Kalaman Putin Sun Faranta wa Kasar Iran Rai yayin da Take Yaki da Amurka

Kalaman Putin Sun Faranta wa Kasar Iran Rai yayin da Take Yaki da Amurka

  • Shugaban Iran Masud Pezeshkian ya gode wa Vladimir Putin kan goyon bayan Moscow ga Tehran yayin yaki da Amurka
  • Pezeshkian ya ce alakar Iran da Rasha ta kasance mai muhimmanci, yana mai cewa kasashen za su hada kai wajen yaki da danniya
  • Putin ya tabbatar da goyon bayan Rasha ga al’ummar Iran, tare da cewa Moscow za ta ci gaba da huldar tattalin arziki da kasuwanci

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Tehran, Iran - Shugaban kasar Iran, Masud Pezeshkian, ya gode wa Shugaban Rasha Vladimir Putin kan matsayin Moscow game da yakin Gabas ta Tsakiya.

Majiyoyi sun tabbatar da cewa wannan shi karon farko da suka hadu tun bayan fara rikicin Iran da kuma Amurka.

Shugaban Iran ya gana da Putin
Shugaban Iran, Masoud Pezeshkian a hagu da Vladimir Putin na Rasha a dama. Hoto: Anadolu Ajansi.
Source: Getty Images

Rahotanni sun ce Rasha ta bai wa Iran hotunan tauraron dan Adam da wasu bayanan sirri, wadanda suka taimaka wa Tehran wajen kai hari kan sansanonin Amurka da ke yankin Tekun Fasha a cikin watannin baya, cewar Al Jazeera.

Kara karanta wannan

Lauya ya tsage gaskiya, an ji dalilin da ya sa Amurka ba ta kama Shugaba Tinubu ba

Kasashen biyu sun kuma kara fadada huldar soji da tattalin arziki tsakaninsu a cikin shekarun baya.

Pezeshkian ya bayyana alakar Iran da Rasha a matsayin “dabarun hadin gwiwa”, yana mai cewa Tehran da Moscow za su iya yin aiki tare wajen tinkarar abin da ya kira “son-kai na Amurka”.

Ya bayyana hakan ne yayin ganawarsa da Putin a gefen taron kungiyar Shanghai Cooperation Organization, SCO, da aka gudanar a Bishkek, babban birnin Kyrgyzstan, ranar 1 ga Satumba.

Iran ta ci gaba da matsa lamba a mashigar Hormuz, wadda ke da muhimmiyar rawa wajen jigilar man fetur da iskar gas a duniya, lamarin da ya sa hanyoyin zirga-zirgar jiragen ruwa na kasa da kasa suka tsaya cik.

A yayin taron SCO, Pezeshkian ya ce Tehran har yanzu a shirye take ta koma kan teburin diflomasiyya, amma sai Washington ta koma ga alkawuran da ta dauka karkashin yarjejeniyar watan Yuni.

Shugaban Iran ya godewa takwaransa na Rasha
Shugaban Iran, Masoud Pezeshkian. Hoto: Anadolu Ajansi.
Source: Getty Images

Putin ya magantu kan ganawa da Pezeshkian

Kara karanta wannan

An shiga tashin hankali da 'yan bindiga suka hallaka shugaban APC a Kano

A nasa bangaren, Putin ya ce Moscow na nuna hadin kai da al’ummar Iran wajen fafutukar kare muradunsu.

Shugaban na Rasha ya kuma ce Moscow da Tehran za su ci gaba da huldar tattalin arziki da kasuwanci duk da yanayin soja da siyasa da ake ciki.

Putin ya ce:

“Mun yi maraba da rattaba hannu kan yarjejeniyar fahimtar juna tsakanin Iran da Amurka kan tsagaita bude wuta a watan Yunin wannan shekara, amma abin takaici, tsagaita bude wutar ya kasance marar tabbas kuma mai rauni sosai.”

Ya kara da cewa a wannan mawuyacin lokaci, Rasha na kokarin bai wa Iran tallafin da take bukata, tare da samar mata da kayayyakin da take bukata, cewar Jerusalem Post.

Iran ta kulla yarjejeniya da Rasha

A baya, an ji cewa shugaban Iran, Masoud Pezeshkian, da takwaransa na Rasha, Vladimir Putin, na shirin ganawa a mako mai zuwa.

Jakadan Iran a Rasha ya ce ganawar za ta gudana ne a yayin taron ƙungiyar SCO da za a yi a Kyrgyzstan.

Ganawar na zuwa ne bayan Iran da Rasha sun cimma yarjejeniyar gina sabbin tashoshin makamashin nukiliya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jarida ne da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.