Bazoum: Abubuwa 5 da ya kamata ka sani game da sabon shugaban kasar Nijar

Bazoum: Abubuwa 5 da ya kamata ka sani game da sabon shugaban kasar Nijar

A ranar 2 ga watan Afrilu, 2021, aka rantsar da Mohammed Bazoum a matsayin sabon shugaban kasar Jamhuriyyar Nijar.

Legit.ng Hausa ta kawo maku takaitaccen tarihin sabon shugaban kasar, wanda kafin yanzu ya rike kujerun da yawa a Nijar.

1. Haihuwa

An haifi Mohammed Bazoum ne a ranar farko na shekarar 1960. Hakan na nufin ya na da shekara 61 a Duniya.

Bazoum Balaraben yankin Diffa ne da ya zama shugaban kasa bayan ya samu nasara a zaben da aka yi a 2020.

2. Nigerien Party for Democracy and Socialism

Kafin ya samu mukami, Bazoum ya yi shugabancin ‘yan kwadago. Sannan ya rike shugaban jam’iyyar PNDS-Tarayya.

Bazoum ya yi aiki a karkashin ma’aikatar harkokin kasar waje a gwamnatin Amadou Cheiffou tsakanin 1991 da 1993.

KU KARANTA: An damke sojojin da suka yi yunkurin juyin mulki a kasar Nijar

3. Majalisa

A zaben Afrilun 1993 ne Mohammed Bazoum ya lashe kujerar majalisar tarayya, ya wakilci mazabarsa a jam’iyyar PNDS.

Bayan zaben 1996 sai aka daure Bazoum tare da shugaban kasar lokacin, Mahamadou Issoufou, daga baya ya sake koma wa majalisa.

4. Kujerar Minista

Mohammed Bazoum ya fara zama Minista ne a 1995, ya rike kujerar Ministan harkokin kasar waje na shekara daya zuwa 1996.

A 2011, Bazoum ya sake dawo wa gwamnati, aka kuma nada shi a matsayin Ministan harkokin kasar waje har zuwa 2015.

Bazoum: Abubuwa 5 da ya kamata ka sani game da sabon shugaban kasar Nijar
Shugaban kasar Nijar, Mohammed Bazoom Hoto: www.bbc.com
Asali: UGC

KU KARANTA: An rantsar da sabon shugaban jamhurriyar Nijar

Tsakanin 2015 da 2016, Bazoum ya zama karamin Ministan harkokin fadar shugaban kasa, a gwamnatin Issoufou.

Bayan Mohammed Issoufou ya zarce, Bazoum ya zama Minista cikin gida, tsaro, da sha’anin addini, ya yi murabus a 2020.

5. Zaben 2020

Bazoum ya yi nasara a zaben 2020, ya doke tsohon shugaban kasa Mahamane Ousmane a zaben da aka hana Hama Amadou takara.

Asali: Legit.ng

Online view pixel