Kansilar APC Ta Mutu a Hannun Yan Bindiga Mako Guda bayan Sace Ta

Kansilar APC Ta Mutu a Hannun Yan Bindiga Mako Guda bayan Sace Ta

  • ’Yan bindiga sun kashe wata kansila a ƙaramar hukumar Olamaboro ta Jihar Kogi bayan sun yi garkuwa da ita
  • An sace ta ne ranar 30 ga Satumba yayin tafiyarta kasuwar Onitsha, inda maharan suka fitar da ita daga motar haya
  • An kama direban motar da wanda ya amsa kiran wayar mamaciyar domin taimakawa bincike

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Olamaboro, Kogi - Rahotanni sun nuna cewa wasu da ake zargin masu garkuwa da mutane ne sun kashe Hon. Rosemary Adukwu.

Adukwu ita kansila da ke wakiltar mazabar Ogugu ta Uku a Ƙaramar Hukumar Olamaboro ta Jihar Kogi, kwanaki bayan yin garkuwa da ita.

Kansila ta mutu a hannun yan bindiga
Marigayiya Rosemary Adukwu da ta mutu a hannun yan bindiga. Hoto: Comr Emmanuel Ameh.
Source: Facebook

Shugaban Ƙaramar Hukumar Olamaboro, Dokta Ameh Williams, ya sanar da rasuwarta a cikin wata sanarwa da ya fitar ranar Juma’a, cewar Daily Trust.

Kara karanta wannan

Yan bindiga sun shiga gari a lokacin da mutane ke hutun yamma, sun bude wuta

Yadda aka sace kansila a Kudancin Najeriya

An ce Hon. Adukwu na kan hanyarta ta zuwa kasuwar Onitsha a ranar 30 ga Satumba, 2026, lokacin da masu garkuwa da mutanen suka tare motar haya da take ciki a yankin Oji River, tsakanin jihohin Enugu da Anambra.

Rahotanni sun ce yan bindigan sun fitar da kasilar daga motar da ƙarfi, sannan suka tafi da ita zuwa wani maboyarsu a cikin daji.

Sanarwar ta ce:

“Cikin tsananin baƙin ciki muke sanar da rasuwar ’yar’uwarmu kuma abokiyar aikinmu, Hon. Rosemary Adukwu, kansila mai wakiltar al’ummar mazabar Ogugu ta Uku a Majalisar Dokokin Ƙaramar Hukumar Olamaboro ta Takwas.”

Shugaban ƙaramar hukumar ya ce an tabbatar da rasuwarta ranar Alhamis, lokacin da take hannun masu garkuwa da mutane.

Sai dai iyalan mamaciyar sun nuna damuwa kan yadda lamarin ya faru, sun yi zargin cewa masu garkuwa da mutanen sun ware kansilar ne kawai, suka bar sauran fasinjojin ba tare da sun cutar da su ba.

Kara karanta wannan

2027: Arewa ta shirya gagarumin gangamin tallata Tinubu da Shettima

Sun kuma ce masu garkuwar ba su tuntubi iyalanta domin neman kuɗin fansa ba kafin sanar da rasuwarta.

Yan bindiga sun kashe kansila a Imo
Taswirar jihar Kogi da aka kashe kansila bayan sace ta. Hoto: Legit.
Source: Original

Yadda aka gano rasuwar kansila

Wata majiya daga iyalan ta ce sun gano rasuwarta ne yayin da suke ƙoƙarin gano inda wayarta take.

A lokacin da aka kira lambar wayar, wanda ya amsa ya bayyana cewa ta rasu tana hannun masu garkuwa da mutane.

Majiyar ta ce:

“Hon. Rosemary Adukwu ta saba hawa motar wannan direban domin zuwa kasuwar Onitsha don sayen kayayyakin da take kasuwanci da su. A ranar 30 ga Satumba, ta tafi Onitsha ne bayan ta tabbatar da direban da ta saba hawa cewa za a yi kasuwa ranar 1 ga Oktoba.
“A yankin iyakar jihohin Enugu da Anambra, musamman a Oji River, motarsu ta ci karo da shingen da wasu mutane suka kafa. Daga nan, ’yan bindigar suka fitar da ita kaɗai daga motar suka tafi da ita zuwa wurin da ba a sani ba. Sauran fasinjojin kuwa suka ci gaba da tafiyarsu ba tare da an taɓa su ba."

Kara karanta wannan

Kasurgumin dan bindiga da yaransa 6 sun hadu da abin da ya fi ƙarfinsu, sun mutu nan take

Kakakin Rundunar ’Yan Sandan Jihar Kogi, ASP Saliu Oyiza Afusat, bai amsa tambayoyin da aka aika masa kan lamarin ba har zuwa lokacin kammala wannan rahoto.

Rahotanni sun nuna cewa an binne Hon. Rosemary Adukwu da misalin ƙarfe 1 na rana ranar Juma’a a gidan iyalanta da ke tsakiyar garin Ogugu.

Yan bindiga wuta kan al'umma a Benue

An ji cewa an kashe aƙalla mutane uku, ciki har da yaro mai shekaru uku, a wani hari da ake zargin makiyaya masu ɗauke da makamai sun kai a Benue.

Maharan sun kai hari kan al’ummar kauyen Omulonye da ke Ugboju Icho, a ƙaramar hukumar Otukpo, a yammacin ranar Laraba.

Rundunar ’yan sandan jihar Benue ta tabbatar da mutuwar mutane uku, yayin da wasu mazauna yankin da suka ji rauni ke karɓar magani a Otukpo.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jarida ne da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.