Jirgi Ya Fado a Amurka Ya Kashe Mutane ana Musayar Hare Hare da Iran
- Akalla mutane biyar sun rasa rayukansu, yayin da wasu biyar suka jikkata bayan jirgin dakon kaya na Amazon ya yi hatsari a filin jirgin Amurka
- Jirgin Boeing 767-300 ya ketare titin sauka ne yayin da yake kokarin sauka a filin jirgin kasa da kasa da ke jihar Miami da yammacin Lahadi
- Hatsarin ya haddasa gobara da malalar man jirgin, lamarin da ya tilasta dakatar da zirga-zirgar jiragen sama na tsawon wasu sa’o’i
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf Kari yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Miami – Akalla mutane biyar sun mutu, yayin da wasu biyar suka samu raunuka bayan wani jirgin dakon kaya na Amazon Prime Air ya yi hatsari a filin jirgin Miami International Airport.
Jirgin Boeing 767-300 ya yi hatsarin ne da kusan karfe 2 na rana ranar Lahadi, lokacin da yake kokarin sauka a filin jirgin.

Source: Facebook
BBC ta wallafa cewa hatsarin ya faru ne bayan jirgin ya wuce titin sauka, sannan ya bugi wasu motoci da dama a wata hanya da ke bayan filin jirgin.
Mutane sun mutu a hadarin
Hatsarin ya sanya jami’an agajin gaggawa sun kai dauki da wuri, wadanda suka garzaya wurin domin shawo kan gobarar jirgin da kuma malalar man fetur.
Jami’an sun ce mutane biyar ne suka mutu, yayin da wasu biyar suka jikkata, ciki har da mutum uku da ke cikin mawuyacin hali.
Hukumar kula da zirga-zirgar jiragen sama ta Amurka ta bayar da umarnin dakatar da dukkan zirga-zirgar jirage a filin jirgin na wani lokaci, lamarin da ya haddasa soke tashin jirage da dama.
Hukumar NTSB ta fara bincike
Hukumar Kula da Sufurin Jiragen Sama ta Amurka, NTSB, ta ce ta tura tawagar kwararru domin fara binciken musabbabin hatsarin.
Rahoton USA Today ya nuna cewa hukumar ta ce za ta bayyana sakamakon farko na binciken ga manema labarai a ranar Litinin.

Kara karanta wannan
Tashin hankali: Jirgin yaƙi na sojoji ya yi hatsari, ya faɗo kusa da dandazon taron mutane

Source: Getty Images
Fasinjoji sun koka
Wasu fasinjojin da suka makale a filin jirgin sun bayyana takaicinsu kan rashin samun isasshen bayani daga kamfanin jirgin da kuma hukumomin filin jirgin.
An soke tashin jirage da dama, yayin da wasu fasinjoji suka sake tsara lokutan tafiyarsu saboda hatsarin.
Wani fasinja mai suna Faroush, wanda zai tafi San Francisco, ya ce jirgin farko da ya samu bayan soke nasa shi ne a safiyar Talata.
Ya ce hakan na iya tilasta masa neman otal domin ya ci gaba da zama a Miami har sai lokacin tafiyarsa ya yi.
Amurka ta ka hari Iran
A wani labarin, mun ruwaito cewa hare-haren Amurka kan jiragen dakon man fetur na Iran na iya kara wahalar da Tehran wajen ci gaba da sayar da danyen man fetur.
Sababbin hare-haren da Amurka ta kai kan wasu jiragen dakon man Iran sun nuna karuwar matsin tattalin arziki da Washington ke yi wa Tehran.
Rundunar CENTCOM ta Amurka ta ce a ranar 5 ga Satumba ta dakile jiragen dakon mai guda biyu kusa da Kharg Island da Jask, sannan ta lalata wani jirgi na uku a Gulf of Oman.
Asali: Legit.ng
