Mutuwa Mai Tonon Silili: Iyalan Marigayi Tsohon Gwamna na Rikici kan Dukiyarsa

Mutuwa Mai Tonon Silili: Iyalan Marigayi Tsohon Gwamna na Rikici kan Dukiyarsa

  • ’Ya’ya huɗu na marigayi tsohon gwamnan jihar Kogi, Alhaji Ibrahim Idris, sun garzaya kotu kan kadarorinsa
  • Sun nemi kotu ta naɗa wani mutum da zai kula da kadarorin mahaifinsu, ciki har da Grand Ibro Hotel, gidaje, filaye da asusun banki, har sai an kammala shari’ar
  • Kotun ta umarci dukkan ’yan uwa da su bayyana a gabanta ranar 23 ga Nuwamba, 2026, domin ci gaba da sauraron ƙarar

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al’amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Lokoja, Kogi - ’Ya’ya huɗu na marigayi tsohon gwamnan jihar Kogi, Alhaji Ibrahim Idris, sun shigar da ƙara a wata kotu da ke Abuja kan rabon gadonsa.

A cikin ƙarar, Asma’u, Fatima, Zainab da Jamila Ibrahim Idris ne suka nemi kotu ta hana wasu ’yan uwansu 13 sayarwa, jingina, bayarwa ko canja wurin mallakar duk wata kadara da ke cikin gadon mahaifinsu.

Kara karanta wannan

Muhimmin tarihi da Tinubu ya kafa game da yaki da ta'addanci a Najeriya

An fara rikici kan dukiyar marigayi tsohon gwamna
Marigayi tsohon gwamnan Kogi, Ibrahim Idris. Hoto: Ibrahim Idris.
Source: Facebook

A cikin takardar neman umarnin kotu wacce lauyansu, I. H. Nalaraba, ya shigar, sun nemi a bayar da umarnin hana duk wani abu da zai iya janyo asarar kadarorin har sai an kammala shari’ar, cewar The Nation.

Kadarorin da ake takaddama a kansu

Daga cikin kadarorin da ake takaddama a kansu akwai otal ɗin Grand Ibro Hotel da wani ƙarin otal ɗinsa da ke yankin Wuse Zone 5 a Abuja.

Sauran kadarorin sun haɗa da wani gida da ke kan titin Kwame Nkrumah a Asokoro, Abuja, wani gida da ke bayan gidan gwamnatin jihar Kogi a Lokoja da wani gida a garin Idah.

Haka kuma, akwai filaye da kadarorin gidaje a Lokoja, Idah, Ayingba da Abejukolo, da kuma wani gida mai ɗaki ɗaya da ke Dubai a Hadaddiyar Daular Larabawa.

Sauran kadarorin sun haɗa da fili da ke bayan kamfanin SETRACO a Jabi, Abuja, asusun banki a wasu bankunan Najeriya da kayayyakin marigayin na amfanin kansa., kayayyakin sun haɗa da motoci, tufafi, agogon hannu, takalma da kayan ɗaki.

Kara karanta wannan

Yadda mai babur ya jawo hatsarin mota, ya rutsa da shugaban APC, daraktan kamfen

Rigima ta kaure kan gadon marigayi tsohon gwamnan Kogi
Taswirar jihar Kogi da ta yi rashin tsohon gwamna. Hoto: Legit.
Source: Original

Sun nemi a naɗa wanda zai kula da gadon

Waɗanda suka shigar da ƙarar sun nemi kotu ta naɗa wani mutum da zai karɓi ragamar kula da kadarorin, domin kare su da kuma tattara kuɗaɗen haya da sauran kuɗaɗen shiga.

Sun bukaci wanda za a naɗa ya gabatar da cikakken jerin dukkan kadarorin marigayin da ke Abuja da sauran wurare cikin kwanaki 21 bayan naɗa shi.

Haka kuma, sun nemi a buɗe wani asusun banki na musamman domin adana kuɗaɗen gadon, tare da gabatar da rahoton yadda yake tafiyar da kadarorin a duk bayan watanni uku.

Sun kuma bukaci a hana wanda za a naɗa sayar da kowace kadara ba tare da izinin kotu ba, yayin da kotu za ta tantance kuɗin aikin da zai riƙa karɓa daga kuɗaɗen shiga na kadarorin.

Sun zargi wasu ’yan uwa da karɓar kuɗin haya

Waɗanda suka shigar da ƙarar sun nemi kotu ta umarci duk wani magaji da ya karɓi kuɗin haya ko wasu kuɗaɗen shiga daga kadarorin tun bayan rasuwar tsohon gwamnan a ranar 20 ga Satumba, 2026, da ya yi cikakken bayani kan kuɗaɗen.

Kara karanta wannan

Abin tausayi: Matashi ya mutu a ƙoƙarin kare iyayensa daga sharrin 'yan bindiga

Sun kuma nemi a umarci duk wanda ya karɓi wani abu daga cikin kadarorin marigayin da ya mayar da shi ga wanda kotu za ta naɗa cikin kwanaki 14.

Sun kuma nemi kotu ta umarci waɗanda ake ƙara da su kare duk takardun mallakar kadarori, bayanan asusun banki, rasit da yarjejeniyoyin haya.

A cikin rantsuwar shaidu mai sakin layi 16, wani lauya mai suna Sani Sambo, wanda ke aiki a ofishin lauyoyin waɗanda suka shigar da ƙarar, ya bayyana cewa har yanzu ba a raba gadon marigayin tsakanin magadansa bisa koyarwar shari’ar Musulunci ba.

Ya ce marigayin Musulmi ne mai gudanar da ibadunsa, amma har yanzu ba a yi rabon gadon nasa bisa tanadin shari’ar Musulunci ba.

An zargi wasu da rusa masallaci a otal

Lauyan ya kuma yi zargin cewa bayan rasuwar tsohon gwamnan, wasu daga cikin ’yan uwansa sun rushe wani masallaci da ke cikin otal ɗin, inda suka fara wani sabon gini a wurin.

Ya ƙara da cewa harkokin kasuwancin otal ɗin na ci gaba da gudana, amma ba a gabatar wa iyalan marigayin da cikakken bayani kan kuɗaɗen da ake samu daga kasuwancin ba.

Kara karanta wannan

Kotu ta shiga maganar Aminu Gwarzo da 'yan NDC ke neman hana shi takara a Kano

Baya ga neman dakatar da wasu ayyuka kan kadarorin, waɗanda suka shigar da ƙarar sun kuma nemi kotu ta tabbatar da waɗanda suke da haƙƙin gadon marigayin tare da bayar da umarnin raba kadarorin bisa shari’ar Musulunci.

Kotun ta sanya ranar sauraron ƙarar

Alkalin kotun, Ado Muktar, ya umarci dukkan ’yan uwan marigayin da su bayyana a gabansa ranar 23 ga Nuwamba, 2026, domin ci gaba da sauraron ƙarar.

Haka kuma, an shirya tattara bayanan kadarorin marigayin domin sanin abubuwan da ke cikin gadon.

An yi jana'izar tsohon gwamna Idris

A baya, mun kawo muku cewa an yi jana'iza tare da birne tsohon gwamnan jihar Kogi, Alhaji Ibrahim Idris a makabartar Gudu da ke Apo a birnin tarayya Abuja.

Idan baku manta ha Ibrahim Idris ya rasu yana da shekaru 77 bayan fama da rashin lafiya a kasar Birtaniya.

Gwamnan jihar Kogi, Ahmed Usman Ododo da tsoffin gwamnoni Yahaya Bello da Idris Wada sun halarci jana’izar marigayin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jarida ne da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.