Iran: Mayakan Houthi Sun Hana Jiragen Isra'ila Wucewa Ta Tekun Maliya

Iran: Mayakan Houthi Sun Hana Jiragen Isra'ila Wucewa Ta Tekun Maliya

  • Mayakan Houthi na Yemen masu alaƙa da Iran sun ce a ranar Litinin za su haramta zirga-zirga ga jiragen ruwan Isra’ila a Tekun Maliya
  • Tun da fari, mayakan Houthi masu samun goyon bayan Iran sun harba rokoki zuwa Isra’ila amma ba a samu rahoton barnar da ya yi ba
  • Mai magana da yawun rundunar Houthi, Yahya Saree, ya sanar da cewa haramcin zirga-zirgar jiragen ruwan Isra’ila a Tekun ya fara aiki

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Yemen - Mayakan Houthi masu samun goyon bayan Iran a Yemen sun ɗauki alhakin harin makami mai linzami da aka kai a safiyar yau a Tsakiyar Isra’ila.

Biyo bayan kai hare-haren, mayakan Houthi sanar da cewa za su hana jiragen ruwan Isra'ila zirga-zirga a Tekun Maliya daga yau Litinin.

Kara karanta wannan

Yakin Iran: Trump ya ki goyon bayan Isra'ila, ya gargadi Netanyahu da Khamenei

Jirgin ruwa a Tekun Maliya
Wani jirgin ruwa da mayakan Houthi suka farmaka a Tekun Maliya. Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Wuraren da aka kai hari Isra'ila

Jerussalem Post ta wallafa cewa mayakan Houthi sun ce sun harba jerin makamai masu linzami da suka kai hari kan muhimman wuraren da sojojin Isra’ila ke zaune a yankin Tel Aviv.

A cewar IDF, an kakkabo makami mai linzami guda ɗaya da aka harba daga Yemen a safiyar yau ta hanyar kariyar sararin samaniyar Isra’ila.

An hana Isra'ila shiga Tekun Maliya

Baya kai hare-hare birnin Tel Aviv, mayakan Houthi sun kuma sanar da haramtawa jiragen ruwan Isra'ila zirga-zirga a Tekun Maliya

Times of Israel ta rahoto mayakan sun ce:

"Kuma za mu ɗauki duk wani motsi na maƙiya a matsayin halastaccen hari na soja.”

Sanarwar, wadda ta biyo bayan hare-haren rokoki, ta ɗauki alhakin hare-haren da aka kai tsakiyar Isra’ila, inda Yahya Saree ya ce:

“Bisa ka’idar haɗin kai da kuma martani ga hare-haren Isra’ila kan Lebanon, Iran da Gaza, rundunoninmu sun harba jerin makamai masu linzami kan muhimman wurare a ‘Jaffa da aka mamaye’.”

Kara karanta wannan

Asiri ya tonu: Isra'ila na amfani da farin sinadari mai guba a Lebanon

Yahya Saree na jawabi a Yemen
Kakakin Houthi, Yahya Saree. Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Halin da aka shiga a Isra'ila

Da safiyar yau, kararrawar gargadin hare-haren sama ta yi amo a manyan yankunan Isra’ila bayan mayakan Houthi da ke Yemen sun harba makami mai linzami zuwa ƙasar.

Wannan ƙarin tashin hankali ya biyo bayan matakin Iran na kai hari kai tsaye kan Isra’ila a ranar Lahadi, wanda Tehran ta ce martani ne ga harin da Isra’ila ta kai kan wuraren Hezbollah a yankin Dahiyeh na Beirut.

Bayan jerin hare-haren makamai masu linzami da Iran ta kai wa Isra’ila cikin dare, Houthi sun nuna cewa sun shiga yakin domin taya Iran kai farmaki.

Isra'ila ta yi amfani da guba

A wani labarin, mun kun ji cewa kungiyar Human Rights Watch ta ce amfani da sinadarin phosphorus da Isra’ila ke yi a Kudancin Lebanon na da hadari.

An bayyana cewa matakin yana jefa fararen hula cikin babban haɗari tare da taimakawa wajen tilasta musu yin gudun hijira babu shiri.

Human Rights Watch ta tabbatar da amfani da farin phosphorus da sojojin Isra’ila suka yi a akalla ƙananan hukumomi 17 a Kudancin Lebanon.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng