Ana Batun Nukiliya, Trump Ya Nuna Son Haduwa da Kim Jong Un a China
- Shugaban Amurka Donald Trump ya bayyana yiwuwar ganawa da shugaban Koriya ta Arewa, Kim Jong-un, yayin ziyarar da zai kai China
- Trump ya ce akwai yiwuwar takwaransa na China, Xi Jinping, ya gayyaci Kim zuwa birnin Shenzhen domin ganawa da su
- Shugaban Amurka ya kuma shirya ganawa da Xi Jinping da shugaban Rasha Vladimir Putin a ranar Alhamis, a yayin taron APEC
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf Kari yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
America – Shugaban Amurka, Donald Trump, ya bayyana cewa akwai yiwuwar ya gana da shugaban Koriya ta Arewa, Kim Jong-un, yayin ziyarar da zai kai China domin halartar taron kungiyar APEC.
Trump ya bayyana hakan ne a ranar Litinin, yayin da yake magana da manema labarai a fadar White House kafin ya tashi zuwa China.

Source: Getty Images
BBC ta wallafa cewa ya ce akwai yiwuwar shugaban China, Xi Jinping, ya gayyaci Kim Jong-un zuwa birnin Shenzhen, inda shugabannin za su hallara domin taron.
Trump ya yi maganar ganawa da Kim
Shugaba Donald Trump ya ce yana fatan samun damar ganawa da shugaban Koriya ta Arewa, yana mai cewa hakan zai zama abu mai kyau.
Shugaban Amurkan ya dade yana nuna sha'awar sake ganawa da Kim, musamman ganin kyakkyawar alakar da ya ce suke da ita a matsayinsu na shugabanni.
Sai dai a makon da ya gabata, kafafen yada labaran Amurka sun ruwaito cewa babu wani shiri na ganawar Trump da Kim a yayin ziyarar China, duk da rade-radin yiwuwar farfado da tattaunawar diflomasiyya tsakanin kasashen biyu.
Trump zai gana da Xi da Putin
A News ta wallafa cewa Trump na shirin ganawa da shugaban China, Xi Jinping, da shugaban Rasha, Vladimir Putin, a ranar Alhamis, a gefe da taron APEC da za a gudanar a birnin Shenzhen.
Ganawar shugabannin uku na zuwa ne a daidai lokacin da Trump ke kokarin nemo hanyar diflomasiyya domin kawo karshen yakin Ukraine.
Haka kuma, Amurka da China na ci gaba da samun sabani kan batutuwan cinikayya, haraji da wasu muhimman lamuran siyasar kasa da kasa.

Source: Getty Images
Masana Amurka sun yi hasashen cewa batun makaman nukiliyar Koriya ta Arewa ba zai kasance cikin manyan batutuwan da za a tattauna a ganawar shugabannin uku ba.
Fadar White House ba ta mayar da martani kan tambayar kamfanin dillancin labarai na Yonhap game da ko za a tattauna batun Koriya ta Arewa a ganawar ba.
Amurka ta magantu kan Iran
A wani labarin, kun ji cewa wasu bayanan sirri na Amurka sun nuna cewa Iran na shirin kai hari kan manyan jami'an gwamnatin Trump ta hanyar amfani da wani makami mai gurbata muhalli.
Jami'an Amurka bakwai ne suka bayyana wannan bayanin, inda suka ce har yanzu ana nazarin ko Iran na da niyya ko kuma karfin aiwatar da irin wannan hari.
Sai dai majiyoyin sun ce shirin na Iran a halin yanzu ya fi kama da kokarin tanadar hanyoyin kai hari fiye da shirin kai hari nan take.
Asali: Legit.ng

