Shugaba Tinubu Ya Tura Sakon Jaje Ga Kasar Moroko Bayan Iftila’in Girgizar Kasa da Ta Auku

Shugaba Tinubu Ya Tura Sakon Jaje Ga Kasar Moroko Bayan Iftila’in Girgizar Kasa da Ta Auku

  • Sama da mutane 600 ne rahotanni suka bayyana mutuwarsu a girgizar kasar da ta faru a Maroko a ranar Juma’a 8 ga watan Satumba
  • Shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu ya jajantawa Sarkin Morocco Mohammed VI kan wannan lamari mai ban tausayi
  • Tinubu ya tabbatarwa kasar ta Moroko goyon bayan Najeriya yayin da suke cikin aikib sake ginawa da kuma fitowa da karfi fiye da kowane lokaci

FCT, Abuja - Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya mayar da martani game da mummunar girgizar kasa mai karfin awo 6.8 da ta afku a kasar Moroko a daren Juma'a 8 ga watan Satumba.

A cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Asabar, 9 ga watan Satumba, kuma aka yada a shafin X na fadar shugaban kasa, Tinubu ya mika sakon ta’aziyyarsa ga Sarki Mohammed VI na Moroko.

Kara karanta wannan

Hukuncin Kotun Zabe: A Karshe Peter Obi Ya Aika Gagarumin Sako Ga Mabiyansa

Shugaban ya jajantawa dukkan iyalan da suka rasa ‘yan uwansu da kuma duk wadanda bala’in ya shafa. Ya kuma yi fatan samun lafiya cikin gaggawa ga wadanda suka jikkata.

Tinubu ya mika sakon jaje ga kasar Moroko
Jajantawar Tinubu ga kasar Moroko | Hoto: vanguardngr.com
Asali: Facebook

Jajantawar shugaba Tinubu ga kasar Moroko

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Shugaban ya tabbatar da Mohammed VI a cikin sanarwar mai dauke da sa hannun mai taimaka masa kan harkokin yada labarai, Ajuri Ngelale cewa:

"A cikin wannan mawuyacin hali, Najeriya za ta ci gaba da kasancewa tare da Moroko yayin da take murmurewa, sake ginuwa da kuma fitowa da karfi fiye da kowane lokaci daga wannan abin alhini."

Ba wannan ne karon farko da ake samun girgizar kasa a kasashen duniya, ba a jima ba aka yi girgizar kasa a kasar Turkiya da ke yankin Turai.

Girgizar kasa kan jawo mummunar asarar rayuwa da dukiyoyi, lamarin da ke jefa al’umma cikin mawuyacin halin kakani-kayi.

Kara karanta wannan

Tallafi: Kungiyar CAN A Arewa Ta Bukaci Tinubu Ya Kawo Daukin Gaggawa, Ta Ce Akwai Babbar Matsala

Yadda girgizar kasa ta auku a kasar Moroko

A tun farko, mun ruwaito samuwar girgizar kasa mai karfin gaske a kasar Moroko, lamarin da ake fargabar ya haifar da mummunar asara a kasar.

A cewar rahotanni daga kasa, mutane kusan 632 ne suka riga mu gidan gaskiya bayan wannan iftila'in, rahoton Sky News.

A cewar bayanai daga ma'aikatar harkokin cikin gida ta kasar, wasu mutum 329 sun samu raunika, inda mutum 51 ke cikin mawuyacin hali.

Hakazalika, rahoton ya bayyana adadin mutanen da suka samu raunuka da kuma wadanda a halin yanzu suke cikin mawuyacin hali.

Asali: Legit.ng

Online view pixel