Gwamna Abba Ya Dakatar da Babban Hadiminsa, Ya Fadi Dalili
- Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya ɗauki matakin ladabtarwa kan ɗaya daga cikin hadimansa
- Abba Kabir Yusuf ya dakatar da babban mai ɗauko masa rahoto a ma'aikatar sufuri kan wasu kalamai da ya yi dangane da Rabiu Musa Ƙwankwaso
- Gwamnatin Kano ta kuma gargaɗi masu riƙe da muƙaman siyasa da su guji fitar da bayanai ba tare da an ba su izni ba
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Jihar Kano - Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya ba da umarnin dakatar da hadiminsa, Ibrahim Rabi’u nan take daga kan muƙaminsa.
Gwamna Abba ya dakatar da hadimin na sa ne wanda yake babban mai daukowa gwamna rahoto a ma’aikatar sufuri, saboda wasu kalaman da ba su dace ya furtasu ba.

Asali: Facebook
Hakan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da mai magana da yawun bakin gwamnan, Sanusi Bature Dawakin Tofa ya sanya a shafinsa na Facebook a ranar Asabar, 17 ga watan Mayun 2025.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Gwamna Abba ya dakatar da hadiminsa
Sakataren gwamnatin jihar Kano, Alhaji Umar Farouk Ibrahim, ne ya fitar da sanarwar dakatarwar, wadda ta fara aiki nan take.
Baya ga haka, gwamnatin ta umarci a rubuta takardar tambaya ga hadimin da aka dakatar, bisa kalamansa masu tsauri da suka shafi raɗe-raɗin shirin sauya sheƙa da ake zargin Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso ke yi.
Gwamnatin ta ja kunnen dukkan masu riƙe da muƙaman siyasa da kada su riƙa fitar da bayanai ba tare da izini ba, tana mai jaddada cewa duk wata sanarwa daga gwamnati sai an yarda da ita kafin a bayyana ta ga jama’a.
Gwamnatin ta bayyana cewa ba ta da hannu cikin kalaman da Rabi’u Ibrahim ya fitar, tana mai cewa wannan magana tasa ce kawai, kuma ra’ayinsa ne shi kaɗai, bisa wasu dalilai da shi ne kawai ya sani.
Gwamnatin Kano ta faɗi masu magana da yawunta
Sanarwar ta kuma tunatar da al’umma cewa, kwamishinan yaɗa labarai da harkokin cikin gida, Kwamared Ibrahim Wayya, shi ne kaɗai da ke da hurumin yin magana a madadin gwamnatin jihar.
Hakazalika daraktan yaɗa labarai da hulɗa da jama’a na gwamna, Sanusi Bature, shi ne mai magana da yawun Gwamna Abba Kabir Yusuf
Sanarwar ta ƙara da cewa:
“Gwamnati na jan kunnen duk masu riƙe da muƙaman siyasa da su guji yin bayanai ba tare da izini ba, musamman ma akan batutuwan da ba su shafi aikinsu kai tsaye ba."
"Duk wani hadimin gwamnati dole ne ya samu izini kafin ya fitar da kowace irin sanarwa da ta shafi matsayar gwamnati akan batutuwan da suka shafi jama’a ko siyasa mai sarƙaƙiya."
An haramta bikin ranar Kauyawa a Kano
A wani labarin kuma, kun ji cewa hukumar tace fina-finai ta jihar Kano, ta haramta gudanar da bikin ranar Kauyawa.
Hukumar ta bayyana cewa ta ɗauki matakin ne duba da yadda ake yin abubuwan da ba su dace ba wajen bikin.
Hakazalikaa ta bayyana cewa za ta ɗauki mataki kan duk wani ko wata ƙungiya da aka samu da laifin karya dokar.
Asali: Legit.ng