Mataimakin Trump Ya Yi Tone Tone kan Isra'ila, Ya Gargadi Jami'an Netanyahu

Mataimakin Trump Ya Yi Tone Tone kan Isra'ila, Ya Gargadi Jami'an Netanyahu

  • Ana cigaba da samun baraka tsakanin Amurka da Isra'ila tun bayan yarjejeniyar tsayar da yaki da kasar Iran da aka cimma a kwanan nan
  • Wasu daga cikin jami'an gwamnatin Benjamin Netanyahu sun caccaki Donnald Trump suna nuna yarjejeniyar bata shafe su ba kwata-kwata
  • A wani taron manema labarai a fadar White House, mataimakin shugaba Trump, JD Vance ya gargadi jami'an Netanyahu kan sukar Amurka

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

America - Mataimakin shugaban ƙasar Amurka, JD Vance, ya yi kakkausar gargaɗi ga gwamnatin Isra'ila a ranar Alhamis kan sukar yarjejeniyar Donald Trump da Iran.

Vance ya nuna cewa Isra'ila ta nesanta kanta da yawancin ƙasashen duniya a cikin shekarun baya-bayan nan, kuma Amurka ce kaɗai babbar ƙawarta da ta rage mata.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sama da 100 sun kai hari a Plateau, an kashe jami'an tsaro

Benjamin Netanyahu da JD Vance
Benjamin Netanyahu a hagu da JD Vance a dama. Hoto: Getty Images
Source: Facebook

Kiran Vance ga 'yan Isra'ila

Rahoton Time Magazine ya nuna cewa JD Vance ya ce a yanzu haka kasashe da dama sun juyawa Isra'ila baya, Amurka ce kadai ta rage mata.

"Da a ce ni memba ne a majalisar ministocin gwamnatin Isra'ila, da ba zan soki ƙawata mai ƙarfi da ta rage mini a duk duniya ba,"

In ji Vance a ƙarshen wani taron manema labarai da aka gudanar a Fadar White House na kusan awa guda.

Wadannan kalamai sun kasance mafi bayyana a bainar jama'a na yadda alaƙar gwamnatin Trump da Isra'ila ta ƙara tsami.

Vance ya shafe mafi yawan taron ne yana kare yarjejeniyar da aka ƙulla da Iran kamar yadda Trump ya kare ta a taron da ya ce Faransa.

Isra'ila ba ta kasance kai tsaye a yarjejeniyar ba, amma yarjejeniyar ta tanadi cewa ƙasar za ta dakatar da hare-haren makamai masu linzami a Lebanon.

Benjamin Netanyahu da Donald Trump
Shugaba Donald Trump da Firaministan Isra'ila a Amurka. Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

A cewar wani rahoto, jami'an Isra'ila sun bayyana "babbar damuwa" game da yarjejeniyar. Wani mai ba Netanyahu shawara ya ce Isra'ila ba ta ɗauki kanta a matsayin wanda za ta daina kai hari Lebanon ba.

Kara karanta wannan

Isra'ila ta yi wa Trump kunnen uwar shegu, ta kaddamar da sababbin hare hare

Gargadin kasar Amurka ga Isra'ila

Da yake mayar da martani ga wadannan hare-haren kalamai, Vance ya nuna cewa kashi biyu bisa uku na makaman kare kai na Isra'ila Amurkawa ne suka ƙera kuma suka biya kuɗinsu.

"Duk wani a Isra'ila da yake tunanin babbar matsalarsa ita ce shugaban ƙasar Amurka, to ya kamata ya farka ya gane hakikanin abin da ke faruwa a ƙasarsa,"

In ji shi.

Ya kara da cewa:

"Saƙonmu ga Isra'ilawa, kamar yadda muke isarwa ga kowa, shi ne muna son wannan tsarin zaman lafiya ya kasance mai amfani a gare ku,"

In ji Vance.

Al Jazeera ta wallafa bidiyon Vance a shafinta na X:

Makamai: Donald Trump ya kare kasr Iran

A wani labarin, kun ji cewa shugaban kasar Amurka, Donald Trump ya kare shirin kasar Iran na mallakar makamai masu linzami da ke cin dogon zango.

Trump ya kafa hujja da cewa ba adalci ba ne a ce Iran ba za ta mallaki makaman ba alhali kasashen da ke kewaye da ita suna cigaba da samar da su.

Ya kuma bayyana cewa makamai masu linzami ba za su iya rusa kasa a lokaci guda ba, inda ya ce makamin nukiliya ne zai iya yin illa mai girma nan take.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng