Janar Abdourahmane Tchiani Ya Ayyana Kansa a Matsayin Sabon Shugaban Jamhuriyar Nijar

Janar Abdourahmane Tchiani Ya Ayyana Kansa a Matsayin Sabon Shugaban Jamhuriyar Nijar

  • Janar Abdourahmane Tchiani, wanda ya jagoranci dakarun tsaron fadar gwamnatin jamhuriyar Nijar wajen juyin mulki ya ayyana kansa a matsayin shugaban kasar
  • Janar din mai shekaru 62 ya zayyano matsalolin da ya ce kasar na fuskanta da suka kai su ga daukar matakin kifar da gwamnatin farar hula
  • Har zuwa lokacin da ya tuntsurar da gwamnatin shugaban kasa mai ci, Janar Tchiani ne kwamnadan rundunar tsaron fadar shugaban kasar tun daga shekarar 2015

Yamai, Jamhuriyar Nijar - A ranar Juma'a, 28 ga watan Yuli, Janar Abdourahmane Tchiani, ya ayyana kansa a matsayin sabon shugaban kasar Nijar bayan ya yi juyin mulki mai cike da takaddama.

Janar din wanda aka fi sani da Omar Tchiani, ya tuntsurar da gwamnatin farar hula a ranar Laraba, 26 ga watan Yuli, bayan dakarun tsaron fadar gwamnatin da yake jagoranta sun tsare shugaban kasar, Mohamed Bazoum, rahoton BBC.

Kara karanta wannan

Zaben 2023: Shin Da Gaske Kotun Daukaka Kara Ta Sanar Da Peter Obi A Matsayin Wanda Ya Lashe Zabe? Bayanai Sun Fito

Sabon shugaban kasar Nijar, Janar Abdourahmane Tchiani
Yanzu Yanzu: Janar Abdourahmane Tchiani Ya Ayyana Kansa a Matsayin Sabon Shugaban Jamhuriyar Nijar Hoto: ORTN - Télé Sahel / AFP
Asali: Getty Images

Abdourahmane Tchiani ya ayyana kansa shugaban kasa a Nijar

Tchiani, shugaban dakarun tsaron fadar shugaban kasar Nijar, ya ayyana kansa a matsayin shugaban gwamnatin rikon kwarya a kasar da ke yammacin Afirka, rahoton Al Jazeera.

DUBA: Shigo shafin Legit.ng na manhajar Legit.ng na Telegram! Kada ka bari komai ya wuce ka

Ya bayar da sanarwar ne a kafar talabijin ta kasar, yana mai cewa shine "Shugaban majalisar tsaron kasar".

Babban sojan mai shekaru 62 ya kuma ce ya zama dole su shiga lamarin domin gujewa mutuwar da kasar ke yi sannu a hankali.

Bugu da kari, Tchiani ya caccaki gwamnatin Bazoum na kin ba gwamnatin mulkin soja a Mali da Burkina Faso hadin kai wajen yakar yan ta'addan IS a yankin Sahel, rahoton DW.

Sojoji sun sanar da juyin mulki a jamhuriyar Nijar

A baya mun ji cewa dakarun tsaro sun cire Mohammed Bazoum daga kan karagar mulki a Nijar ta hanyar wani danyen juyin mulki da aka gudanar a ranar Laraba.

Kara karanta wannan

Jerin Sunaye: Gwamna Aliyu Ya Miƙa Sunayen Sabbin Kwamishinoni 16 Ga Majalisar Dokoki

An tattaro cewa wasu sojoji sun yi wa gwamnati tawage sun kifar da Shugaba Mohammed Bazoum.

A wata sanarwa da su ka fitar ta bakin Kanal Amadou Abdramane, sojojin sun sanar da cewa sun kawo karshen gwamnati mai-ci a kasar Nijar.

Abdramane shine ya karanto sanarwar a kafar talbijin na kasar tare da dakarun sojoji a kewaye da shi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng