Zafi Ya Shiga Turai Yana Ta Kashe Mutane a Faransa da Sauran Kasashe
- Rahoto ya nuna cewa fiye da mutum 1,300 ne suka mutu a tarayyar Turai tun daga ranar 21 ga Yunin 2026 sakamakon zafi mai tsanani
- WHO ta bayyana cewa Turai ce nahiya mafi saurin ɗumama a duniyar yau, inda yanayin zafinta ke ƙaruwa fiye da sauran wurare
- A bayanin da masana suka yi, sun ce sauyin yanayi da dumamar duniya ne ke ƙara yawaita tsananin zafin rana a tarayyar Turai
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Faransa - Yanayin zafi ya karu a a nahiyar Turai da aka shiga lokacin bazara, inda tsananin zafin da ya fara tun farkon kaka ya haifar da cututtuka.
Rahoto ya nuna cewa an samu yawaitar mace-mace da kuma tangarɗa ga muhimman kayayyakin more rayuwa a wasu yankuna a tarayar Turai

Kara karanta wannan
Abu ya girma: An farmaki 'dan takarar shugaban ƙasa na jam'iyyar AA a wurin jana'iza

Source: Getty Images
Al Jazeera ta wallafa cewa a ranar Lahadi, yanayin zafi ya kai ma'auni 40 na Celsius a wasu yankuna na nahiyar, ciki har da Jamus, Jamhuriyar Czech da Poland, lamarin da ya shafi harkokin sufuri.
Jama'a sun mutu a Faransa
A Faransa, an ruwaito karin mace-mace 1,000 fiye da yadda aka saba tsammani sakamakon tsananin zafin rana da ya karu.
An kuma fuskanci guguwa bayan kwanaki ana samun matsakaicin zafin, yayin da a wani gari ya kai ma'auni 44 na Celsius.
Sama da mutum 1,300 sun mutu fiye da yadda aka saba tsammani a Turai tun daga ranar 21 ga Yuni, a cewar babban daraktan hukumar lafiya ta duniya (WHO), Tedros Adhanom Ghebreyesus.
A cikin wani saƙo da ya wallafa, ya ce Turai ita ce nahiya mafi saurin ɗumama a duniya, inda yanayin zafinta ke ƙaruwa sau biyu fiye da sauran sassan duniya.
An mutu a kasashen Turai
A Spain, wata mata mai shekaru 90 ta mutu a kusa da Bilbao bayan bugun zafin rana a cibiyar kula da tsofaffi, yayin da wani mutum mai shekaru 68 ya mutu sakamakon irin wannan matsala a Almeria a makon da ya gabata.
A Jamus kuma, Euro News ta ruwaito cewa aƙalla mutum bakwai sun mutu a wasu abubuwan da suka shafi tsananin zafin rana.
'Yan sandan Jamus sun ce aƙalla mutum biyu sun mutu a wasu wuraren shakatawa da mutane ke shiga ruwa saboda zafi a Berlin a ranar Asabar.
A wani lamari kuma, wasu mutane da ke cikin ƙaramin jirgin ruwa sun gano wani mutum a sume a tafkin Jungfernheideteich da ke wani filin shakatawa a yammacin Berlin.

Source: Getty Images
Me ke haddasa zafin rana?
Masana hasashen yanayi sun ce matsanancin zafin da Turai ta fuskanta a wannan watan ya samo asali ne daga tsananin rashin iska da ya mamaye yammacin Turai.
Ana ci gaba da samun wannan yanayi ne saboda wani tsarin yanayi da aka sanya masa suna bisa siffar harafin omega na Girkanci da yake samarwa a sararin samaniya.
A yanayi na yau da kullum, guguwar iska mai ƙarfi tana motsa tsarin yanayi daga yamma zuwa gabas a duniya. Amma idan omega ya samu, tafiyar iska tana rikicewa, lamarin da ke tara iska mai zafi a wuri guda.
Masana kimiyya sun ce sauyin yanayi da ayyukan ɗan Adam ke haifarwa na ƙara yawaita tsananin zafin rana tare da tsananta ƙarfinsa.
Turawa sun gana da Sanusi II
A wani labarin, mun kawo muku cewa tawagar tarayyar Turai ta kai ziyara ta musamman zuwa fadar mai martaba Khalifa Muhammadu Sanusi II.
Tawagar da ta je Kano ta hada da shugabanni da wakilan su daga kasashen Turai kamar Faransa, Spain, Jamus, Poland da sauransu.
Domin karrama su, Sarki Muhammadu Sanusi II ya yi wa bakin hawa na musamman a fadar shi tare da nuna masu wuraren tarihi na jihar.
Asali: Legit.ng

