Saduwa da iyali a kan kari yana kara kaifin kwakwalwa - Masana
A yayin da Hausawa kan ce ilimi kogi ne sai dai kowa ya debi daidai shi, hakan ta ke kuwa domin wani sabon binciken kwararrun masana kiwon lafiya ya bankado wata muhimmiyar fa'ida mai tasiri ga saduwa da iyali akan kari.
Wani sabon bincike da masana suka gudanar a jami'ar Coventry da kuma jami'ar Orford da ke kasar Birtaniya, ya bayyana yadda yawan saduwa da iyali akan kari ke da matukar tasiri wajen kara kaifi da kuma inganta lafiyar kwakwalwa.
Musamman a tsakanin manyan mutane da shekarun su suka ja, binciken masanan ya tabbatar yadda masu saduwa da iyalan su akan kari ke samun habaka ta kaifin basira da kuma inganci na lafiyar kwakwalen su.
Kamar yadda shafin yanar gizo na sciencedaily.com ya bayyana, an wallafa sakamakon wannan bincike da aka gudanar kan mutane 73 ma su shekaru tsakanin 50 zuwa 83 cikin mujallar kimiyya ta The Journals of Gerontology, Series B: Psychological and Social Sciences.
Bayan amsa tamboyi dangane da kiwon lafiya, dabi'un rayuwa da kuma bayanai na kusantar iyalansu cikin tsawon watanni 12 da suka gabata, binciken ya tabbatar da yadda kaifin basira da kuma lafiyar kwakwalen Mazajen 28 da kuma Mata 45 ta inganta.
KARANTA KUMA: Saraki ya nemi shugabanni da su saukaka tsananin da ke cikin al'umma
Jagoran masu binciken, Dakta Hayley Wright, ta tabbatar da sakamakon wannan bincike da a cewar ta a halin yanzu ana iya kiran sa hasashe da har sai bincike mai zurfi gaske ya tabbatar da sahihancin sa.
Cikin wani rahoton da shafin na sciencedaily.com ya bayyana yau Laraba, 16 Janairu, 2019, Sauro mai sanya zazzabi na cutar Malaria mai tsanani ya bayyana karo na farko a kasar Habasha inda ya jefa al'umma cikin zaman dar-dar.
Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da Shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com
Ku biyo cikin shafukan mu na zaurukan sada zumunta:
https://facebook.com/legitnghausa
https://twitter.com/legitnghausa
Asali: Legit.ng