Kannywood: An Fadawa Bashir Maishadda Jarumar da Zai Cire a Shirin Jamilun Jidda
- Masu kallon Jamilun Jidda sun bukaci a cire Firdausi Yahaya, tare da maye gurbinta da Humaira a matsayin diyar Farfesa Inde
- An bukaci mai shirya shirin, Abubakar Bashir Maishadda da ta sauya jarumar idan har yana yin shirin ne don nishadin masu kallo
- Wannan na zuwa ne yayin da aka karrama Firdausi da kambun "Jaruma Mai Tasowa" a bikin ba da lambobin yabo na Pandora a Kano
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Kano - Masu kallon fina-finan Hausa sun bayyana ra’ayoyinsu kan sabon shirin Jamilun Jidda na furodusa, Abubakar Bashir Maishadda.
Sun roƙi a cire jaruma Firdausi Yahaya daga cikin shirin, tare da bada shawarar a saka jaruma Humaira (wadda take fitowa a shirin Matar TikTok).

Asali: Instagram
Wani ma'abocin Facebook, Nazeefi Ibraheem Yareema ya wallafa a shafinsa cewa suna so a maye gurbin Firdausi da Humaira domin karin karsashin shirin.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
An nemi a cire Firdausi daga Jamilun Jidda
Nazeefi na ganin cewa Huamira ta fi Firdausi kwarewa wajen taka rawar masifa da kishi, musamman a matsayin diyar Farfesa Inde a shirin Jamilun Jidda.
Masu kallo sun bayyana cewa shirye-shiryen fina-finai ana yi ne don su, don haka dole ne a zaɓi jaruman da suka dace domin biyan bukatunsu.
A cewarsu, Humaira ce tafi dacewa da rawar saboda halayenta na nuna kishi a cikin fina-finai daban-daban da ta taka rawar gani.
Nazeefi ya wallafa cewa:
"A gaya ma Maishadda ya cire mana wannan yarinyar a cikin shirin Jamilun Jiddan ya sako mana Humaira, ta fi iya acting masifa da kishi kuma tafi dacewa da diyar prof Inde saboda mu yan kallo ake shirin."
Firdausi Yahaya ta lashe kambun Pandora
Duk da wannan ce-ce-ku-ce, Firdausi Yahaya ta kasance daya daga cikin jaruman da suka yi fice a masana’antar Kannywood daga shekarar 2024.
Ta taka rawar gani a fina-finan Kannywood da dama da suka haɗa da Garwashi, Matan Gida, da kuma zangon Manyan Mata mai fitowa.
A farkon shekarar 2025, an karrama Firdausi Yahaya da kambun "Jaruma Mai Tasowa" a bikin ba da lambobin yabo na Pandora, wanda aka gudanar a Kano.
Wannan nasarar ta ƙara mata daraja a idon masana’antar da kuma magoya bayanta.
Masana'antar Kannywood tana da rawar gani wajen samar da nishaɗi da ilmantarwa ga jama’a, kuma jarumai kamar Firdausi Yahaya suna taka muhimmiyar rawa wajen tabbatar da hakan.
Finafinan Kannywood da za a haska a 2025
Tun da fari, mun ruwaito cewa Jamilun Jidda na fitaccen mai shirya fina-finai Bashir Maishadda na daga cikin finafinan da za a haska a 2025.
A shekarar 2024 aka kammala daukar Jamilun Jidda kuma aka fara haska shi a 2025 kamar yadda aka fara haska shirin Manyan Mata, Gidan Badamasi da sauransu.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng