Kasar Amurka Ta Saki Sunayen ‘Yan Najeriya 24 da Aka Kama da kuma Laifuffukansu

Kasar Amurka Ta Saki Sunayen ‘Yan Najeriya 24 da Aka Kama da kuma Laifuffukansu

  • Amurka ta bayyana sunayen ’yan Najeriya 24 da jami’an ICE suka kama bisa zargin aikata laifuffuka daban-daban
  • Zarge-zargen da ake yi masu sun hada da damfara, safarar kuɗin haram, satar bayanan mutane da laifuffukan kwayoyi
  • Matakin na zuwa ne yayin da gwamnatin Donald Trump ke tsaurara matakan shige da fice da korar baki daga Amurka

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

M Malumfashi ya shafe shekaru 10 yana kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada

America - Hukumar tsaron cikin gida ta Amurka (DHS) ta fitar da sunaye da hotunan ’yan Najeriya 24 da aka yi ram da su saboda zargin laifi.

Jami’an kula da shige da fice sun kama su bisa zargin aikata laifuffuka daban-daban, yayin da kasar ake tsaurara matakan korar baki.

Donald J. Trump
Shugaban kasar Amurka, Donald J. Trump
Source: Getty Images

Amurka ta kama mutanen Najeriya 24

The Cable ta ce a cewar bayanan da hukumar ta fitar, jami’an Hukumar Shige da Fice da Kwastam ta Amurka (ICE) ne suka kama su.

Kara karanta wannan

Tinubu Must Go: Yan sanda sun faɗi abin da ya faru bayan zargin hana masu gangami

An yi ram da wadannan mutane har su 24 a wurare daban-daban na kasar Amurka.

Laifuffukan da ake zargin mutanen da aikatawa sun hada da damfara ta hanyar aika sakonnin kudi ko wasiku na karya da yaudara.

Akwai kuma zargin safarar kudin haram da laifuffukan da suka shafi harkar kwayoyi, satar bayanan mutane, kai hari da sauransu.

Rahoton Blueprint ya ce sauran laifuffukan sun kunshi amfani da jabun takardu da cin zarafin yara.

A cikin sanarwar kama mutanen, DHS ta ce manufar fitar da bayanan ita ce nuna wadanda ba ’yan kasar Amurka ba da aka kama.

Sanarwar da hukumomin Amurka suka fitar

Hukumar ta ce:

“Ma’aikatar Tsaron Cikin Gida ta Amurka tana bayyana sunayen bakin da ake ganin sun fi kowa muni wajen aikata laifuffuka, wadanda jami’an Hukumar Shige da Fice da Kwastam ta Amurka (ICE) suka kama.”

Ta kara da cewa jami’an DHS da ICE suna aiwatar da manufar Shugaba Donald Trump na korar baki da yawa daga kasar.

Kara karanta wannan

Kansilar APC ta mutu a hannun yan bindiga mako 1 bayan sace ta

Jawabin ya ce gwamnatin Amurka za ta fara da wadanda ake ganin sun fi yin barna.

Sunayen ’yan Najeriya 24 da hukumar ta ambata

Wadannan su ne zarge-zargen da aka danganta wa mutanen. Ambaton suna a cikin jerin ba ya tabbatar da cewa an same su da laifi a kotu.

1. Emmanuel Omowaiye — An kama shi bisa zargin damfara ta hanyar wasiku a Richmond, Texas.

2. Laurene Onwuka — An kama ta bisa zargin damfara da kwaikwayon wani a Chantilly, Virginia.

3. Olusegun Shonekan — An kama shi bisa zargin damfara ta hanyar aika sakonnin kuki a Newark, New Jersey.

4. Olusegun Olaseni — An kama shi bisa zargin sayar da ƙwayar amphetamine a Greencastle, Indiana.

5. Peter Ude — An kama shi bisa zargin damfara ta hanyar aika saƙonnin kuɗi a Atlanta, Georgia.

6. Newton Jemide — An kama shi bisa zargin damfara ta hanyar aika saƙonnin kuɗi da wasiƙu, da kuma haɗa baki wajen aikata laifi a Fort Dix, New Jersey.

7. Shedrack Umukoro — An kama shi bisa zargin safarar kuɗaɗen haram a Yazoo City, Mississippi.

Kara karanta wannan

Labaran bogi da suka rika yawo a kafafen sada zumunta a makonnin nan

8. Olasoji Akinbode — An kama shi bisa zargin damfara da karya da sunan wani wani a Kearny, New Jersey.

9. Oluwatosin Afolabi — An kama shi bisa zargin damfara a Conroe, Texas.

10. Alameen Adetunji Tokosi — An kama shi bisa zargin mallakar kwayoyi a Chicago, Illinois.

11. Joshua Ipoade — An kama shi bisa zargin damfara ta hanyar aika sakonnin kudi a Atlanta, Georgia.

12. Michael Orji — An kama shi bisa zargin karya dokokin makamai, damfara, satar bayanan mutum, damfara ta hanyar aika sakonnin kudi, karyar cewa shi ɗan ƙasar Amurka ne da kuma safarar kuɗin haram a Oxford, Wisconsin.

13. Ahmadu Apooyin — An kama shi bisa zargin aikata laifin da ya shafi ƙwayoyi a Baltimore, Maryland.

14. Teslim Kiriji — An kama shi bisa zargin safarar kuɗin haram a Yazoo City, Mississippi.

15. Onomen Uduebor — An kama shi bisa zargin satar bayanan wani mutum a Seattle, Washington.

16. Charles Ochi — An kama shi bisa zargin safarar kuɗin haram a White Deer, Pennsylvania.

17. Daniel Eta — An kama shi bisa zargin damfara ta hanyar aika saƙonnin kuɗi a White Deer, Pennsylvania.

Kara karanta wannan

Asiri ya tonu, an cafke wani da ke cin mutuncin malaman Musulunci a Najeriya

18. Ifeanyi Ibennah — An kama shi bisa zargin cin zarafin yaro a Tampa, Florida.

19. Kazeem Runsewe — An kama shi bisa zargin damfara ta hanyar aika saƙonnin kuɗi a Thomson, Illinois.

20. Fatiu Lawal — An kama shi bisa zargin damfara ta hanyar aika sakonnin kudi a Lompoc, California.

21. Justin Akubueze — An kama shi bisa zargin safarar kuɗaɗen haram a Orem, Utah.

22. Moyinoluwaseun Okeowo — An kama shi bisa zargin sata, yin jabun takardu da kuma boye kadarorin sata a Orlando, Florida.

23. Babajide Oluwaseun Faseyi — An kama shi bisa zargin kai hari a Alden, New York.

24. Bright Eigbedion — An kama shi bisa zargin safarar kuɗaɗen haram a Lompoc, California.

Shugaba Donald TrumpShugaba Donald Trump
Shugaba Donald Trump wanda yake mulkin Amurka Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Amurka za ta harbe tsohon sojan kasar

Ana da labari cewa Mai girma Donald Trump ya amince da shirin kashe Nidal Malik Hasan, tsohon likitan sojan Amurka, ta hanyar harbe shi.

An samu Hasan da laifin kashe sojoji 13 da raunata wasu 32 a sansanin Fort Hood a shekarar 2009.

Wannan zai zama karon farko da sojojin Amurka za su aiwatar da hukuncin kisa ta hanyar harbe mutum tun bayan Yaƙin Duniya na Biyu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng