Hukumar Tace Fina Finai Ta Kano Ta Dauki Mataki a kan Mawaki Soja Boy da Wasu Mata 2
- Hukumar tace fina-finai ta jihar Kano ta dakatar da mawaki Usman Soja Boy da wasu jaruman mata biyu daga harkokin fim
- Hukumar ta ce ta samu korafe-korafe masu yawa daga malamai da al’ummar jihar Kano a kan bidiyon da ke nuna mawakin
- Shugaban hukumar, Abba El Mustapha ya ba da umarnin ƙin tace duk wani fim ko mawaka da Jaruman uku su ka fito a ciki
CHECK OUT: Education is Your Right! Don’t Let Social Norms Hold You Back. Learn Online with LEGIT. Enroll Now!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Kano - Hukumar tace fina-finai da dab'i ta jihar Kano ta ce ta samu korafe-korafe masu tarin yawa a kan Mawaki Usman Soja Boy saboda yawaitar batsa a bidiyon wakokinsa.
Wannan ta sa hukumar ta dakatar da Mawakin da wasu jarumai mata da ake gani a faifan bidiyon wakokin da ya ke saki a shafukan sada zumunta a kwanakin nan.

Asali: Instagram
Jaridar Aminiya ta ruwaito cewa dakatarwar na kunshe a sanarwar da jami'in hulda da jama'a na hukumar, Abdullahi Sani Sulaiman ya fitar ga manema labarai a Kano.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Hukumar tace fina-finai ta hukunta Soja Boy
Hukumar tace fina-finai ta jihar Kano Kano ta tabbatarwa da Legit cewa an kwace lasisin Soja Boy da wasu 'yan Kannywood mata biyu da ake gani a bidiyon batsa.
Shugaban Hukumar Abba El-Mustapha ya umarci sashen tace fina-finai na Hukumar umarnin kada ya kuma tace fim ko waƙa da Sojaboy ko matan suka fito a ciki.
Abdullahi Sani Sulaiman ya kara da cewa:
"Hukumar tace fina-finai ta jihar Kano ƙarƙashin jagorancin Alhaji Abba Al Mustapha a yau ta dakatar da mawaki Usman, wanda aka fi sani da Soja Boy biyo bayan korafe-korafe da mu ka samu daga al'umar jihar Kano dangane da wani sabon salon bidiyo da ya dauko a wakokin shi."
Malamai sun yi korafi a kan Soja Boy

Kara karanta wannan
Kudiri yayi nisa a majalisa, Gwamna Abba zai kafa hukumar tsaro mallakin jihar Kano
Jami'in hulda da jama'a na hukumar tace fina-finai ta Kano ta ce Malaman Musulunci da sauran jama'a sun yi takaicin yadda Soja Boy ya ke gurbata tarbiyyar jama'a.
A sababbin bidiyon mawakin da ya karade kafafen sada zumunta, ana ganin Soja Boy da jarumai Shamsiyya Muhammad da Hassana Suzan su na rungume juna, wanda ya saba da Musulunci.
Hukumar tace fina-finai ta gargadi 'yan fim
Shugaban hukumar tace fina-finai ta Kano, Abba El Mustapha ya gargadi ƴan fim da su kaucewa duk wani abu da zai zubar masu mutunci, musamman wanda ya saba addini.
Hukumar ta ce;
Kafin ta dauki irin wannan matakin Hukumar na yin iya kokarinta kan gargadin masu irin wannan halayya da su kiyayi yin duk wani abu da zai zubar da kimarsu ko ta sana'arsu."
Hukumar ta ce ba za ta dauki duk wani abu da zai taba addini, al'ada ko tarbiyar a'lummar jihar Kano da sauki ba ko goyon hakan da sunan sana'a.

Kara karanta wannan
Gwamnatin Kano ta yafewa masu zanga zanga, an dakatar da shari'ar zargin cin amanar kasa
Hukumar tace fina-finai ta dakatar da jarumai
A baya, mun ruwaito cewa hukumar tace fina-finai ta Jihar Kano ta sanar da dakatar da fitacciyar jarumar Kannywood, Samha M. Inuwa, na tsawon shekara ɗaya.
Sanarwar da jami’in yaɗa labaran hukumar, Abdullahi Sani Sulaiman, ya fitar, ta bayyana cewa an sha gargaɗin jarumar game da halayenta na rashin tarbiyya, amma ta ƙi ji.
Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.
Asali: Legit.ng