Abin da Amurka Za Ta Yi kan Zaben Shugaban Kasar Najeriya a 2027

Abin da Amurka Za Ta Yi kan Zaben Shugaban Kasar Najeriya a 2027

  • ’Yan majalisar dokokin Amurka sun ce za su sa ido sosai kan zaɓen shugaban ƙasar Najeriya na watan Janairun 2027
  • Dan majalisa Riley Moore ya ce dole ne Amurka ta tabbatar da cewa ’yan Najeriya sun samu damar zaɓen shugabanninsu cikin ’yanci
  • Frank Garcia ya ce har yanzu ba a samu isasshen ci gaba wajen magance matsalolin tsaron Najeriya ba, duk da haɗin gwiwar ƙasashen biyu

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Birnin Washington, Amurka - ’Yan majalisar dokokin Amurka sun yi alƙawarin sanya ido sosai kan zaɓen shugaban ƙasar Najeriya na watan Janairun 2027, sakamakon damuwar da ake da ita kan matsalar tsaro da kuma buƙatar gudanar da sahihin zaɓe.

’Yan majalisar sun bayyana hakan ne yayin wani zaman sauraron ra’ayoyin jama’a kan Najeriya da ƙaramin kwamitin majalisar wakilan Amurka mai kula da harkokin Afirka ya shirya.

Kara karanta wannan

Akwai yiwuwar Amaechi ya bar gwamnatin Atiku idan suka hau mulki

Amurka ta yi magana kan zaben 2027 a Najeriya
'Yan majalisar wakilan Amurka yayin zama a majalisa Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

A yayin zaman, sun duba ƙoƙarin gwamnatin Najeriya na kare al’ummomin da ke cikin haɗari da magance rikice-rikice, musamman a yankin Middle Belt, cewar rahoton jaridar Daily Trust.

Amurka za ta sanya ido kan zaɓen 2027

Ɗan majalisar wakilan Amurka na jam’iyyar Republican, Riley Moore, ya ce ya kamata majalisar dokokin ƙasar ta mayar da hankali sosai kan zaɓen Najeriya domin tabbatar da cewa ’yan ƙasar sun samu damar zaɓen shugabanninsu cikin ’yanci.

“Muna buƙatar sanya ido sosai kan waɗannan zaɓukan shugaban ƙasa, kamar yadda shaho ke sa ido kan abin da yake farauta. Ni da kaina zan sanya ido, kuma ya kamata dukkanmu mu yi hakan.” In ji shi.

Zaman sauraron ra’ayoyin, wanda aka gudanar ƙarƙashin taken “Shekara Ɗaya Bayan Haka: Tantance Ƙoƙarin Najeriya na Kare Kiristoci da Tabbatar da Tsaron Middle Belt”, ya kuma mayar da hankali kan matakan da gwamnati ke ɗauka bayan hare-hare.

Haka kuma, mahalarta sun tattauna gurfanar da waɗanda ake zargi da aikata laifukan da kuma matakan da Amurka za ta iya ɗauka domin taimakawa wajen magance matsalar tsaro, jaridar TheCable ta kawo labarin.

Kara karanta wannan

"Ku ce ni da Kwankwaso mun gaza"; Peter Obi ya dauki muhimmin alkawari ga 'yan Najeriya

Amurka ta ce ba a samu isasshen ci gaba ba

A nasa jawabin, mataimakin ministan harkokin wajen Amurka mai kula da Afirka, Frank Garcia, ya amince cewa har yanzu ba a samu isasshen ci gaba wajen magance matsalolin tsaron Najeriya ba, duk da tattaunawa da haɗin gwiwar da ƙasashen biyu ke yi.

Sai dai ya bayyana cewa hakan ba yana nufin Najeriya ta yi watsi da damuwar Amurka ba ko kuma ba ta ɗaukar matakai ba. Ya ce matsalar ita ce matakan da aka ɗauka ba su samar da sakamakon da ake buƙata ba tukuna.

Ya ƙara da cewa Amurka na sa ran ganin ƙarin sakamako na zahiri daga tattaunawar da take yi da Najeriya.

Ya ce ana buƙatar ƙarin ƙoƙari wajen kare al’ummomin da ke cikin haɗari, inganta yadda hukumomi ke mayar da martani ga gargaɗin hare-hare tun kafin su faru, da kuma tabbatar da hukunta waɗanda suka aikata laifuffuka.

Amurka za ta sa ido kan zaben 2027 a Najeriya
Shugaba Donald Trump na Amurka a fadar White House Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

An yi zargin magudin zabe a 2027

Kara karanta wannan

Tinubu ya kwantar da hankulan 'yan Najeriya, ya fadi shirinsa kan kawo karshen rashin tsaro

A wani labarin kuma, kun ji cewa jagoran jam’iyyar Nigeria Democratic Congress (NDC) na ƙasa, Seriake Dickson, ya yi zargi kan shirin magudi a zaben 2027.

Sanata Dickson ya yi zargin cewa wasu mutanen da bai bayyana sunayensu ba na shirin yin maguɗin sakamakon zaɓen 2027 tare da amfani da jami’an tsaro na bogi wajen tsoratar da masu zaɓe.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng