Gwamnatin Abba Za Ta Magance Matsalar Ruwa, An Fitar da Biliyoyi domin Noman Rani

Gwamnatin Abba Za Ta Magance Matsalar Ruwa, An Fitar da Biliyoyi domin Noman Rani

  • Gwamnatin Kano ta bayyana shirin bunkasa ayyukan noma ta hanyar gina katafariyar madatsar ruwa a yankin Dansoshiya
  • Hadimin gwamnan a kan yada labarai, Ibrahim Adam ne ya bayyana haka, inda ya ce an ware sama da Naira biliyan shida domin aikin
  • Ana sa ran wasu kananan hukumomi za su fi cin moriyar aiki, manoma kusan 3,000 ne ake sa ran za su fara ban ruwan zamani a madatsar

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Kano – Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf, ya amince da ware N6.8bn domin aikin gina madatsar ruwa a Dansoshiya wanda zai samar da lita biliyan uku na ruwa.

A cikin kudin, za a samar da ababen more rayuwa da samar da wurin noman ban ruwan noman rani a karamar hukumar Kiru da ke jihar.

Gwamna
Gwamnatin Abba za ta gina dam a Dansoshiya Hoto: Sanusi Bature D-Tofa
Asali: Facebook

Wannan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da Ibrahim Adam, mai ba gwamnan shawara na musamman kan harkokin yada labarai, ya wallafa a shafinsa na Facebook.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya bayyana cewa aikin, wani bangare ne na kudirin gwamnatin jihar na bunkasa harkar noma da kuma tabbatar da isasshen abinci ga al’ummar jihar da ma kasa baki daya.

Gwamnatin Kano za inganta noman rani

A cikin wata cikakkiyar sanarwa da Adam ya fitar zuwa manema labarai a Kano, wanda Legit ta gani, Ibrahim Adam ya bayyana cewa Kiru da Bebeji su ne za su fara cin moriyar aikin.

A cewar hadimin gwamnan, amma tasirin aikin zai watsu zuwa dukkannin kananan hukumomi 44 na jihar Kano.

Gwamna
Ana sa ran manoman Kano kusan 3,000 za su ci moriyar madatsar ruwan Hoto: Abba Kabir Yusuf
Asali: Facebook

Ya ce:

“Jihohin Najeriya ma za su amfana daga karuwar amfanin gona da kuma kirkirar tsarin noma na zamani, irin yadda ake gani a kasuwar shinkafa ta Kura da cibiyar noma ta Gafan.”

An shirya gina dam a jihar Kano

Da zarar an kammala dam din Dansoshiya, ana sa ran za ta rike lita biliyan 3.1 na ruwa, kuma an ware kimanin hektar 1,000 na filin noma domin amfani da tsarin ban ruwa.

Ibrahim Adam ya kara da cewa za a fara aikin ban ruwan noman ranin da kadada 500 a matakin farko, kafin a kara bunkasa aikin.

Ya bayyana cewa tsakanin manoma 1,000 zuwa 3,000 ake sa ran za su amfana kai tsaye daga wannan shiri a matakin farko kadai.

Ya ce:

“Wannan tsari ba zai tsaya kawai ga taimaka wa manoma ba, zai kara yawan amfanin gona, samar da ayyukan yi, da kuma bunkasa tattalin arzikin jihar gaba daya.”

Gwamnatin Kano ta ce wannan wani babban bangare ne na aiwatar da manufofin cigaban jihar da kuma tabbatar da cewa noma ya koma matsayin ginshikin ci gaban tattalin arziki.

Gwamnan Kano ya ji koken jama'a

A baya, kun ji cewa gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf, ya ba da gudunmawar kayan abinci da na more rayuwa ga fursunoni da ke manyan cibiyoyin gyaran hali guda uku dake fadin jihar.

Ya kai taimakon ga cibiyoyin gyaran hali na Kurmawa, Janguza da Goron-Dutse a kokarin gwamnatinsa wajen kyautata rayuwar mutanen dake tsare saboda laifuffuka da dama.

An gabatar da tallafin ne a hukumance a Kurmawa, inda Kwamishinan Harkokin Jin Kai da Rage Talauci, Hon. Adamu Aliyu Kibiya, ya wakilci Gwamna Abba Kabir Yusuf.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.