Kano da Wasu Jihohi 7 da Cutar 'Diphtheria' Ta Fi Kama Mutane, NCDC Ta Gano Matsalar

Kano da Wasu Jihohi 7 da Cutar 'Diphtheria' Ta Fi Kama Mutane, NCDC Ta Gano Matsalar

  • Hukumar NCDC ta bayyana cewa galibin wadanda suka kamu da cutar mashako watau diphtheria ba su yi rigakafi na
  • Ta kuma jero jihohi takwas da cutar ta fi yaduwa, wadanda ta ce 98% na masu dauke da wannan cuta suna wadannan jihohi
  • Hukumar ta bukaci iyaye su tabbatar sun yi wa 'ya'yansu da sauran wadanda ke karkashinsu da suka cancanta rigakafi

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Abuja, Nigeria - Hukumar Kula da Cututtuka masu Yaduwa ta Najeriya (NCDC) ta bayyana cewa kashi 68 cikin 100 na mutanen da aka tabbatar suna dauke da cutar diphtheria ba su taba yin rigakafin cutar ba.

Ta ce kashi 28 cikin 100 na wadanda aka tabbatar suna dauke da cutar ba su san matsayin rigakafinsu ba, yana mai cewa yawancin wadanda suka mutu sakamakon cutar ba su yi rigakafi ba.

Kara karanta wannan

Shugaban da ya nemi mata su kashe aurensu kan zaben APC ya magantu

Jide Idris.
Shugaban hukumar NCDC ta Najeriya, Dr. Jide Idris a wurin taron wayar da kai Hoto: @NCDCgove
Source: Twitter

Babban jami'in yada bayanan lafiya na NCDC, Michael Okali, ne ya bayyana hakan a wata hira da Channels Television ranar Asabar, 5 ga watan Satumba, 2026.

NCDC ta gano dalilin yaduwar cutar

Okali, wanda kuma shi ne shugaban bangaren sadarwa kan haɗari, hada kan al'umma da yaki da yada bayanan karya a tsarin kula da annobar diphtheria na kasa, ya ce kowa na cikin haɗarin kamuwa da cutar.

Ya ce wadanda ba su cika yin rigakafin da ya kamata ba na iya yada cutar ga wasu mutane cikin sauki.

Jami'in ya bukaci iyaye su tabbatar sun yi wa 'ya'yansu da sauran wadanda ke karkashinsu da suka cancanta rigakafi.

An bukaci mutane su yi rigakafi

A cewarsa, ana yin rigakafin kyauta a dukkan cibiyoyin kula da lafiya na matakin farko, sai dai ya ce gaggauta sanar da jami'an lafiya idan aka lura da alamun cutar na iya taimakawa wajen dakile yaduwarta.

Kara karanta wannan

Sirrin yadda sojoji ke ceto mutane a daji ba tare da kashe 'yan ta'adda ba

Ya ce:

“Wannan ne ya sa muke bayar da shawarar a kammala dukkan rigakafin da ake bukata. Ga jarirai, ana yin rigakafin a mako na shida, na 10 da na 14.
"Idan mutum bai tabbatar da matsayin rigakafinsa ba, akwai karin rigakafi mai suna Td ko Tdap, wanda ya kunshi rigakafin diphtheria, tetanus da pertussis. Ana iya amfani da shi wajen kara garkuwar jikin mutum.”

Jihohi 8 da cutar mashako ta yadu

Okali ya ce jihohi takwas ne cutar ta fi yaduwa, wadanda alkaluma suka nuna suna dauke da kashi 98 cikin 100 na wadanda aka tabbatar sun kamu da cutar diphtheria a Najeriya.

Jihohin sun hada da Kano, Kaduna, Katsina, Borno, Bauchi, Filato, Sakkwato da Zamfara, kamar yadda Vanguard ta ruwaito.

Rigakafi.
Yadda ake yin allurar rigakafi domin kauce wa kamuwa da cututtuka Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

A cewarsa, daga ranar 24 zuwa 30 ga watan Agustan 2026, Najeriya ta samu mutane 69 da ake zargin sun kamu da cutar, yayin da aka tabbatar da mutane 48 sun kamu, sannan mutane hudu suka mutu.

Kara karanta wannan

Tinubu ya yi wa gwamnoni umarni su inganta rayuwar talaka

Da gaske cutar ta kashe yara 50?

Kun ji cewa gwamnatin Kano ta musanta rahoton cewa yara 50 sun mutu sakamakon barkewar cutar mashako watau diphtheria a yankin karamar hukumar Rano.

KNCDC ta ce mutum biyu ne suka mutu a Rano a 2026, yayin da jimillar mutanen da suka mutu a yankin daga Yuli 2023 zuwa Agusta 2026 ta kai 29

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262