Harin Kyamar Baki: Matakin da Tinubu Yake So ECOWAS Ta Dauka kan Afrika ta Kudu

Harin Kyamar Baki: Matakin da Tinubu Yake So ECOWAS Ta Dauka kan Afrika ta Kudu

  • Shugaba Bola Tinubu ya bukaci kasashen Afirka su hada murya wajen Allah wadai da hare-haren kyamar baki da ake kai wa baki a Afirka ta Kudu
  • Tinubu ya ce Najeriya ta kwashe sama da ’yan kasa 1,490 daga Afirka ta Kudu, tare da shirye-shiryen daukar karin matakai idan bukata ta taso
  • Shugaban ya jaddada goyon bayan Najeriya ga ECOWAS Compact, yana mai kira da a karfafa tsaro, dimokuradiyya da hadin kan kasashen yankin

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza ƙwararren edita ne a fannin nishaɗi, al'amuran yau da kullum, da kuma siyasa, wanda ke da shekaru sama da takwas a aikin jarida.

Saliyo - Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya bukaci kasashen Afirka su hada murya wajen yin Allah wadai da hare-haren kyamar baki (Afrophobia ko Xenophobia) da ake kai wa ’yan Afirka a Afirka ta Kudu.

Shugaban ya ce hadin kan kasashen nahiyar wajen yin tir da hare-haren zai aika da sako mai karfi ga gwamnatin Afirka ta Kudu cewa ba za a amince da irin wannan rashin hakuri da wariya ba ko ta wace hanya.

Kara karanta wannan

Tinubu ya kaddamar da manyan ayyukan tallafawa talakawa

Tinubu ya nemi ECOWAS ta taka wa Arika ta Kudu birki kan haren haren kyamar baki
Shugaba Bola Ahmed Tinubu a taron ECOWAS. Hoto: @ecowas_cedeao
Source: Twitter

Tinubu ya yi magana a taron ECOWAS

Tinubu, wanda Mataimakin Shugaban Kasa Kashim Shettima ya wakilta, ya bayyana hakan ne a Freetown, babban birnin Saliyo, yayin taron karo na 69 na shugabannin kasashen ECOWAS, in ji rahoton Arise News.

Ya sanar da shugabannin kasashen yammacin Afirka cewa gwamnatin Najeriya ta riga ta kwashe sama da ’yan kasarta 1,490 daga Afirka ta Kudu cikin zagaye bakwai domin kare rayukansu.

Ya kuma tabbatar da cewa Najeriya na shirye ta dauki karin matakai kan lamarin idan bukatar hakan ta taso.

Najeriya ta goyi bayan sabon shirin ECOWAS

Shugaban ya kuma bayyana cikakken goyon bayan Najeriya ga sabon shirin ECOWAS Compact for the Future of Regional Integration, yana mai cewa shirin zai kara karfafa hadin kai tsakanin kasashen yankin.

A cewarsa, shirin zai taimaka wajen sake gina amincewa tsakanin gwamnati da al'umma, tare da tabbatar da cewa hadin kan yankin ya ci gaba da kasancewa mai anfani duk da kalubalen siyasa da tattalin arziki da ake fuskanta.

Kara karanta wannan

Kasafin kudin 2026: Atiku ya zargi gwamnatin Tinubu da boye Naira tiriliyan 12.8

Tinubu ya ce ya kamata a tunasar da Afirka ta Kudu cewa kasashen Afirka, musamman Najeriya, sun taka muhimmiyar rawa wajen yaki da mulkin wariyar launin fata da ya ba kasar damar samun ’yanci.

Ya ce saboda haka bai dace a rika cin zarafin ’yan Afirka da ke zaune ko aiki a kasar ba, a cewar jaridar Punch.

Kashim Shettima ya wakilci Tinubu a taron ECOWAS
Mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima (farko daga hagu, a sahun baya) yayin da ya wakilci Tinubu a taron ECOWAS. Hoto: @officialSKSM
Source: Twitter

Kira kan tsaro da dimokuradiyya

Shugaban ya kuma bukaci kasashen ECOWAS su kara hada kai wajen yaki da matsalar tsaro da kuma kare tsarin mulkin dimokuradiyya a yankin.

Ya ce zaman lafiya, tsaro da bin doka su ne ginshikin ci gaba mai dorewa, yana mai jaddada cewa Najeriya za ta ci gaba da aiki tare da sauran kasashen kungiyar domin tabbatar da aiwatar da manufofin sabon shirin ECOWAS da kuma karfafa hadin kai a yankin.

Tinubu ya kuma sake nanata cewa Najeriya ba za ta yi kasa a gwiwa ba wajen kare dimokuradiyya, bin doka da kuma kin amincewa da duk wani sauyin gwamnati da ya saba wa kundin tsarin mulki.

An nemi soke lasisin MTN, DStv

A wani labari, mun ruwaito cewa, Sanata Adams Oshiomhole ya yi kira ga Gwamnatin Bola Tinubu da ta soke lasisin kamfanonin Afirka ta Kudu, musamman MTN da DSTV.

Kara karanta wannan

Tura ta kai bango: Mutanen gari sun aika sako ga Tinubu kan hare haren 'yan bindiga

Wannan kiran ya biyo bayan sabon harin ƙyamar baki da ake kai wa ƴan Najeriya a ƙasar Afirka ta Kudu, wanda ya jawo asarar dukiyoyi.

Sanatan ya jaddada cewa dole ne Najeriya ta mayar da martani mai tsauri domin kare mutuncin ƴan ƙasarta duba da yadda ake cin zarafin su a ƙasar waje.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com