Zaben Amurka: An Bar Attajirin Duniya, Elon Musk da Cizon Yatsa bayan Kashe $500m
- Dukiyar da Elon Musk ya batar a zaben Amurka da aka yi ya kusa kai dala miliyan 500 saboda ‘yan Republican su rike mulki
- Wadannan kudi ba su yi tasirin da ake tunani ba domin kuwa ‘yan jam’iyyar hamayya suka lashe yawancin kujeru a majalisar kasar
- Da yanzu za a dawo da abubuwa baya, Musk ya ce babu abin da zai sa ya kashe makudan kudi a Amurka domin tallata ‘yan takara
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
M Malumfashi ya shafe shekaru 10 yana kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada
America - Elon Musk ya ce yana nadamar kashe kusan dala miliyan 500 wajen tallafa wa 'yan takarar Republican a zaɓen Amurka.
Elon Musk mai shekara 55 ya yarda cewa ya yi asarar kuɗin ne sakamakon kayen da yawancin 'yan takarar da ya taimaka masu suka sha.

Kara karanta wannan
Lamari ya yi tsanani har kotu tana yi wa ministan Tinubu barazana da dauri a kurkuku

Source: AFP
Musk ya ce da a ce za a dawo da hannun agogo baya, da ya rage kuɗin da ya kashe wajen yaƙin neman zaɓen a cewar rahoton Telegraph.
Elon Kusk ya ce yana jin kamar ya yi wauta da ya kashe kusan $500m wajen tallafa wa 'yan takarar Republican a zaɓen tsakiyar wa'adin Amurka.
Attajirin da ya fi kowa arziki a duk duniya ya koka musamman ganin yadda mafi yawan ‘yan siyasan da ya mara wa baya suka sha kaye a bana.
Elon Musk ya kashe $212m a Texas
Yana da-na-sanin tallafa wa wasu 'yan takara musamman Ken Paxton na jam'iyyar Republican a jihar Texas wanda ‘yan adawa suka doke shi.
Mai kudin ya kashe masa sama da dala miliyan 210 domin neman kujerar Majalisar Dattawan Amurka.
A karshe kuwa Paxton ya sha kaye hannun James Talarico, matashin ɗan majalisar dokokin jihar Texas mai wakiltar jam'iyyar adawa ta Democrat.
A garin Texas inda yake zaune, ɗan takarar Republican kuma gwamna mai ci, Greg Abbott, ya sha kaye a zaɓen gwamna a hannun Gina Hinojosa.
Musk, wanda ya halarci taron ta kafar bidiyo daga China, inda yake cikin ‘yan rakiyar Shugaba Donald Trump a wajen taron ƙungiyar APEC da ake yi.
Shi da kan shi, attajirin ya amince cewa tulin miliyoyin da ya kashe a zaɓen ba su yi tasirin kirki ba.
Musk ya shaida haka yayin wata tattaunawa da aka gudanar a taron DealBook Summit na jaridar New York Times ranar Laraba 18 ga Nuwamba 2026.
Ya ce:
"Ina jin kamar na yi wauta da na kashe kuɗi masu yawa ba tare da samun wani abin a zo a gani ba. Hakan ya nuna cewa zaɓukan Amurka ba kuɗi ne kawai ke tafiyar da su ba. Da a ce zan iya mayar da lokaci baya, da na rage kuɗin da na kashe."
Attajirin, wanda shi ne mutum na farko da dukiyarsa ta kai dala tiriliyan, ya mayar da hankali ne wajen tallafa wa Jam'iyyar Republican a zaɓen bana.
Yawancin gudummawar sun bi ta hannun ƙungiyoyin Senate Leadership Fund da America PAC.

Source: Getty Images
Majalisar Amurka ta koma hannun 'yan Democrat
Jam’iyyar Democrat ta samu rinjaye a Majalisar Dattawan Amurka bayan ta ƙwace kujeru a jihohi irinsu Texas, North Carolina, da Ohio a Amurka.
An ji rahoto cewa karɓe ikon Majalisar Wakilai zai takaita damar Shugaba Donald Trump na aiwatar da manufofinsa da kuma wajen naɗi a gwamnati.
Rashin jin daɗin jama'a kan yaƙin da Amurka ke yi da Iran da kuma tsadar man fetur ne suka taimaka wa Democrat wajen samun wannan babbarr nasara.
Asali: Legit.ng

