Yadda Ake ciki a Kasar Nijar da Sojoji Suka Yi Yunkurin Yi wa Tchiani Juyin Mulki
- Jami'an tsaron Nijar tare da taimakon dakarun kasar Rasha sun samu nasarar murkushe yunkurin juyin mulki a Niamey
- Shugaban mulkin sojan kasar, Abdourahamane Tchiani, yana ci gaba da rike madafun iko duk da luguden wuta da aka sha
- Yanayin fargabar da ake ciki na samar da dama ga kungiyoyin 'yan ta'adda na kara bazuwa a cikin Jamhuriyyar Nijar
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
M Malumfashi ya shafe shekaru 10 yana kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada
Niger - A ranar Asabar 29 ga watan Agusta 2026, sojoji suka nemi su yi wa gwamnatin Abdourahamane Tchiani tawaye a kasar Nijar.
Sai dai duk da hare-haren da sojojin suka kai filin jirgin sama na Diori Hamani da wasu wurare a Niamey, ba su canza gwamnatin kasar ba.

Source: Getty Images
Sojoji sun kai hari a kasar Nijar
New York Times ta rahoto an kai wa har Fadar shugaban kasa hari wanda hakan ya yi sanadiyyar dakatar da shirye-shiryen rediyo da talabijin.

Kara karanta wannan
Halin da ake ciki a Nijar bayan harbe harben sojoji da fargabar shirin juyin mulki
Ma’aikatar tsaron kasar ta fitar da jawabi tana cewa an shawo kan boren da wasu sojojin tawaye suka fara tun kusan karfe 1:00 na tsakar dare.
Nijar: Yunkurin juyin mulki ya yi nasara?
Rahoton Premium Times ya bayyana cewa duk da sojoji sun sanar da hambarar da gwamnati, hare-haren nasu bai kai ko ina ba a yanzu.
An fahimci gwamnatin Abdourahamane Tchiani ta nemi agajin dakarun Rasha wajen ganin ba a iya shirya wani juyin mulkin a kasar Nijar ba.
Beatrice Bianchi wanda mashawarciya ce a wata cibiyar tsaro a Dakar ta ce an kashe sojoji da-dama cikin masu neman kifar da gwamnati mai-ci.
Kasashen waje sun goyi bayan yunkurin juyin mulkin?
Wasu kasashen Afrika musamman wadanda sojoji suke mulkinsu a yau sun goyi bayan shugaba Tchiani da aka yi kokarin kifar da shi.
Ban da AES da ta yabi sojojin Nijar, gwamnatocin Turkiyya da Aljeriya sun nuna cewa suna tare da gwamnatin Abdourahamane Tchiani.
Su wanene suke son yin juyin mulki a Nijar?
I-Sahel ta ce ba a gama gane wadanda suka kitsa wannan yunkuri na juyin mulki ba, amma ana zargin cewa wasu kananan sojojin kasar ne.
Ana zargin Kanal Kimba Tahirou ya goyi bayan sojojin tawayen yayin da ake ganin akwai hannun Abdoulaye Idé wanda ya zama kyaftin a 2021.
Yunkurin zai ba bude wa 'yan ta'adda kofa a Nijar
Sojojin da suka tada kayar bayan sun fito ne daga yankunan Ouallam, Téra, and da Dosso inda ake fama da matsalar tsaro a Jamhuriyyar Nijar.
Sakamakon sojoji sun bar aikinsu sun tafi kifar da gwamnati, ana ganin wannan zai iya ba ‘yan ta’adda irinsu ISSP da JNIM damar yin barna.
Masana tsaro sun fara ankarar da gwamnatin Nijar wannan bayan ganin abin da ya faru kuma babu mamaki ba shi ne zai zama na karshe ba.

Source: Getty Images
Gwamnatin Nijar ta ce abubuwa sun dawo daidai
Jaridun kasashen waje kamar SABA a Yemen sun rahoto Ministan tsaron Nijar, Salifou Mody, yana cewa an yi maganin matsalar da ta taso.
Salifou Mody ya bayyana cewa abubuwa sun dawo daidai kuma kowa yana harkarsa.
Ana sa ran wannan ya kawo karshen zaman dar-dar da ake ciki tun da sojoji suka hambarar da gwamnatin Mohamed Bazoum a 2023.
Tafiye-tafiye zuwa kasashe sun ci N37bn a makwabta
A gida, an ji labari gwamnatin tarayya ta kashe N37.64bn wajen tafiye-tafiye a cikin shekaru 3, yayin da 'yan Najeriya ke fama da matsin lamba.
An kashe biliyoyi wajen sayen dalar waje, tikitin jirgi, da sauran bukatun tafiye-tafiyen aiki na gida da na waje a tsawon wannan lokaci a Najeriya.
Tafiya-tafiyen matar shugaban kasa, Remi Tinubu ya jawo an kashe Naira miliyan 700 a shekara guda.
Asali: Legit.ng

