Ilhan: Musulmar da Trump ke Adawa da Ita Ta Lashe Zaben Amurka
- 'Yar majalisar wakilan Amurka, Ilhan Omar, ta sake lashe zaɓe a gundumar Minnesota ta 5 bayan ta doke ɗan takarar jam'iyyar Republican, John Nagel
- Nasarar ta ba Omar damar ci gaba da wakiltar gundumar da ta ke kai wa tun shekarar 2019, inda za ta fara wa'adi na biyar a majalisar
- Omar, wadda 'yar asalin Somaliya ce kuma ta taɓa zama 'yar gudun hijira, ta samu nasarar ne a daidai lokacin da take fuskantar suka daga Donald Trump
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf Kari yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru huɗu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Amurka – 'Yar majalisar wakilan Amurka, Ilhan Omar, ta sake lashe zaɓe a gundumar Minnesota ta 5 bayan ta doke ɗan takarar jam'iyyar Republican, John Nagel
Ilhan Omar ta kasance tana wakiltar gundumar tun shekarar 2019. Gundumar ta ƙunshi birnin Minneapolis da wasu unguwannin da ke kewaye da shi, kuma ita ce gundumar da ta fi goyon bayan jam'iyyar Democrat a jihar Minnesota da ma ƙasar baki ɗaya.

Source: Twitter
Gidan talabijin na CBS ne ya bayyana hakan bisa hasashen cibiyarsa ta tantance sakamakon zaɓe, inda ya ce Omar ta samu nasarar ne a daren Talata.
Yadda Ilhan Omar ta yi nasara
Omar ta samu gagarumar nasara a zaɓen fitar da ɗan takarar jam'iyyar Democrat da aka gudanar a watan Agusta, inda ta doke Julie T. Le, Abena McKenzie, Latonya Reeves da Nate Schluter.
A watan Mayu, jam'iyyar Democrat ta Minnesota (DFL) ta amince da ita a matsayin 'yar takararta yayin babban taron jam'iyyar na jihar.
Nasarar da ta samu a babban zaɓen na nufin za ta ci gaba da wakiltar al'ummar gundumar Minnesota ta 5 a majalisar wakilan Amurka.
Sukar Trump ga Ihan
Ilhan Omar, wadda ta fito daga Somaliya kuma ta shiga Amurka a matsayin 'yar gudun hijira, ta daɗe tana fuskantar kalaman suka daga Shugaba Donald Trump kan batun baƙi.
Bayan zaɓenta na farko, Trump ya taɓa cewa ta koma ƙasarta ta asali. Haka kuma, ya kira ta da kalaman cin mutunci tare da cewa ya kamata a gudanar da bincike a kanta.

Kara karanta wannan
Abubuwan da ya kamata ku sani game da tallafin N50,000 da aka fara turawa mutane a Najeriya

Source: Facebook
A watan Oktoban 2026, jami'an tsaron cikin gida na Amurka sun kai samame a gidan Omar da ke birnin Washington DC, a wani bincike da ake yi kan takardun shige da fice da marigayin mahaifinta ya gabatar mata lokacin tana yarinya.
Omar ta yi Allah-wadai da samamen da binciken, inda ta bayyana su a matsayin amfani da ikon gwamnati ba bisa ƙa'ida ba da kuma yunƙurin amfani da hukumomin tsaro wajen farautar abokan hamayyar siyasa.
Democrat ta kwace ikon majalisa
A wani labarin, mun ruwaito cewa jam'iyyar Democrat ta samu nasarar karɓe ikon Majalisar Wakilan Amurka, inda ake hasashen za ta samu kujeru kusan 255, fiye da 218 da ake buƙata domin samun rinjaye.
Haka kuma, jam'iyyar ta sake samun ikon Majalisar Dattawa bayan ta doke 'yan takarar Republican a zaɓukan da aka gudanar a faɗin ƙasar.
Wannan nasara na nufin Democrat za ta samu ikon jagorantar majalisun dokokin Amurka guda biyu daga shekara mai zuwa, a karon farko tun shekarar 2022..
Asali: Legit.ng
