Trump Ya Bukaci 'Yan Amurka da ke Iran Su Dauki Wani Matakin Gaggawa
- Ofishin Jakadancin Amurka a Iran ya gargadi ’yan ƙasar Amurka da su bar Iran nan take saboda ƙara tabarbarewar yanayin tsaro a yankin
- Ofishin ya ce akwai yiwuwar soke tashin jiragen sama ko kuma rufe sararin samaniyar ƙasar, lamarin da ka iya wahalar da ficewar jama’a
- Gargadin ya zo ne yayin da Amurka da Iran ke ci gaba da fuskantar barazanar ƙarin rikici, duk da wasu alamomin da ke nuna yiwuwar sake komawa teburin tattaunawa
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf Kari yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
FCT, Abuja – Ofishin Jakadancin Amurka a Iran ya shawarci ’yan ƙasar Amurka da ke Iran da su fice daga ƙasar nan take, tare da gargadin cewa za a iya soke zirga-zirgar jiragen sama ko kuma rufe sararin samaniya.
Ofishin ya kuma gargadi ’yan Amurka da kada su je Iran ko da kuwa saboda wani dalili, yayin da ake samun ƙarin barazanar tsaro a yankin.

Kara karanta wannan
Abu ya girma: Shugaba Tinubu ya ɗauki zafi kan kutuwar matasa 37 a wajen hukumar NSCDC

Source: Facebook
Amurka ta fitar da gargadi
Tashar Al Jazeera ta wallafa cewa a cikin wata sanarwa da ofishin ya wallafa a shafinsa na intanet ranar Lahadi, ya ce:
“Kar ku yi tafiya zuwa Iran saboda kowane dalili. Ya kamata ’yan ƙasar Amurka su bar Iran da gaggawa.”
Ofishin ya bayyana yanayin tsaron ƙasar a matsayin mai sarkakiya, tare da yiwuwar samun wani yanayi da ba a yi tsammani ba.
Ya kuma shawarci ’yan Amurka da su ƙara taka-tsantsan tare da tuntubar kamfanonin jiragen sama kai tsaye domin samun bayanan da suka shafi tashin jirage da ficewa daga ƙasar.
Rikicin yankin na iya ƙara muni
Gargadin na Amurka ya kuma ambaci rikicin da ya shafi Houthi masu samun goyon bayan Iran da Saudi Arabia, ciki har da hare-haren da suka shafi filayen jiragen sama na fararen hula.
Rahoton Iran International ya nuna cewa ofishin ya ce wannan rikicin na da damar ƙara tsananta cikin sauri, lamarin da ya ƙara janyo damuwa kan tsaron yankin.
Iran na nuna shirin tattaunawa
A Iran kuwa, jami’an ƙasar sun ci gaba da aika saƙonni biyu a lokaci guda, na nuna shirye-shiryen tattaunawa da kuma shirye-shiryen tunkarar wani sabon rikici.
Sakatare na Majalisar Tsaro ta Ƙasa ta Iran, Mohsen Rezaei, ya ce ana gudanar da tattaunawa ta hanyar masu shiga tsakani daga Pakistan da Qatar.

Source: Getty Images
Iran kuma na sa ran wata tawagar Pakistan da ministan cikin gida zai jagoranta za ta isa ƙasar, lamarin da ke nuna yiwuwar samun ƙarin tattaunawar diflomasiyya.
Sai dai jami’an Iran sun kuma ce ƙasar a shirye take ta fuskanci wani sabon zagaye na rikici idan aka sake samun tashin hankali.
Sharudan Iran kan Hormuz
A wani labarin, kun ji cewa babban mai shiga tsakani na Iran, Mohammad Bagher Ghalibaf, ya ce Tehran ta sanar da Amurka sharudan da take buƙata domin sake buɗe mashigin Hormuz ta hannun masu shiga tsakani.
Bangarorin biyu sun ci gaba da samun takaddama watanni bayan fara rikicin da ya biyo bayan hare-haren Amurka da Isra’ila kan Iran a ƙarshen watan Fabrairun 2026.
Tun daga lokacin, Tehran ta ci gaba da hana zirga-zirga a mashigar Hormuz, yayin da Washington ke matsa wa Iran ta fuskar tattalin arziki da kokarin takaita ayyukan tashoshin jiragen ruwa na ƙasar.
Asali: Legit.ng
