Tinubu Ya Kaddamar da Manyan Ayyukan Tallafawa Talakawa
- Shugaban Najeriya, Asiwaju Bola Tinubu ya ce gwamnatinsa ta himmatu wajen ganin an kawar da matsanancin talauci a fadin Najeriya
- Ya ce sama da Dala biliyan uku za a kashe ta sabbin shirye-shiryen tallafawa manoma, 'yan kasuwa, 'yan gudun hijira da bangarorin lafiya da ilimi
- Gwamnatin tarayya ta ce ta riga ta tallafa wa gidaje miliyan 15 masu karamin karfi, lamarin da ya taimaka wajen fitar da mutum miliyan 7.5 daga talauci
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
FCT Abuja – Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya sake jaddada kudirin gwamnatinsa na raba Najeriya da matsanancin talauci.
Ya ce idan manufofinsa sun gama aiki, za a sau raguwar talakawan da ake da su a kasar nan wanda hakan zai fito da kwazon gwamnatinsa.

Kara karanta wannan
Fadar shugaban ƙasa: 'Tinubu ya fitar da mara 'da kunya, ya kamata a saka masa a 2027'

Source: Facebook
Jaridar Nigerian Tribune ta kawo labarin cewa Tinubu ya bayyana hakan ne ta bakin Ministan Kudi kuma Ministan Kula da Tattalin Arziki, Wale Edun, yayin kaddamar da manyan shirye-shiryen gwamnati uku a Legas.
Bola Tinubu ya kaddamar da ayyuka
Jaridar Vanguard ta kawo labarin cewa shirye-shiryen da aka kaddamar sun hada da NG-CARES, SOLID da kuma HOPE da ake sa ran zai taimaki jama'a.
A cewar shugaban kasar, shirye-shiryen za su taimaka wajen samar da ayyukan yi, bunkasa noma, fadada tallafin jin kai da kuma karfafa tattalin arzikin al'ummomi a karkashin ajandar Renewed Hope.
Tinubu ya ce:
"Waɗannan ba shirye-shirye kawai ba ne, alkawuran da muka cika ne. Mun yi alkawarin gyara tattalin arziki, tabbatar da tsaro da kuma zuba jari a rayuwar jama'a, kuma yau muna cika wannan alkawari."
Ya kara da cewa ci gaban tattalin arziki ba zai zama mai ma'ana ba idan bai inganta rayuwar talakawan da ake mulka a Najeriya ba.

Kara karanta wannan
Dubu ta cika: An cafke wasu yan ƙasashen waje kan zargin hannu a matsalar tsaron Najeriya
Tinubu ya magantu kan shirinsa
Shugaban kasar ya bayyana cewa sabbin shirye-shiryen sun kunshi zuba jari sama da Dala biliyan uku domin tallafawa kananan manoma, kanana da matsakaitan 'yan kasuwa, 'yan gudun hijira da kuma inganta harkokin lafiya, ilimi da shugabanci a matakin kananan hukumomi.

Source: Facebook
A karkashin shirin NG-CARES, gwamnatin tarayya tare da Bankin Duniya za su kashe Dala biliyan 1.25 domin bunkasa noma da kananan kasuwanci.
Shirin SOLID kuwa zai samu tallafin Dala miliyan 300 domin inganta rayuwar 'yan gudun hijira da al'ummomin da suka karbe su.
Sai kuma shirin HOPE, wanda zai samu Dala biliyan 1.5 domin inganta ilimi, kiwon lafiya na matakin farko da shugabanci a matakin gundumomi.
Shugaba Tinubu ya yi nadin mukamai
A wani labarin, mun wallafa cewa shugaba Bola Tinubu ya amince da naɗa mutane 26 a hukumomi da kwamitocin gwamnatin tarayya guda 10 domin inganta ayyukan gwamnatin tarayya.
Tsohon gwamna Ayo Fayose, ya zama shugaban Hukumar REA, yayin da Manjo Janar Junaid Bindawa ya jagoranci Hukumar Albashi, akamar yadda aka sanar a ranar Litinin 20 ga watan Yuli, 2026.

Kara karanta wannan
Kashin 'yan bindiga ya bushe, gwamnati ta ɓullo da dabarun yaƙi da ta'addanci a Najeriya
Fadar shugaban kasa ta bayyana cewa dukkan sababbin naɗe-naɗen za su fara aiki nan take bayan amincewar shugaba Tinubu domin a kara karfafa gudanar da ayyukan gwamnati wajen ci gaban kasa.
Asali: Legit.ng