Ba Sauki: Matatar Dangote Ta Sake Kara Farashin Man Fetur

Ba Sauki: Matatar Dangote Ta Sake Kara Farashin Man Fetur

  • Matatar Dangote ta kara farashin fetur da N65, inda farashin ya tashi daga N1,200 zuwa N1,265 kan kowace lita daga ranar Asabar
  • Karin na baya-bayan nan shi ne na uku cikin kwanaki takwas, inda jimillar karin farashin fetur ya kai N100, wato kashi 8.6 cikin 100
  • Masana harkar man fetur sun yi hasashen cewa karin zai iya haifar da sabon tashin farashin fetur a gidajen mai da kuma kudin sufuri

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

​​​​​​​​​​​​​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Jihar Legas - Matatar Man Fetur ta Dangote ta kara farashin sayar da Premium Motor Spirit, wanda aka fi sani da fetur, da N65 kan kowace lita.

Sabon karin ya daga farashin da matatar ke sayar wa dillalai daga N1,200 zuwa N1,265 kan kowace lita.

Farashin fetur ya karu a matatar Dangote
Motocin jigilar man fetur a matatar Dangote Hoto: Dangote Industries Limited
Source: Facebook

Matatar ta sanar da cewa sabon farashin zai fara aiki daga ranar Asabar, lamarin da ake sa ran zai iya shafar farashin fetur a fadin Najeriya, cewar rahoton jaridar The Punch.

Kara karanta wannan

Sowore: DSS ta dakatar da kararta kan dan takarar shugaban kasa, an ji dalili

Wannan shi ne karo na uku da matatar ta kara farashin fetur cikin kwanaki takwas, inda jimillar karin da aka samu a wannan lokaci ya kai N100 kan kowace lita.

Matatar Dangote ta sauya farashin sau uku

Bayanin karin farashin ya kunshi wata sanarwar canjin farashi daga kamfanin Dangote Petroleum Refinery and Petrochemicals FZE da aka gani.

Matatar ta kuma kara farashin fetur na lodawa daga teku daga N1,582,380 zuwa N1,669,545 kan kowace metric tonne.

Kamfanin ya umarci kwastomominsa da su mayar da dukkan takardun Authorisations to Collect (ATCs) da suke da su domin sake farashi kafin a loda musu kayayyakin.

Kamfanin ya ce za a ba su sababbin kwangilolin adadin man da za a loda kafin a ci gaba da jigilar kayayyakin.

A ranar 21 ga watan Agusta, matatar Dangote ta kara farashin fetur daga N1,165 zuwa N1,185 kan kowace lita.

Bayan kwanaki biyar, wato ranar 26 ga Agusta, ta sake kara N15, inda farashin ya koma N1,200 kan kowace lita.

Kara karanta wannan

Sabon farashin man fetur ya jefa yan kasuwa a fargaba, lita ta doshi N1,300

Sabon karin N65 da aka sanar a yanzu ya sa farashin ya kai N1,265, wanda ke nufin an samu karin N100 cikin sama da mako guda.

Ana sa ran farashin fetur zai sake tashi

Masu ruwa da tsaki a harkar man fetur na ganin cewa sabon karin zai iya tilasta masu dillalan man fetur kara farashin da suke sayarwa a gidajen mai.

Hakan na iya haifar da karin farashin fetur a gidajen mai, musamman yayin da ‘yan kasuwa ke sake tsara farashin kayayyakin da suke da su domin daidaita shi da sabon kudin saye.

Rahotanni sun danganta karin farashin da sauye-sauyen da ake samu a kasuwar man fetur ta duniya, musamman karuwar kudin jigilar danyen mai da kayayyakin man fetur.

Haka kuma, tashin hankali tsakanin Iran da Amurka ya kara jawo fargaba kan yiwuwar matsalolin samar da danyen mai da kuma tasirinsa kan farashin kayayyakin man fetur a duniya.

Matatar Dangote ta kara farashin fetur
Motocin dakon mai a matatar Dangote Hoto: Dangote Industries Limited
Source: Facebook

Allah ya kawo mana sauki

Yusuf Ahmad ya nuna damuwarsa kan yadda farashin fetur yake ci gaba da yin tashin gwauron zabi.

'Wannan karin ba alheri ba ne a gare mu domin gidajen mai za su kara farashin da suke sayar da kowace lita."

Kara karanta wannan

Tinubu ya saka lokacin samun saukin sufuri bayan zama da gwamnoni

"Abin ba a cewa komai domin mu a nan wajenmu fetur ya kai N1,300 kaga kenan yanzu sai ya jiyo kamshin wajen N1,400 ko fiye da haka."

- Yusuf Ahmad

Matatar Dangote ta yi barazana

A wani labarin kuma, kun ji cewa matatar man fetur ta Dangote ta yi barazanar fitar da rarar fetur da take da shi zuwa kasuwannin ƙasashen waje,

Matatar ta bayyana cewa idan kasuwar cikin gida ba ta iya ɗaukar dukkan man da aka samar ba, za ta tilasta mata fitar da rarar man zuwa kasuwannin yankin da na duniya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng