Sarki Mohammed VI na Morocco ya ziyarci Najeriya
Sarki Mohammed VI na Morocco ya isa kasar Najeriya a ranar Alhamis, 1 ga watan Disamba, don wani ziyarar aiki.
Mataimakin shugaban kasa Farfesa Yemi Osinbajo ya tarbi sarkin sannan kuma zai ziyarci shugaban kasa Muhammadu Buhari a yau a fadar shugaban kasa Abuja.
A farko shugaban kasa ya tarbi Sharif Muhammad Kabir Ibn Muhammad na Morocco, khalifan Sheikh Ahmed Tijani a fadar shugaban kasa a ranar Talata, 29 ga watan Nuwamba, 2016.
KU KARANTA KUMA: Yan Shi'a na zanga-zanga a majalisar dokoki
Ku tuna cewa shugaban kasa Buhari ya bar Marrakech, Morocco, bayan ya halarci taron Conference of the Parties (COP) na 22 zuwa taron United Nations Framework Convention on Climate Change (UNFCCC) wanda aka fi sani da COP-22, daga Nuwamba 14 zuwa 16.
Kalli wasu hotuna a kasa:
Asali: Legit.ng