An Shiga Jimami Yayin da Mace Mafi Tsayi a Duniya Ta Rigamu Gidan Gaskiya a Kasar Brazil

An Shiga Jimami Yayin da Mace Mafi Tsayi a Duniya Ta Rigamu Gidan Gaskiya a Kasar Brazil

  • Maria Feliciana dos Santos, 'yar Brazil, wacce ta ajiye tarihi a matsayin mace mafi tsayi a duniya ta rigamu gidan gaskiya
  • Santos wadda ta rasu tana da shekaru 77 a duniya ta rike kambun 'Sarauniyar Tsawo' a shekarun 1960 a Brazil
  • A watan Mayun 2022, gidan tarihi na Museu de Gente Sergipana ya karrama Santos ta hanyar yin wani mutum-mutumi nata

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Brazil - Daya daga cikin mata mafi tsayi a duniya, 'yar wasan kwallon kwando da ta yi suna a matsayin 'sarauniyar tsawo' a shekarun 1960' ta rasu a asibiti tana da shekaru 77.

Sarauniyar tsawo ta duniya, Maria Feliciana dos Santos ta rasu
Maria Feliciana dos Santos, mace mafi tsayi a duniya ta rasu tana da shekaru 77. Hoto: @Mariafelicianaofc
Asali: Instagram

Maria Feliciana dos Santos, 'yar Brazil, wacce ta ajiye tarihi, ta kara tsayi zuwa inci 87.8 a lokacin da shiga shekaru ashirin na rayuwarta, jaridar Daily Mail ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Murna yayin da hafsan tsaron Najeriya ya laluɓo hanyar daƙile matsalar tsaro, ya fadi dalilai

'Yan uwan ​​Santos sun tabbatar da rasuwarta, tare da cewa ta mutu ne a wani asibiti da ke Aracaju, inda aka kwantar da ita sakamkon kamuwa da cutar huhu.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Mutuwar 'Sarauniyar Tsawo' ta girgiza mutane

Santos, wadda aka haifa a garin Amparo do São Francisco, ta zagaya birane da dama tana yin wasanni kafin ta lashe gasar 'sarauniyar tsawo ta duniya' a cikin shekarun 1960.

Edvaldo Nogueira, magajin garin Aracaju City inda ta ke zaune ya ayyana zaman makoki na kwanaki uku a yankin tare da karrama tsohuwar 'yar wasan kwallon kwandon.

“A cikin jimami na samu labarin mutuwar Maria Feliciana daga Sergipe. Daya daga cikin mata mafi tsayi a duniya, wadda na santa tun ina karamin yaro.”

- In ji Nogueira.

An karrama Maria Feliciana dos Santos

Jaridar The Guardian ta ruwaito gwamnan Sergipe, Fábio Mitidieri, ya ce ya samu labarin mutuwar Maria, mace mafi tsayi a duniya, yana mai cewa labarin ya girgiza shi matuka.

Kara karanta wannan

Jimami yayin da fitacciyar mawakiyar yabo ta riga mu gidan gaskiya, ta yi tashe

"Maria Feliciana ta bar tarihin da ba zamu taba mantawa da shi ba, inda kuma aka sanyawa wani babban gini a jiharmu sunanta domin tunawa da ita."

- A cewar Mitidieri.

A watan Mayun 2022, Museu de Gente Sergipana ya karrama Santos ta hanyar yin wani mutum-mutumi nata tare da ajiye shi a ƙofar shiga gidan tarihin.

Mawakiyar yabo, Adeleke ta mutu

A nan kasa Najeriya, Legit Hausa ta ruwaito matashiyar mawakiya wacce ta kware a wakokin yabo, Morenikeji Adeleke ta riga mu gidan gaskiya a ranar Asabar 27 ga watan Afrilu.

Abokiyar aikin marigayiyar, Esther Igbekele ita ta sanar da hakan inda ta ce tabbas za su yi keyar marigayiyar wadda ta rayu cikin yabon Yesu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.

Online view pixel