Sojojin Najeriya Sun Nuna Bajinta a Duniya wajen Bikin 'Yancin Kasar Kamaru
- Babban hafsan tsaron Najeriya, Janar Christopher Musa, ya jagoranci tawaga zuwa bikin cikar Kamaru shekaru 53 da samun ‘yancin kai a Yaoundé
- Sojojin Najeriya ne kaɗai suka samu damar yin fareti cikin 'yan kasashen waje, inda suka ja hankalin jama'a da suka nuna kwarewa a wajen taron
- Wannan ziyara ta nuna karfin dangantaka tsakanin Najeriya da Kamaru, musamman a fannin tsaro da zaman lafiya a yankin Yammacin Afrika
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
FCT, Abuja - Najeriya ta samu yabo a idon duniya yayin da sojojinta suka haskaka a bikin cikar Kamaru shekaru 53 da samun ‘yancin kai.
Rahotanni sun nuna cewa an gudanar da bikin ne a ranar Talata, 20 ga Mayu 2025, a birnin Yaoundé.

Asali: Twitter
Zagazola Makama ya wallafa a X cewa bikin ya gudana ne karkashin shugaba Paul Biya na Kamaru kuma manyan jami’an gwamnati sun halarci taron.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Babban Hafsan Tsaron Najeriya, Janar Christopher Musa ne ya jagoranci tawagar sojojin Najeriya zuwa bikin, inda suka nuna bajinta da ƙwarewar soja da ta burge mahalarta.
Sojojin Najeriya sun burge duniya a Kamaru
Daga cikin abubuwan da suka fi jan hankali a wajen bikin akwai nuna bajinta da dakarun Najeriya suka yi, wanda su ne 'yan ƙasashen waje kaɗai da suka samu damar yin hakan.
Sojojin sun ja hankalin dubban jama'a da ke wajen bikin ta hanya fareti, kida, da tsare-tsaren soja da suka nuna ingancin horonsu da kwarewarsu.
Hakan ya jawo tafi da jinjina daga manyan baki, tare da nuna girmamawa ga Najeriya da karfafa dangantakar dakarun ƙasashen biyu.

Asali: Twitter
Ziyarar ta karfafa alaƙar Najeriya da Kamaru
Bikin ya zama wani dama da Najeriya ta sake bayyana niyyarta na ci gaba da haɗin gwiwa da Kamaru da sauran ƙasashen makwabta wajen yaki da matsalolin tsaro da karfafa zaman lafiya.
Janar Musa ya bayyana farin cikinsa bisa yadda aka tarbe su da mutunci da martaba, yana mai tabbatar da cewa Najeriya za ta ci gaba da zama abokiyar hulɗa ta kwarai.
Ya jaddada cewa haɗin gwiwa a fannin tsaro da diflomasiyya zai taimaka wajen kawo zaman lafiya da ci gaban al'umma a yankin.
Bikin ya nuna ƙwazon dakarun Kamaru
Bikin ya hada da faretin soja, baje kolin makamai da kayan aikin tsaro, da sauran ayyukan da suka nuna haɗin kai daga sassa daban-daban na ƙasar.
Wannan ya nuna yadda Kamaru ke ƙoƙarin haɗa kan jama’arta tare da gina ƙasa mai cike da zaman lafiya da cigaba.
Janar Musa ya gana da dakarun Rasha
A wani rahoton, kun ji cewa hafsun tsaron Najeriya, Janar Christopher Musa ya gana da dakarun Rasha.
Legit ta wallafa cewa taron ya mayar da hankali kan kan kyautata alakar tsaro da yaki da ta'addanci.
Rahoton bayan taron ya nuna cewa kasar Rasha ta tabbatar wa Janar Musa cewa za ta cigaba da tallafawa Najeriya wajen yaki da 'yan ta'adda.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng