Asiri Ya Tonu, an cafke Wani da Ke Cin Mutuncin Malaman Musulunci a Najeriya
- ‘Yan sanda sun kama wani mutum da aka ayyana a matsayin wanda ake nema, bisa zargin cin zarafin malaman addini ta kafafen sada zumunta
- An kama mutumin ne bayan wasu limaman addini sun shigar da korafi, inda suka zarge shi da yin kalaman batanci kan su da akidunsu
- ‘Yan sanda sun ce za a gurfanar da wanda ake zargin bayan kammala bincike, yayin da ake jiran wasu korafe-korafe domin gano cikakken lamarin
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Ikeja, Lagos - Yan sanda a Jihar Lagos sun kama wani mutum da ake nema bisa zargin cin zarafin malaman addini ta kafafen sada zumunta da kuma yin kalaman batanci kan addininsu.
An kama wanda ake zargin, wanda ke zaune a yankin Alakuko na jihar, ranar Talata, bayan wasu malaman addini sun shigar da korafe-korafe a kansa.

Kara karanta wannan
Dubu ta cika: An kama wanda ya kashe malamin addinin Musulunci a Arewacin Najeriya

Source: Facebook
Bayan korafe-korafen, Kwamishinan ‘Yan Sandan Jihar Lagos, Fatai Tijani, ya umarci Sashen Binciken Manyan Laifuka na Jiha, Panti, Yaba, da gudanar da cikakken bincike kan zarge-zargen, cewar PM News.
Fasto, malami sun shigar da korafi kan matashi
Wata majiya daga rundunar ‘yan sandan ta ce wani fitaccen Fasto na Cocin Celestial da ke yankin Ojokoro ne ya fara shigar da korafi.
Faston ya zargi wanda ake zargin da yin kalaman batanci a kansa da kuma addininsa. Haka kuma, wani fitaccen malamin Musulunci da ke yankin Ogba ya shigar da irin wannan korafi.
Malamin ya zargi wanda ake zargin da yin kalaman batanci a kansa da kuma imaninsa, a cewar majiyar, ‘yan sanda a Jihar Kwara ma suna neman mutumin.
Majiyar ta ce an samu sammacin kama shi a Kwara, wanda ke da alaka da wasu kararrakin cin zarafin malaman addini ta kafafen sada zumunta.

Source: Original
Matakin da yan sanda a Lagos

Kara karanta wannan
A karshe, kotu ta ba da belin matasa da ke tsare kan sanya rigar 'Tinubu Must Go'
Majiyar ta ce rundunar ‘yan sandan Lagos ta tattara bayanan wanda ake zargin, yayin da take jiran wasu korafe-korafe daga mutanen da ka iya fuskantar irin wannan zargi.
Ta kara da cewa karin korafe-korafen zai taimaka wa masu bincike wajen gano cikakken yadda lamarin ya faru da kuma matakin da ya dace a dauka.
Majiyar ta ce ana sa ran gurfanar da wanda ake zargin a gaban kotu bayan kammala binciken. Ta tabbatar da cewa za a gudanar da binciken cikin kwarewa.
Ta kuma ce za a bai wa dukkan bangarorin da abin ya shafa damar gabatar da hujjoji da bayanansu kafin daukar matakin karshe, kamar yadda Daily Post ta ce.
Matashi ya kashe wani kan N500
An ji cewa rundunar ’yan sandan Jigawa ta kama matashi mai shekaru 20 bisa zargin kashe wani bayan takaddama kan bashin N500.
An ce wanda ake zargin ya daba wa matashin wuƙa bayan ya kasa biyan N500 da ya rage daga kuɗin wayar hannu da ya saya a wurinsa.
Har ila yau, ’yan sanda sun kama Abbas Ibrahim bisa zargin ƙona ɗakin ɗan uwansa, lamarin da ya yi sanadin mutuwarsa nan take.
Asali: Legit.ng