Sabon Farashin Man Fetur Ya Jefa Yan Kasuwa a Fargaba, Lita Ta Doshi N1,300
- Yan kasuwar man fetur sun ce farashin fetur ya tashi zuwa tsakanin N1,250 da N1,300 kan lita a wasu wurare, lamarin da ya daga masu hankali
- IPMAN ta ce sauyin farashin ɗanyen mai, manufofin gwamnati da canjin darajar Naira na ƙara jefa ’yan kasuwa cikin rashin tabbas
- Matatar Dangote ta ƙara farashin fetur a tasharta da N15, daga N1,185 zuwa N1,200 kan lita, kasa da mako guda bayan ƙarin farashin baya
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Nigeria – ’Yan kasuwar man fetur sun nuna damuwa kan ci gaba da tashin farashin man fetur, inda suka ce farashin zai iya kai wa tsakanin N1,250 zuwa N1,300 kan lita a wasu sassan Najeriya.
Hakan ya biyo bayan sabon ƙarin farashin da Matatar Man Fetur ta Dangote ta yi, lamarin da ya sa ’yan kasuwar ke fuskantar ƙarin matsala wajen tsara harkokin kasuwancinsu.

Source: Original
Punch News ta kawo labarin cewa Sakataren yaɗa labarai na Ƙungiyar ’Yan Kasuwar Man Fetur Masu Zaman Kansu ta Najeriya (IPMAN), Chinedu Ukadike, ne ya bayyana hakan.
Ana fargaba kan farashin fetur a Najeriya
Ya ce sauyin da ake samu a kasuwar mai ta duniya, manufofin gwamnati da kuma canjin darajar Naira na sa kasuwar man fetur ta kasance cikin rashin tabbas.
Matatar Dangote ta ƙara farashin fetur da take sayarwa daga tasharta da N15 kan kowace lita ranar Laraba, inda farashin ya tashi daga N1,185 zuwa N1,200. Sabon farashin ya fara aiki ne daga ranar 26 ga Agusta, 2026.
Wannan ƙarin ya zo ne kwanaki biyar kacal bayan da matatar ta ƙara farashin fetur daga N1,165 zuwa N1,185 kan lita da ta ke sayar wa abokan huldarta a kasar nan.
Farashin fetur na raguwa a duniya
Da yake magana kan sabon ƙarin, Ukadike ya ce abin ya zo ne a lokacin da farashin ɗanyen mai a kasuwar duniya ke raguwa. Ya ce ’yan kasuwar na fama da wasu abubuwa da ke ci gaba da haifar da rashin tabbas a kasuwar man fetur.

Kara karanta wannan
Ba irin na baya ba ne"; Amaechi ya fayyace shirin Atiku na dawo da tallafin fetur

Source: Getty Images
A kalamansa:
“Muna fuskantar ƙalubalen sauyin yanayin kasuwa. Akwai manufofin gwamnati, manufofin kasuwar duniya da kuma canjin darajar kuɗi. Waɗannan abubuwa ne da ke haifar da ƙarin farashin da ake samu a gidajen mai. Mu ba masu tace mai ba ne da za mu iya ƙayyade farashin kayayyakin man fetur."
Sai dai Ukadike ya ce a baya Matatar Dangote ta kasance tana rage farashinta idan yanayin kasuwar duniya ya sauya, amma a wannan lokaci ba haka ne ya samu ba.
Jigon ADC ya y i magana kan man fetur
A baya, kun ji cewa jigon jam’iyyar ADC, Ralph Nwosu, ya ce Atiku Abubakar zai rattaba yarjejeniya da ’yan Najeriya kan farashin man fetur idan ya lashe zaɓen 2027.
Mr. Nwosu ya ce yarjejeniyar za ta bayyana farashin man fetur da sauran manufofin tattalin arzikin Atiku Abubakar da ya shirya kawo wa jama'a sauki idan sun hau mulki.
Ya ce tawagar kamfen ɗin Atiku na tsara shirin kwanaki 100 na farko na gwamnatin sa domin tabbatar da cewa alkawuran sun tabbata idan an zabe shi
Asali: Legit.ng
