'Yan Bindiga Sun Sace Shugaban Makarantar Firamare, Suna Neman N30m Kuɗin Fansa
- Rahotanni sun nuna cewa 'yan bindiga sun sace shugaban wata makarantar firamare a ƙaramar hukumar Itesiwaju da ke jihar Oyo
- An ce masu garkuwa da mutanen sun nemi Naira miliyan 30 a matsayin kuɗin fansar shugaban makarantar bayan sun tuntuɓi iyalansa
- Yayin da aka samu bayanai kan sace shi, 'yan sandan Oyo sun tabbatar da faruwar lamarin tare da cewa ana kan kokarin ceto shi
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza ƙwararren edita ne a fannin nishaɗi, al'amuran yau da kullum, da kuma siyasa, wanda ke da shekaru sama da biyar a aikin jarida.
Oyo - Wasu 'yan bindiga sun yi garkuwa da shugaban makarantar firamare ta Nomadic da ke garin Igbojaye a ƙaramar hukumar Itesiwaju ta jihar Oyo.
Rahotanni sun nuna cewa masu garkuwar sun sace Kolawale Mathew Owoade, wanda aka fi sani da Onaiye, kuma sun nemi Naira miliyan 30 a matsayin kudin fansa.

Source: Getty Images
Yadda aka sace shugaban makaranta

Kara karanta wannan
Umahi: Ma'aikaciyar jinya ta mutu a gida Minustan Tinubu, an zarge shi da boye gaskiya
Bincike ya nuna cewa lamarin ya faru ne da yammacin ranar Asabar, 11 ga Yuli, 2026, tsakanin ƙarfe 5:00 na yamma zuwa 6:00 na yamma, kamar yadda rahoton The Cable ya nuna.
Ɗan wanda aka sace, Abiola Owoade, ya bayyana cewa mahaifinsa yana kan hanyarsa ta dawowa daga gona da ke Budo Aare lokacin da maharan suka yi garkuwa da shi.
A cewarsa, jim kaɗan bayan sace shi, maharan sun kira iyalan ta amfani da wayar shugaban makarantar, inda suka buƙaci a biya Naira miliyan 30 kafin su sake shi.
Ya kuma ce da misalin ƙarfe 8:20 na safiyar Lahadi, wata tawagar masu bincike ta gano babur ɗin mahaifinsa da aka jefar a cikin daji.
An roki jami'an tsaro su ceto shi
Abiola ya roƙi rundunar sojin Najeriya, 'yan sanda, Hukumar DSS, Hukumar NSCDC, jami'an tsaron Amotekun, mafarauta da 'yan sa-kai da su haɗa kai domin ceto mahaifinsa cikin ƙoshin lafiya.
Haka kuma, abokan aikinsa da sauran masu ruwa da tsaki a fannin ilimi a ƙaramar hukumar sun nuna alhininsu kan faruwar lamarin.
'Yan sanda sun tabbatar da sace malamin
Da aka tuntubi kakakin rundunar 'yan sandan jihar Oyo, CSP Olayinka Ayanlade, ya tabbatar da faruwar lamarin, kamar yadda jaridar Punch ta ruwaito.

Source: Original
Ya ce:
"Zan iya tabbatar muku cewa an yi garkuwa da wani manomi mai suna Mathew Owoade a gonarsa da ke Budo Aare. A halin yanzu jami'anmu na ci gaba da ƙoƙarin ceto shi, tare da kamo waɗanda suka aikata laifin."
Lamarin ya faru ne kwanaki kaɗan bayan jami'an tsaro suka kuɓutar da sama da ɗalibai 40 da malamansu, waɗanda aka sace daga makarantu uku a ƙaramar hukumar Oriire ta jihar Oyo bayan shafe kwanaki 56 suna hannun masu garkuwa da mutane.
An ceto daliban makarantar Oyo
Tun da fari, mun ruwaito cewa, Dalibai da malamai da aka yi garkuwa da su a ƙaramar hukumar Oriire da ke jihar Oyo sun shaki iskar 'yanci bayan kwanaki fiye da 50 a tsare.
Mai ba shugaban ƙasa shawara na musamman kan harkokin yaɗa labarai da dabaru, Bayo Onanuga, ne ya bayyana hakan a ranar Juma'a, 10 ga watan Yulin 2026.
An yi garkuwa da ɗaliban da malaman ne a ranar 15 ga Mayu, 2026, lokacin da wasu ɗauke da makamai suka kai hari kan makarantu uku a yankunan Esiele da Yawota na ƙaramar hukumar Oriire.
Asali: Legit.ng
