Trump Ya Ballo Sabon Rikici da ICC, Faransa da Sauran Kasashe Sun Ce ba Ruwansu

Trump Ya Ballo Sabon Rikici da ICC, Faransa da Sauran Kasashe Sun Ce ba Ruwansu

  • Amurka ta kakaba takunkumi kan kotun ICC), lamarin da ya sa ƙasashe da dama ciki har da ƙawayen Amurka suka soki matakin tare da jaddada goyon bayansu ga kotun
  • Hadimin Trump, Marco Rubio ya sanar da cewa Washington za ta dakatar da mu'amala da kotun, yayin da Shugaba Donald Trump ya ce ba zai taɓa yarda kotun ta hukunta 'yan Amurka ba
  • Kotun ICC ta bayyana matakin a matsayin harin da aka kai wa tsarin shari'a da ma'aunin shari'ar ƙasa da ƙasa, inda ta yi kiran ƙasashe mambobi 125 da su tsaya tsayin daka wajen kare cibiyar

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf Kari yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Washington – Amurka ta ƙara ƙara ƙarfafa takunkumin da take kakaba wa kotun ICC, wanda hakan ya haifar da martani mai tsanani daga ƙasashen Turai, Canada, Japan, da kuma Majalisar Ɗinkin Duniya (MDD).

Kara karanta wannan

Yadda Trump ya ajiye takama ya tafi Rasha neman agajin Putin

Marco Rubio ya bayyana cewa Washington za ta hana dukkan mu'amala da kotun, da nufin ruguza ƙarfinta na gudanar da ayyukanta, yana mai jaddada cewa Shugaba Donald Trump ba zai amince da shari'anta 'yan ƙasarsa ba.

Shugaba Donald Trump
Shugaban Amurka, Donald Trump. Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Martanin kotun ICC ga kasar Amurka

Al Jazeera ta rahoto cewa a martaninta, kotun ICC ya ayyana matakin a matsayin babban haɗari ga tsarin shari'ar ƙasa da ƙasa, tare da yin kira ga ƙasashe mambobi 125 da su tsaya mata.

Kotun ya bayyana cewa:

"Karfin kotun yanzu yana hannun ƙasashen da suka ƙirƙire ta. Wannan ba tsaron cibiya guda ɗaya ba ne kawai, kariya ne ga tsarin shari'ar duniya."

Shugaban majalisar dinkin duniya, Antonio Guterres ya nuna adawa da matakin, inda ya bayyana damuwarsa kan yadda takunkumin zai tafiyar da ayyukan kotun.

Kazalika, Shugaban Haƙƙoƙin Ɗan Adam na majalisar, Volker Turk ya ƙi amincewa da takunkumin, yana mai kiran a ɗauki matakai na gaggawa domin kare ma'aikata da 'yancin kotun.

Kasashe sun yi tir da Amurka

BBC ta rahoto cewa ministan harkokin wajen na ƙasar Netherlands, Tom Berendsen, ya bayyana cewa matakin na Amurka yana da ban takaici kwarai da gaske, inda ya ce ƙasarsa za ta tsaya tsayin daka wajen kare kotun.

Kara karanta wannan

Kotun ɗaukaka ƙara ta yanke hukunci kan buƙatar bada belin Nasir El Rufai

A wata sanarwa ta haɗin gwiwa, Ministocin Harkokin Waje na Birtaniya, Denmark, France, Germany, Italy, Netherlands, Canada da Japan sun bayyana rashin amincewarsu sosai da takunkumin.

Shugaban kasar Faransa
Shugaba Emmanuel Macron na Faransa. Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Ministan Harkokin Waje na kasar Belgium, Maxime Prevot ma ya buƙaci ƙasashen Turai da su gaggauta ɗaukar matakin kare 'yancin kotun ICC.

Donald Trump ya nemi agajin Rasha

A wani labarin, mun ruwaito cewa mambobin jam'iyyar Republican da na Democrat sun haɗu a ranar Juma'a wajen sukar Shugaba Donald Trump sakamakon janye takunkumin da ya yi kan dizal ɗin Rasha.

Sanata Chris Van Hollen ya mayar da martani da cewa Trump ya haifar da yaƙin da ya jawo tashin farashin dizal sannan yanzu yana son tura wa Rasha kudi ta yaki Ukraine ta hanyar sayen mai daga gare ta.

Kazalika, ɗan majalisa Don Bacon ya jaddada cewa kashi 70 na Amurkawa suna goyon bayan Ukraine, saboda haka tallafa wa tattalin arzikin yaƙin Putin kuskure ne.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng