Wata Sabuwa: An Samu Sabani tsakanin Najeriya da Amurka kan Wasu Na'urori da Aka Kwato
- Dakarun Sojojin Najeriya sun saba wa ikirarin Amurka cewa ta kwace wasu muhimman kayayyaki daga ‘yan ta’adda
- Hedikwatar tsaro ta ce gwamnatin Najeriya ce ta miƙa kayayyakin ga Amurka a wani bangare na aikin haɗin gwiwar tsaro
- Amurka dai ta yi ikirarin cewa ta kashe mayaƙan jihadi 199 a wani samame da ta kawo Najeriya tare da kwato wasu muhimman kayayyaki
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Abuja, Nigeria - Mai magana da yawun rundunar sojin Najeriya ya saba wa kirarin babban jami’in gwamnatin Amurka cewa dakarun ƙasar sun ƙwace tarin na’urorin tara bayanan sirri daga hannun ‘yan ta’adda a Najeriya.
Tun farko Amurka ta yi ikirarin cewa sojojinta ne suka kwace kayan daga hannun yan ta'adda, sannan suka fice da su daga Najeriya.

Source: Twitter
Daraktan Yaɗa Labarai na Hedikwatar Tsaro, Birgediya Janar Samaila Uba, ya shaida wa Premium Times cewa ba Amurka ce ta ƙwace na'urorin daga hannun ‘yan ta’adda ba.
Najeriya ta saba wa ikirarin Amurka
A cewarsa, gwamnatin Najeriya ce ta miƙa waɗannan kayayyaki ga Amurka a matsayin wani ɓangare na haɗin gwiwar yaƙi da ta’addanci tsakanin ƙasashen biyu.
Ya ce:
"Mu ne muka ba su kayayyakin. Wannan wani ɓangare ne na haɗin gwiwar tsaro tsakanin Najeriya da Amurka."
Wannan ne karo na farko da wani jami’in Najeriya ya yi bayani kan lamarin tun bayan da Amurka ta fara bayyana hakan.
Abin da jami'in Amurka ya faɗa
A ƙarshen watan Yuni, 2026, Mataimakin Mai Ba Shugaban Amurka Shawara kan Yaƙi da Ta’addanci, Sebastian Gorka, ya ce dakarun Amurka sun kwato na'urori masu tarin yawa daga ‘yan ta’adda a Najeriya.
Ya ce:
"Na ga yadda jami’anmu suka kashe mayaƙan jihadi 199 a hari guda, sannan muka kwato kayayyakinnsu da yawa."
Ya ƙara da cewa adadin kayayyakin da aka kwato ya hura nunki uku na duk wani irin abin da Amurka ta taɓa kwatowa daga abokan gaba tun bayan harin 11 ga Satumba, 2001.
Hare-haren da Amurka ta kawo Najeriya
Ko da yake Gorka bai ambaci sunan farmakin ba, bayanansa sun yi daidai da harin haɗin gwiwa da Najeriya da Amurka suka kai a watan Mayu, 2027, cewar rahoton The Cable.
A wannan farmaki ne aka kashe Abu Bilal al-Minuki, wanda aka fi sani da Abubakar Mainok, ɗaya daga cikin manyan kwamandojin kungiyar ISWAP.

Source: Twitter
Manyan jami'an gwamnatin Donald Trump sun sha amfani da wannan farmaki a matsayin hujjar nasarar yaƙi da ta’addanci a Najeriya.
Da aka tambayi Janar Uba dalilin da ya sa gwamnatin Najeriya ba ta sanar da jama'a cewa ta miƙa kayayakin ba, ya ce haɗin gwiwar tsaro tsakanin Najeriya da Amurka ba sabon abu ba ne.
Ribadu ya gana da tawagar Amurka
Rahoto ya zo cewa mai bai wa Shugaban Ƙasa shawara kan harkokin tsaro, Malam Nuhu Ribadu, ya gana da sabon Mataimakin Sakataren Harkokin Wajen Amurka mai kula da Afrika.
An gudanar da ganawar ne a Abuja a ranar Litinin 13 ga watan Yuli, 2026 domin ƙara ƙarfafa haɗin gwiwar tsaro tsakanin Najeriya da Amurka.
Ziyarar ta zo ne a lokacin da aka ake samun matsalolin tsaro musamman a Arewacin Najeriya inda yan ta'adda da yan bindiga ke kashe jama'a ba dare ba rana.
Asali: Legit.ng


