'Ni na Biya Ka a Fim': Fitaccen Furodusa Ya Kalubalanci Soja Boy kan Ɓaram Ɓaramarsa

'Ni na Biya Ka a Fim': Fitaccen Furodusa Ya Kalubalanci Soja Boy kan Ɓaram Ɓaramarsa

  • Fitaccen furodusa Abdulaziz Dan Small ya karyata ikirarin Soja Boy kan cewa babu wanda ya taba biyansa a masana'antar Kannywood kan aikinsa
  • Dan Small ya bayyana cewa ya taba ba Soja Boy kudi sau biyu, har ma ya kara masa kudi a matsayin taimako cikin mutunci
  • A cikin wata bidiyo, Dan Small ya ce yana da shaida cewa ya taba biya wa Soja Boy kudin hotel har N200,000 da N100,000

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Kano - Fitaccen furodusa a masana'antar Kannywood, Abdulaziz Dan Small ya yi martani kan kalaman Soja Boy.

Furodusan ya kalubalanci jarumin musamman kan cewa babu wanda ya taba biyansa a masana'antar kan yi masa aiki.

Furodusa a Kannywood ya kalubalanci Soja Boy kan kalamansa
Abdulaziz Dan Small ya tona wa Soja Boy asiri kan alfaharin da ya yi. Hoto: Usman Soja Boy Yarima, Abdulaziz Dansmall.
Asali: Facebook

An dakatar da Soja Boy daga Kannywood

Dan Small ya yi wannan martani ne a cikin wani faifan bidiyo da shafin Arewa Beauty ya wallafa a Facebook.

Kara karanta wannan

Dogara ya tona asirin 2019: "Yadda Wike ya taimaki Bala ya zama gwamnan Bauchi a PDP"

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wannan ya biyo bayan bugan kirji da Soja Boy ya yi cewa ya yi fina-finai da yawa amma taimako kawai ya ke yi saboda yana da kudi a aljihunsa.

Soja Boy daga bisani ya jero fina-finai da ya yi masu yawa inda ya ce ko kudin hotel shi ke biya wa kansa.

Mawakin ya fadi hakan ne bayan dakatar da shi a masana'antar da aka yi inda ya ce daman bai dogara da ita ba.

Dan Small ya fusata da kalaman Soja Boy

Sai dai furodusa, Dan Small bai ji dadin maganganun ba inda ya kalubalance shi game da kalamansa.

Dan Small ya ce sun yi aiki ya biya masa kudin hotel har sau biyu kan N300,000 kuma ya ba shi N50,000 ya kara mai.

Furodusan ya ce abin takaici ne Soja Boy ya fito ya fadi haka duk da sun yi alakar ce cikin mutunci da mutuntawa a wancan lokaci.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Kano ta yi kuskuren ingiza wa wani jami'inta maƙudan kuɗi, ya dawo da su

"Assalamu Alaikum, sunana Abdulaziz Dan Small, n ji bayanin Soja Boy kan masana'antar Kannywood."
"Ya ce duk wanda ya taba daukar kudi ya ba shi idan akwai ya daga hannu, to ni na daga hannu."
"Ni na taba ba shi kudi a fim din Barauniyar Amarya wanda kuma da kansa ya fadi fim din a cikin fina-finan da ya yi."

- Abdulaziz Dan Small

Alherin Dan Small ga jarumi Soja Boy

Furodusan ya tabbatar da cewa sun yi aiki a lokacin cikin mutunci da mutuntawa amma bai ji dadin abin da ya ji ba.

"Farkon zuwansa ya min kwana hudu na dauki N200,000 na bayar a matsayin kudin hotel."
"Na biyu, ya sake dawowa ya min kwana biyu na dake ba shi N100,000, sannan ranar da zai tafi na dauki N50,000 na bashi na ce Soja Boy ka kara mai."

- Abdulaziz Dan Small

An shawarci a sauya jarumar fim

Kara karanta wannan

Shugaba a Izala ya sha rubdugu yayin bayani kan bikin 'Qur'anic Festival'

Kun ji cewa masu kallon Jamilun Jidda sun bukaci a cire Firdausi Yahaya, tare da maye gurbinta da Humaira a matsayin diyar Farfesa Inde.

An bukaci mai shirya shirin, Abubakar Bashir Maishadda da ta sauya jarumar idan har yana yin shirin ne don nishadin masu kallo.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.