"Yan Hassada ne"; Trump Ya Hasala kan Masu Sukar Yarjejeniyar Amurka da Iran

"Yan Hassada ne"; Trump Ya Hasala kan Masu Sukar Yarjejeniyar Amurka da Iran

  • Shugaban kasar Amurka, Donald Trump, ya yi martani kan masu sukarsa saboda yarjejeniyar da ya kulla da Jamhuriyar Musulunci ta Iran
  • Donald Trump ya bayyana cewa mutanen da ke ganin bai matsawa Iran ba, ba su san abin da ke zuwa yana dawowa ba
  • Kasashen biyu dai sun sanya hannu kan yarjejeniyar fahimtar juna domin kawo karshen yakin da aka fara a ranar 28 ga watan Fabrairun 2026

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

​​​​​​​​​​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Birnin Washington, Amurka - Shugaban kasar Amurka, Donald Trump ya mayar da zazzafan martani ga sukar da ake yi wa sharuɗɗan yarjejeniyar fahimtar juna ta samar da zaman lafiya tsakanin Amurka da Iran.

Shugaba Trump ya ce waɗanda ke tunanin bai matsawa Iran sosai ba ko dai “masu hassada, miyagun mutane ko kuma wawaye.”

Trump ya ragargaji masu sukarsa
Shugaban kasar Amurka, Donald Trump Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Shugaba Trump ya bayyana hakan ne a wani rubutu da ya yi a shafinsa na Truth Social a ranar Alhamis, 18 ga watan Yunin 2026.

Kara karanta wannan

Wata sabuwa: Iran ta yi watsi da tattaunawa da Amurka kan makamai masu linzami

Amurka da Iran sun rattaba hannu kan yarjejeniya

Kalamansa suna zuwa ne jim kaɗan bayan shugabannin Amurka da na Iran sun sanya hannu a kan wata takardar yarjejeniyar fahimtar juna mai sharudda 14 domin tsawaita tsagaita wuta, ciki da a ƙasar Lebanon da kuma sake buɗe mashigar Hormuz.

Yarjejeniyar ta nuna ɓangarorin biyu sun ɗauki alƙawarin ci gaba da tattaunawa domin cimma matsaya ta ƙarshe a cikin kwanaki 60 masu zuwa.

Hakazalika yarjejeniyar ta haɗa da tsarin dala biliyan 300 na sake gina Iran da kuma janye “kowane nau'i” na takunkumin Amurka da aka kakaba wa Jamhuriyar Musulunci ta Iran.

Yarjejeniyar ta sanya wasu suna cewa sharuɗɗan kamar sun ƙarfafa ikon Tehran ne saboda abubuwan da ke kunshe a cikinta.

Wane martani Donald Trump ya yi?

A martaninsa, Shugaba Trump ya ragargaji masu ganin cewa kamar yarjejeniyar ta fi yin armashi ga Iran.

“Waɗannan wawayen, waɗanda ke tunanin ban matsawa Iran sosai ba, alhali kuwa a daidai lokacin ne kasuwar hannun jari ta kafa sabon tarihi, kuma farashin mai yana ‘durkushewa’ ƙasa, ko dai masu hassada ne, miyagun mutane, ko kuma wawaye."

Kara karanta wannan

Trump ya yi maganar ci gaba da kai hari Iran duk da cimma yarjejeniya

- Shugaba Donald Trump

Kasuwar hannun jari ta Amurka kwanan nan ta sami sabon matsayi mafi ɗaukaka na tarihi, kuma farashin mai ya fayi ƙasa sakamakon labarin yarjejeniyar zaman lafiya ta Iran.

Shugaba Donald Trump ya soki masu sukarsa
Shugaban kasar Amurka, Donald Trump, a wajen yakin neman zabe Hoto: Donald J Trump
Source: Facebook

Matsayar Iran kan yarjejeniyar

Shugabannin Iran sun yi ƙoƙarin fassara yarjejeniyar a matsayin gagarumar nasara ta fuskar dabarun yaƙi da diflomasiyya, tashar CNBC ta kawo rahoton.

Shugaban kasar Iran, Masoud Pezeshkian, ya bayyana takardar yarjejeniyar a matsayin wata dama ta tunkarar matsalolin tattalin arziki da na siyasa na Iran, inda ya ce za ta iya taimakawa wajen samar da “duniya ta daban” a Iran da kuma Gabas Ta Tsakiya.

“Wannan takarda ce ta tarihi kuma saƙo ne da ya fito daga ƙwaƙƙwarar Iran: Za a tabbatar da zaman lafiya a ƙarƙashin inuwar girmama juna."

- Masoud Pezeshkian

Trump ya magantu kan sauya gwamnatin Iran

A wani labarin kuma, kun ji cewa Shugaban kasar Amurka, Donald Trump, ya yi maganar cimma nasarae sauya gwamnatin kasar Iran.

Kara karanta wannan

Yadda cimma yarjejeniya da Iran a yaƙi ya kara fito da raunin Amurka a fili

Shugaba Donald Trump ya bayyana cewa gwamnatinsa ta cimma nasarar gwamnati a Jamhuriyar Musulunci ta Iran.

Trump ya ƙara da cewa da zai iya ci gaba da yaƙin, amma ba ya son ganin an samu koma baya ta fannin tattalin arziki.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng