Gabbard: Babbar Jami'a a Gwamnatin Trump Ta Yi Murabus
- Shugabar hukumar tattara bayanan sirri ta Amurka, Tulsi Gabbard, ta dauki matakin hakura da ci gaba da rike mukaminta
- Tulsi Gabbard ta sanar da yin murabus daga mukaminta a cikin wata wasika da ta aika ga shugaban kasar Amurka, Donald Trump
- Shugaba Trump ya yabawa Tulsi Gabbard inda ya bayyana cewa za su yi kewarta kuma ta dauki matakin da ya dace
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
Birnin Washington, Amurka - Shugabar hukumar tattara bayanan sirri ta Amurka, Tulsi Gabbard, ta sanar da yin murabus daga mukaminta.
Murabus din Tulsi Gabbard ya kawo ƙarshen wa'adin mulkin wata zaɓaɓɓiya mai cike da cece-kuce wadda ta fito a matsayin mai saɓawa da Shugaba Donald Trump kan yaƙin Iran.

Source: Getty Images
Tulsi Gabbard ta sanar da murabus din ne a cikin wata wasika waddda ta sanya a shafinta na Facebook, a ranar Juma'a, 22 ga watan Mayun 2026.
Meyasa Tulsi Gabbard ta ajiye aiki?
Gabbard, ƴar shekara 45, ta ce tana ajiye aiki ne a matsayin shugabar hukumar tattara bayanan sirri domin ta kula da mijinta, Abraham Williams.
Ta ce za ta yi murabus din ne bayan da aka gano kwanan nan mijonta yana ɗauke da wani "nau'in cutar daji na ƙashi mai wuyar gaske da ba a cika gani ba."
"Yana fuskantar manyan ƙalubale a makonni da watanni masu zuwa. A wannan lokacin, dole ne na janye jikina daga aikin gwamnati domin na kasance a gefensa kuma na ba shi cikakken goyon baya a wannan yaƙi da yake yi."
- Tulsi Gabbard
Trump ya yabi Gabbard
Trump ya yabi Gabbard, wadda aikinta ya haɗa da daidaita bayanan sirri daga gagarumar hanyar sadarwa ta hukumomin leƙen asiri guda 18 na Amurka domin bayanan yau da kullum na shugaban ƙasa.
Shugaban na Amurka ya bayyana a shafinsa na Truth Social cewa:
"Tulsi ta yi babban aiki na ban mamaki, kuma za mu yi kewarta."
Shugaba Trump ya ƙara da cewa ta yi "daidai" da take son ta taimaki mijinta a yaƙin da yake yi da cutar daji.
Mataimakin jami'ar, Aaron Lukas, shi ne zai yi aiki a matsayin mai jiran gado na shugaban hukumar tattara bayanan sirrin, kamar yadda shugaban ƙasar ya ƙara da cewa.

Source: Facebook
Wasu mata sun bar gwamnatin Trump
Jaridar Vanguard ta ce Gabbard ita ce mace ta huɗu a cikin jerin fitattun mata da suka bar rukunin ministocin Trump a cikin watannin baya-bayan nan.
Trump ya kori shugabar tsaron cikin gida Kristi Noem a watan Maris, da kuma babbar lauyan gwamnati Pam Bondi a watan Afrilu. Ministar Kwadago Lori Chavez-DeRemer ta yi murabus a watan Afrilu a tsakiyar jerin badakaloli da suka taso.
Sai dai kuma, Fadar White House ta yi watsi da wani rahoto da ke cewa an tilasta wa Gabbard barin aiki ne.
Majalisa ta daga kafa ga Trump

Kara karanta wannan
Sanata zai rikita APC, ya yi watsi da sakamakon zaɓen fitar da gwani a Cross River
A wani labarin kuma, kun ji cewa shugabannin jam’iyyar Republican a Majalisar Wakilai ta Amurka sun soke kada kuri’ar da aka shirya yi domin takaita ikon yaƙin Donald Trump kan Iran.
An dauki matakin ne bayan alamu sun nuna cewa Republican za su iya faduwa a zaben saboda rashin halartar wasu ‘yan majalisa masu goyon bayansu.
Manyan shugabannin Democrat sun soki soke zaben, suna zargin Republican da kare gwamnatin Trump maimakon kare muradun al’ummar Amurka gaba daya.
Asali: Legit.ng

