Iran Ta Kashe Sojojin Amurka da Dama da Ta kai Masu Jerin Hare Hare
- Iran ta kai hare-haren ramuwar gayya kan sansanonin sojojin Amurka da ke Jordan, Kuwait da Bahrain, bayan da Amurka ta sake kai mata hare-hare
- Hare-haren sun jawo karar ƙararrawa da fashe-fashe a wasu daga cikin ƙasashen, yayin da hukumomi suka ce an yi amfani da tsarin kariyar sama
- Iran ta ce ta kai hari kan sansanonin Amurka a Erbil da sauran sassan Iraki, yayin da Jordan ta tabbatar da tare makamai masu linzami 10 da aka harba
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf Kari yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Iran – Iran ta ƙaddamar da hare-haren ramuwar gayya kan sansanonin sojojin Amurka a Jordan, Kuwait da Bahrain, bayan da Amurka ta sake kai hare-hare kan wuraren dakarun IRGC a Iran ranar Talata.
Hare-haren sun faru ne cikin daren Talata zuwa Laraba, inda ƙasashen da abin ya shafa suka kunna ƙararrawar gargaɗi tare da amfani da tsarin kariyar sama.

Source: Getty Images
Iran ta farmaki Kuwait da Bahrain
Al Jazeera ta wallafa cewa Kuwait ta ce tsarin kariyar sararin samaniyarta ya tunkari hare-haren jirage marasa matuƙa da ta bayyana a matsayin “ta’addancin Iran”.
A cikin wata sanarwa da rundunar sojin Kuwait ta fitar, ta ce karar fashe-fashe da aka ji na faruwa ne sakamakon amfani da tsarin kariyar sama wajen tare hare-haren.
A Bahrain kuwa, Ma’aikatar Cikin Gida ta sanar da “faɗakarwa kan yiwuwar barazana”, yayin da kafafen yaɗa labarai suka ruwaito cewa an ji fashe-fashe akalla huɗu a jere.
Bayanin da Iran ta yi
Rundunar IRGC ta ce ta kai wani hari na makamai masu linzami da jirage marasa matuƙa kan sansanonin sojojin Amurka da ke Erbil, babban birnin yankin Kurdistan na Iraki.
Rundunar ta yi iƙirarin cewa harin ya lalata cibiyar gyaran kayan aiki da rumbunan kayan fasaha na sojojin Amurka, tare da lalata wani tsarin jagorantar leƙen asiri da ake amfani da shi a sansanin.
IRGC ta kuma yi zargin cewa mayakanta sun banka wa wuraren ajiyar man fetur na sansanin wuta tare da kashe wasu daga cikin sojojin Amurka.

Source: Getty Images
Jerussalem Post ta wallafa cewa har zuwa lokacin wallafa rahoton, Amurka da gwamnatin Iraki ba su tabbatar da waɗannan hare-haren ba.
Sai dai kakakin IRGC ya yi iƙirarin cewa Iran ta kai hari kan sansanin sojojin ruwan Amurka da ke Jordan da makamai masu linzami, inda ya ce an kashe sojojin Amurka da dama.
A wata sanarwa ta baya, kakakin IRGC ya ce dakarun rundunar sun kai wani gagarumin hari da makamai masu linzami kan wuraren ajiye jiragen sama marasa matuƙa kirar RQ-4 da MQ-9 a sansanin Prince Hassan da ke Jordan.
Sojan Amurka ya yi murabus
A wani labarin, mun ruwaito cewa Shugaban Sojin Amurka, Dan Driscoll, ya gabatar da takardar murabus dinsa ga Shugaba Donald Trump.
Majiyoyi da dama sun ce matakin ya zo ne bayan tsawon watanni ana samun rashin jituwa tsakanin Driscoll da Ministan Tsaron Amurka, Pete Hegseth.
Wata majiya ta ce Driscoll ya bayyana damuwarsa kan sauye-sauyen da ake shirin yi wa rundunar sojin ƙasa da kuma shirye-shiryen yaƙi.
Asali: Legit.ng

