Trump Ya Hana Netanyahu kai Hari Lebanon bayan Waya da Hezbollah
- Shugaban Amurka, Donald Trump, ya ce ya shawo kan Firaministan Isra’ila, Benjamin Netanyahu, kada ya tura sojoji zuwa Kudancin Beirut
- Kiran wayar da aka yi tsakanin shugabannin Amurka da Isra’ila ya zo ne bayan Dakarun Juyin Juya Halin Musulunci na Iran sun yi barazanar kin yarda da sulhu
- Rahoto ya nuna cewa Iran ta sanar da Trump cewa za ta ci gaba da rufe mashigar Hormuz saboda hare-haren da Isra’ila ke kai wa a Lebanon
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
America - Shugaban Amurka, Donald Trump, ya ce ya yi magana da kungiyar Hezbollah ta Lebanon mai alaka da Iran ta hannun masu shiga tsakani, kuma ya samu alkawarin cewa ba za ta kai hari kan Isra’ila ba.

Source: UGC
Trump ya ce ya kuma tattauna da Firaministan Isra’ila, Benjamin Netanyahu, kuma Isra’ila ta amince da janye duk wasu sojojin da suke shirin kai hari Kudancin Lebanon.
Trump ya yi waya da Lebanon, Isra'ila
A wani sako da Fox News ta wallafa a X, shugaban Amurka ya tabbatar da cewa ya yi magana da bangarorin Lebanon da Isra'ila.
Trump ya ce:
“Na yi wata tattaunawa mai matukar amfani da Firaminista Bibi Netanyahu na Isra’ila, kuma ba za a tura sojoji zuwa Beirut ba, yayin da duk sojojin da suke kan hanyarsu tuni aka mayar da su baya,”
“Haka kuma, ta hannun wasu manyan wakilai, na yi kyakkyawar tattaunawa da Hezbollah, kuma sun amince cewa za a dakatar da dukkan harbe-harbe.”
Rahoton Reuters ya nuna cewa babu wani shugaban Amurka da ya taba yin magana da Hezbollah, kai tsaye ko ta hannun masu shiga tsakani. Amurka na daukar kungiyar a matsayin kungiyar ta’addanci.
Wani jami’in Lebanon ya shaida cewa Hezbollah ta sanar da Amurka, ta hannun kakakin majalisar dokokin Lebanon cewa a shirye take ta dakatar da hare-haren da take kai wa Arewacin Isra’ila muddin ƙasar ba za ta kai hare-hare Beirut.
Barnar Isra'ila a kasar Lebanon
Fadan da ake yi a Lebanon shi ne mafi girman fadadar yakin Iran zuwa wasu yankuna, inda sama da mutane miliyan 1.2 na Lebanon suka rasa matsugunansu sakamakon hare-haren Isra’ila.
A 'yan kwanakin nan, sojojin Isra’ila sun kwace sansanin Beaufort Castle mai shekaru 900 da kuma wani muhimmin tudu a Kudancin Lebanon, kamar yadda rundunar sojin ta bayyana.

Source: Getty Images
Wannan ya biyo bayan daya daga cikin ranakun da Hezbollah ta fi kai hare-hare da rokoki zuwa Arewacin Isra’ila tun bayan tsagaita wutar yaki da aka yi a watan Afrilu, lamarin da ya sa aka rufe makarantu tare da kakaba wasu takunkumai.
Iran ta harbo jirgin Amurka
A wani labarin, mun kawo muku cewa gwamnatin kasar Iran ta sanar da cewa ta harbo wani jirgi mallakar dakarun Amurka.
Sai dai a wata sanarwa da ta fitar, rundunar sojin Amurka ta ce babu wani jirgin sojin ta da aka harbo wani yanki na Iran.
Hakan na zuwa ne yayin da ake cigaba da takun saka tsakanin kasashen duk da cewa sun amince da tsagaita wuta a baya.
Asali: Legit.ng

