auren jaruman Kannywood na yawan tayar ƙura a kusan kowane lokaci, tun daga shagalin biki, da tarukan murna da aka shirya.

A Arewa, al'adu da addini na da muhimmanci a kowace auratayya, mun tattaro maku wasu daga cikin dailin da ke jawo ce-ce-ku-ce game da auren ƴan Kannywood.

1. Yawaitar jita-jita

A Arewacin Najeriya, jita-jita da kage sun fi yaduwa fiye da gaskiya, ko kafin bikin aure ya ƙare, wasu na iya fara yaɗa jita-jitar cewa “sun rabu.”

Kannywood ba ta tsira daga irin waɗannan ba domin a wasu lokutan tun kafin a ɗaura aure, mutane ke fara bincike don gano aibun jaruman matuƙar aka san suna soyayya.

Jarumai mata sun fi fuskantar irin waɗannan matsaloli daga jama'a, kamar bankaɗo tarihin rayuwarsu musamman idan aka ce jarumar ta taɓa aure.

2. Bikin ƙasaita da kashe kuɗi

A duk lokacin da ƴan Kannywood za su yi aure, mutane na zuba ido su ga wane irin biki za a shirya na kece raini da irin kuɗin da za a kashe.

Wannan yana matuƙar jan hankalin masu bibiyar harkokin jaruman Kannywood kuma yana haifar da ka-ce-na-ce a shafukan sada zumunta.

Alal misali a bikin Rarara da Aisha Humaira, mutane sun yi ta surutu tun daga akwatunan da ango ya yi da kuɗin da aka kashe a liyafa da sauran tarukan murna.

Yayin da wasu ke ganin mawaƙin da ita kanta amaryar suna da sararin yin fiye da haka, wasu kuma sun soki lamarin saboda halin da ake ciki a Arewa.

3. Auren fitattun jarumai a Kannywood

Idan jaruman da suka shahara suka yi aure, galibi jama'a na sa wa duk wani motsinsu ido tun daga tufafin da suke sa wa, zuwa hoton da suka dora, ko ma adon da nace za ta riƙa yi.

Sannan da an yi auren mutane za su fara sa ido su ga shin matar za ta daina shiga fim, ko mijin zai bar ta ta ci gaba, waɗannan na daga cikin abubuwan da mutane ke bibiya.

A wasu lokuta, an sha ganin yadda auren jarumai ke karewa da saki watau rabuwa da kuna, wanda za ka ga jama'a sun nuna abin bai masu daɗi ba.

Misali auren Sani Danja da Mansurah Isah, dukansu fitattun jarumai ne da ke jan zarensu a Kannywood lokacin da suka yi aure.

Tun kafin auren jaruman aka fara yaɗa maganganu iri-iri musamnan yadda Sani Danja ke tashe da kuma yadda yake d alaƙa da wasu matan a Kannywood.

Bayan sun rabu mutane sun riƙa sukar Mansurah Isah tare da kiranta da sunaye marasa daɗi har da aka kaita bango, ta mayar da martani.

A rahoton da Premium Times ta wallafa, Mansurah ta bukaci jama'a su fita daga rayuwarta domin ba ita ce mace ta farko da aurenta ya mutu ba.

Jarumi Sadiq ya ce ba tarbiya suke koyarwa ba

A wani rahoton, kun ji cewa fitaccen jarumi a masana’antar Kannywood, Sadiq Sani Sadiq ya neman kudi ya sa yake harkar fim ba koyar da tarbiyya ba.

Sadiq ya bayyana cewa tarbiyya daga gida take fitowa sai kuma malamai da ke wa'azantarwa amma ƴan fim ba.

Sadiq ya kuma bayyana cewa bai da ubangida a harkar fim amma akwai wasu da ya ke ganin girmansu matuka a masana'antar.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262