Amurka Ta Kaddamar da Sababbin Hare Hare kan Jirgin Iran

Amurka Ta Kaddamar da Sababbin Hare Hare kan Jirgin Iran

  • Jirgin ruwan dakon man fetur na Iran ya fuskanci harin makamai masu linzami daga sojojin Amurka kusa da tsibirin Kharg
  • Rahotanni sun bayyana cewa an harba makamai masu linzami guda hudu kan jirgin, duk da babu rahoton rasa rayuka
  • Nan take aka fara kwashe ma’aikatan jirgin bayan harin Amurka, kamar yadda wata kafar yada labarai ta Iran ta bayyana

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf Kari yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Tehran – Wani jirgin ruwan dakon man fetur na Iran ya fuskanci hari daga sojojin Amurka a ranar Asabar kusa da yankin tashar jiragen ruwa na tsibirin Kharg da ke mashigar tekun Gulf.

Rahotanni sun ce jirgin ya fuskanci harin ne a yankin da ake ajiye jiragen ruwa a kusa da tsibirin, lamarin da ya kara sanya fargaba kan makomar masana’antar man fetur ta Iran.

Kara karanta wannan

An ce sojojin Amurka sun tonawa Trump asiri kan yakin Iran, ana bincike

Shugaba Donald Trump
Wajen da aka kai hari da Donald Trump abgefen dama. Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Tasahr Iran ta Tasnim ta ruwaito cewa wakilinta da ke Kharg ya ce an harba makamai masu linzami guda hudu kan jirgin.

Babu asarar rai da aka tabbatar

Wasu majiyoyin yankin sun ce babu wanda ya rasa ransa sakamakon harin, yayin da ake ci gaba da kwashe ma’aikatan jirgin zuwa wani wuri mai tsaro.

Har zuwa lokacin wallafa rahoton, hukumomin Iran ba su fitar da sanarwar hukuma kan lamarin ba.

Haka kuma, Rundunar Sojin Amurka ta CENTCOM ba ta mayar da martani nan take kan bukatar yin bayani game da harin ba.

Trump ya taba barazana a Kharg

A ranar 31 ga watan Agusta, Shugaban Amurka Donald Trump ya wallafa wani sako a shafinsa na sada zumunta tare da wani bidiyo da aka samar da fasahar AI, inda ya ce ana “tarwatsa tsibirin Kharg”.

Rahoton Reuters ya nuna cewa hukumomin Iran sun sha alwashin mayar da martani mai karfi idan Amurka ta kai hari kan tsibirin.

Kara karanta wannan

Yadda Rasha ke taimakon Iran wajen hada makamai masu linzami

Iran na dogaro da Kharg

Iran ita ce kasa ta uku wajen samar da man fetur a cikin kasashen OPEC, inda kafin yakin ta rika fitar da kusan kashi 90 cikin 100 na danyen man da take samarwa ta tsibirin Kharg.

Sai dai tun bayan fara takunkumin hana fitar da man Iran da Amurka ta kakaba a tsakiyar watan Afrilu, jigilar man ta samu cikas.

Wani hari kan Kharg na iya kara matsin lamba kan masana’antar man fetur ta Iran da tattalin arzikinta baki daya, wanda tuni ke fama da matsin lamba sakamakon takunkumin sojin ruwa na Amurka.

Mojtaba Khamenei a Iran
Jagoran Iran, Mojtaba Khamenei. Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Ana binciken sojin Amurka

A wani labarin, mun ruwaito cewa gwamnatin Amurka ta sanya kusan jami’an rundunar sojin hadin gwiwa 50 cikin gwajin gano karya yayin da ake gudanar da bincike kan fallasa bayanan sirri ga ‘yan jarida.

Rahotanni sun ce binciken ya mayar da hankali kan ko wasu jami’an soji da ma’aikatan farar hula sun fitar da bayanan sirri ga manema labarai, ciki har da bayanai kan raguwar makaman Amurka.

An gudanar da gwaje-gwajen ne a watan Agusta, bayan wasu rahotannin kafafen yada labarai sun bayyana Amurka na fama da karancin wasu muhimman makamai.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng