Ana Shirin Zaben 2027, An Fito da Abin da Ya Faru lokacin da Aka Shirya Yi Wa Tinubu Juyin Mulki

Ana Shirin Zaben 2027, An Fito da Abin da Ya Faru lokacin da Aka Shirya Yi Wa Tinubu Juyin Mulki

  • Ministan Tsaro, Christopher Musa, ya ce an gurfanar da wadanda ake zargi da hannu a yunkurin hambarar da gwamnatin Bola Tinubu a gaban kotu
  • Musa ya tabbatar da cewa yunkurin juyin mulkin na gaske ne, yana mai cewa wadanda ake zargin sun shirya kwace mulki
  • Ya ce bincike ya nuna cewa wasu daga cikin wadanda ake zargin sun shiga shirin ne saboda neman kudi da wasu anfani na kansu

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Abuja - Ministan Tsaro, Christopher Musa, ya tabbatar da cewa an gurfanar da wadanda aka kama kan zargin shirya hambarar da gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu a gaban kotu.

Musa, tsohon janar na sojin Najeriya mai ritaya, ya tabbatar da cewa da gaske an yi yunkurin kifar da Shugaba Bola Tinubu, amma hakar ba ta cimma ruwa ba.

Kara karanta wannan

Lauya ya tsage gaskiya, an ji dalilin da ya sa Amurka ba ta kama Shugaba Tinubu ba

Musa.
Ministan Tsaron Najeriya kuma tsohon babban hafsan tsaro, Janar Christoher Musa Hoto: @DHQNigeria
Source: Facebook

Tsohon babban hafsan tsaron Najeriya ya bayyana hakan ne a ranar Alhamis yayin wata hira da gidan talabijin na Channels a shirinsa na Politics Today.

Ministan ya yi bayani kan halin da bincike kan zargin yunkurin juyin mulkin da aka gano a shekarar 2025 yake ciki

Ya ce yunkurin na gaske ne, kuma masu bincike sun tabbatar da cewa wadanda ake zargi suna da niyyar kwace mulki.

“Yunkurin juyin mulkin na gaske ne, kuma da gaske suna da niyyar aikata shi,” in ji Musa.

Dalilin da ya sa assska shirya juyin mulki

A cewar ministan, babban abin da ya sanya wadanda ake zargi shiga wannan shiri shi ne neman kudi, ba wani dalili na akida ko siyasa ba.

Ya ce:

“Yunkurin na gaske ne, kuma da gaske suna son aikata shi saboda wasu dalilai. Amma idan ka ji dalilin da ya sa suka so aikata hakan, za ka gane cewa wasu mutane ne da suka bace hanya, wadanda suka shiga lamarin saboda kudi kawai.”

Kara karanta wannan

Yadda batun maido tallafin mai ya zafafa adawa tsakanin Tinubu da Atiku

Musa ya ce babu wani kwakkwaran dalili da zai iya tabbatar da matakin da suka yi yunkurin dauka.

An kai wadanda ake zargi gaban kotu

Ministan ya ce da farko hukumomin tsaro sun tsare wadanda ake zargi domin gudanar da bincike. Sai dai ya ce yanzu an mika su ga kotuna domin fuskantar shari'a.

Ya ce batun ya fita daga hannun sojoji, domin yanzu yana gaban bangaren shari'a.

Shugaba Tinubu.
Shugaban kasa, Mai girma Bola Ahmed Tinubu lokacin da ya kai wata ziyara kasar Birtaniya Hoto: @aonanuga1956
Source: Getty Images

A rahoton Premium Times, Musa ya kara da cewa:

“Na yi imanin an gudanar da bincike a kansu. An kai su kotu, don haka yanzu batun yana hannun kotuna. Ba ya hannunmu, yana gaban kotuna.”

An gano zargin yunkurin juyin mulkin ne a karshen watan Satumban 2025, lamarin da ya kai ga cafke jami'an soji da wasu mutane.

Yadda sojoji ke ceto mutane a daji

A wani rahoton, kun ji cewa ministan tsaro, Christopher Musa, ya bayyana dabarun da rundunonin tsaro ke amfani da su wajen ceto mutanen da aka sace ba tare da sun kashe 'yan ta'addan ba.

Ya bayyana cewa dabarar ta haɗa da kewaye 'yan ta ta'adda, katse musu hanyoyin gudu da kuma hana su samun abinci, ruwa, fetur da sauran kayan masarufi

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262