Tashin Hankali: Jirgin Yaki na Sojoji Ya Yi Hatsari, Ya Fado Kusa da Dandazon Taron Mutane
- Jirgin sojojin kasar Girka kirar F-4 Phantom ya yi hatsari a yau Asabar, inda aka ruwaito cewa duka matukan da ke ciki sun mutu
- Rahotanni sun ce fashewa ta faru nan take bayan jirgin ya fadi, yayin da dubban mutane ke kallon taron Athens Flying Week
- Jiragen kashe gobara guda 11, ciki har da jirage masu saukar ungulu, sun dura wurin domkn aikin shawo kan wutar da ta bazu zuwa wani daji
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Jirgin yakin sojoji kirar F-4 Phantom ya yi hatsari a ranar Asabar, 5 ga Satumba, 2026 a wani sansanin soji da ke wajen birnin Athens na kasar Girka yayin wani babban baje kolin jiragen sama.
Kamfanin dillancin labarai na Girka, ANA, ya ruwaito cewa da farko ba a bayyana musabbabin faduwar jirgin ba.

Source: Getty Images
Haka kuma, rahotannin farko da jaridar Vanguard ta wallafa sun nuna cewa ba a tabbatar da halin da matukan jirgin biyu suke ciki ba bayan aukuwar lamarin.
Jirgin sojojin Girka ya yi hatsari
Wani dan jarida daga gidan talabijin na gwamnati ERT, wanda ke wurin da lamarin ya faru, ya ce jirgin ya tashi ne daga filin jirgin kafin daga bisani ya rasa tsayi kwatsam ya fadi.
Rahotanni sun ce fashewa ta faru nan take bayan jirgin ya fadi, yayin da dubban mutane ke kallon taron Athens Flying Week na shekara-shekara.
An tura jirgin sama mai saukar ungulu na hukumar kashe gobara zuwa wurin domin kashe wutar da hatsarin ya haddasa.
Ministan tsaron kasar Girka, Nikos Dendias, ya soke wata tafiya da zai yi zuwa bikin baje koli na kasa da kasa da ake gudanarwa a Thessaloniki domin kai ziyara wurin da hatsarin ya faru.
Matukan jirgin sun rasa rayukansu

Kara karanta wannan
Ana shirin zaben 2027, an fito da abin da ya faru lokacin da aka shirya yi wa Tinubu juyin mulki
Wani jami'i ya tabbatar wa kamfanin dillancin labarai na Reuters da cewa matukan jirgin biyu sun mutu a hatsarin.
Jami'in ya ce jirgin ya fadi ne kimanin kilomita biyu daga filin jirgin, yana mai cewa babu rahoton wani mutum daga cikin jama'a ko mazauna yankin da ya ji rauni.
Hotunan da gidan talabijin na ERT ya nuna sun nuna jirgin F-4 ya rika juawa zuwa bangaren dama a 'yan mitoci kadan sama da kasa kafin ya fadi ya kama da wuta.
An yi kokarin kawar da mutane
Jiragen kashe gobara guda 11, ciki har da jirage masu saukar ungulu, sun dura wurin domkn aikin shawo kan wutar da ta bazu zuwa wani daji da ke kusa.
Wani ganau ya shaida wa ERT cewa:
“Dukkanmu mun shiga cikin rudani. Jirgin bai wuce mintuna uku da tashi ba.”
Rahotanni sun ce an yi amfani da lasifika a sansanin sojin wajen kira ga jama'a da su bar yankin bayan faruwar hatsarin.
Jirgin F-4 din na daga cikin jiragen da ke halartar Athens Flying Week, wani taron shekara-shekara da ke hada tawagogin jiragen sama na soja da farar hula daga kasashe da dama.

Kara karanta wannan
Da gaske Opay zai daina aiki kuma yan Najeriya za su rasa kuɗaɗensu? Gaskiya ta fito
Jirgin yawon bude ido ya yi hatsari
Kun ji cewa jirgin sama mai saukar ungulu ya yi hatsari a Dutsen Ololokwe da ke Samburu a Kenya, inda dukkan mutane shida da ke cikinsa suka mutu.
Hukumar Kula da Sufurin Jiragen Sama ta Kenya (KCAA) ta ce jirgin na kan wani yawon shakatawa ta sama ne daga wani wurin kiwon namun daji a Losaiba zuwa Ewaso Nyiro,
Asali: Legit.ng
