Saudi Ta Yi Bayani kan Batun Yunkurin kai Harin Bam Dakin Ka'aba
- Gwamnatin Saudiyya ta musanta rahotannin da ke yawo cewa an kama wani ɗan kunar bakin wake da ya yi yunkurin kai hari a Masallacin Harami da ke Makkah
- Ma’aikatar Harkokin Cikin Gida ta Saudiyya ta ce jami’an tsaro sun kama mutumin ne saboda tsangwamar masu wucewa da kuma jawo firgici da tsoro a tsakanin jama’a
- Rahoton ya bazu ne bayan wasu bidiyoyi da aka wallafa a kafafen sada zumunta suka yi ikirarin nuna yadda jami’an tsaro ke kama wani da ake zargin ɗan kunar bakin wake ne
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf Kari yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Saudi Arabia – Gwamnatin Saudiyya ta musanta rahotannin cewa wani ɗan kunar bakin wake ya yi yunkurin kai hari a Masallacin Harami da ke birnin Makka.
Lamarin ya biyo bayan yaɗuwar wasu bidiyoyi a kafafen sada zumunta da suka yi ikirarin nuna yadda jami’an tsaron Saudiyya suka kama wani da ake zargin ɗan kunar bakin wake ne.

Source: Getty Images
Saudiyya ta fadi me ya faru
A sakon da ta fitar a X, Ma’aikatar Harkokin Cikin Gida ta Saudiyya ta ce jami’an tsaro sun kama mutumin ne saboda tsangwamar masu wucewa da kuma jawo musu firgici da tsoro.
Ma’aikatar ta ce an tunkari mutumin nan take a lokacin da lamarin ya faru, sannan aka ɗauki matakan shari’a da suka dace a kansa tare da miƙa shi ga hukuma.
Ta kuma jaddada cewa babu gaskiya a cikin ikirarin da ake yaɗawa cewa mutumin ɗan kunar bakin wake ne ko kuma ya yi yunkurin kai hari a Masallacin Harami.
Bidiyon da ya jawo rudani
Rahoton Anadolu ya nuna cewa bidiyon da aka rika yadawa ya samu dubban masu kallo, inda aka yi ikirarin cewa suna nuna wani ɗan kunar bakin wake da jami’an Saudiyya suka kama.
Masu yaɗa bidiyon sun kuma yi ikirarin cewa mutumin ya yi yunkurin tarwatsa Ka’aba, wadda ke tsakiyar Masallacin Harami kuma ita ce cibiyar ibadar Musulmi a duniya.

Source: Getty Images
Sai dai Ma’aikatar Harkokin Cikin Gida ta Saudiyya ta ce babu gaskiya a cikin ikirarin, tare da yin kira ga jama’a da su riƙa samun bayanai daga majiyoyin hukuma.
Wannan lamari ya faru ne a lokacin da Saudiyya ke fuskantar hare-haren ƙungiyar Houthi da ke samun goyon bayan Iran daga Yemen, inda ake zargin ƙungiyar da kai hare-haren makamai masu linzami da jirage marasa matuƙa kan Saudiyya.
Jirgi ya sauka a Saudiyya
A wani labarin, mun ruwaito cewa Ma’aikatar Harkokin Cikin Gida ta Saudiyya ta ce binciken farko kan saukar gaggawar jirgin Flydubai a Saudiyya ya nuna cewa an kai wa babban matukin hari.
Jirgin Flydubai mai lamba FZ1073 yana kan hanyarsa daga Dubai zuwa Tel Aviv lokacin da wani rikici ya faru a cikin ɗakin matuka.
Jirgin ya sauka lafiya da fasinjoji 174 da ma’aikatan jirgi takwas, yayin da fasinjojin suka ci gaba da tafiyarsu da wani jirgin Flydubai.
Asali: Legit.ng

