Halin da Ake Ciki a Nijar bayan Harbe Harben Sojoji da Fargabar Shirin Juyin Mulki
- Sojojin Nijar sun ce suna “sake samun iko a hankali” bayan wasu sojojin tawaye sun yi garkuwa da jami’ai tare da bude wuta a sansanin soji
- An ji karar harbe-harbe a sassa daban-daban na Yamai cikin dare, musamman kusa da fadar shugaban kasa da filin jirgin saman kasa da kasa
- Ma’aikatar tsaron Nijar ta bukaci jama’a su kwantar da hankalinsu, su ci gaba da harkokinsu, yayin da sojoji ke kokarin shawo kan lamarin
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Niamey, Niger - Sojojin Nijar sun ce a ranar Asabar suna “sake samun iko a hankali” bayan wasu sojojin tawaye sun fara yin garkuwa da jami’ai a sansanin soji.
Sansanin yana kusa da filin jirgin saman babban birnin kasar, Yamai, inda aka kuma rika jin karar harbe-harbe a wasu sassan birnin.

Source: Getty Images
A cikin wata sanarwa da aka karanta a gidan talabijin na kasar, wadda Ministan Tsaro, Janar Salifou Mody ya sanya wa hannu, hukumomi sun bukaci jama’a, cewar Channels TV.
Shawarar sojoji ga al'ummar Nijar
Hukumomin sun bukaci jama’a da su “kwantar da hankalinsu, su ci gaba da harkokinsu cikin ’yanci”, yayin da jami’an tsaro ke kokarin dawo da zaman lafiya.
An ji karar harbe-harbe mai yawa a wasu yankunan Yamai cikin dare, musamman a tsakiyar birnin kusa da fadar shugaban kasa.
Haka kuma, an ji karar harbe-harbe a yankin filin jirgin saman kasa da kasa, inda ake da wani muhimmin sansanin soji.
An yi arangama a Yamai yayin da ‘yan tawaye cikin rundunar sojin Nijar suka yi yunkurin mamaye fadar shugaban kasa.
Wani mazaunin birnin ya shaida cewa an ji karar harbe-harbe mai tsanani da fashe-fashe a Base 101, wani babban sansanin soji da ke birnin Yamai.
Bana Wagana Ibrahim, mamba a Ofishin Majalisar Shawara ta Nijar kuma mataimaki a Majalisar Tarayyar Kasashen Sahel (AES), ya ce maharan sun kai hari sansanin Base 101, cewar Punch.
Ya sanar da cewa:
“Wani sabon hari na matsorata kan Base 101, kuma a wannan karon ma jami’an tsaronmu da sojojinmu sun tabbatar da cewa… lamarin yana karkashin iko."

Source: Getty Images
Matakin da hukumomin Nijar suka ɗauka
An dakatar da watsa shirye-shiryen gidan talabijin na kasar na tsawon sama da awa daya kafin a dawo da siginar da misalin karfe 10:00 na safe.
Nijar na karkashin mulkin sojoji tun shekaru uku da suka gabata, yayin da gwamnatin mulkin sojin ke fuskantar kalubalen dakile hare-haren ’yan jihadi.
Hare-haren ’yan jihadin sun addabi kasar Nijar da ke yammacin Afirka tsawon kusan shekaru goma, lamarin da ya jefa yankunan kasar cikin rashin tsaro.
Nijar da Mali sun dura kan Tinubu
An ji cewa Burkina Faso, Mali da Niger sun caccaki Shugaban Najeriya, Bola Tinubu, bayan ya alakanta matsalolin tsaron Najeriya da tabarbarewar tsaro a kasashensu.
Kasashen uku na ƙungiyar AES sun gayyaci jami'in diflomasiyyar Najeriya a Ouagadougou domin nuna rashin amincewarsu da kalaman Tinubu.
Ministan Harkokin Wajen Burkina Faso, Karamoko Jean-Marie Traoré, ya ce Najeriya da kasashen AES na fuskantar barazanar tsaro iri ɗaya.
Asali: Legit.ng

