‘Jamhuriyar Musulunci Ta Birtaniya’: Netanyahu Ya Yi Shagube ga da Ingila
- Benjamin Netanyahu ya kira Birtaniya “Jamhuriyar Musulunci ta Birtaniya”, yana sukar yadda ake ɗaukar rahotannin Isra’ila
- Ƙungiyar Yahudawa ta Birtaniya ta soki kalaman Netanyahu, tana cewa suna da haɗari, suna ƙara kyamar Musulmi da rarrabuwar kawuna
- Dangantakar Isra’ila da Birtaniya ta ƙara yin tsami tun bayan zuwan gwamnatin Labour, wadda ta ɗauki matakai kan makamai
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Abuja - Firaministan Isra’il, Benjamin Netanyahu ya kira Birtaniya “Jamhuriyar Musulunci ta Birtaniya”, a wani furuci da ya yi cikin fushi.
Majiyoyi sun bayyana cewa Netanyahu ya furta haka ne ga ɗaya daga cikin tsofaffin ƙawayen Isra’ila a Turai.

Source: Getty Images
Netanyahu ya yi wannan furuci ne a wani faifan bidiyo na podcast na Isra’ila mai suna Melech Blitzer Haim, wanda Al Jazeera ta bibiya.
Netanyahu ya yi shagube ga Birtaniya
A matsayin misali, Netanyahu ya ambaci marubucin Birtaniya Randolph Churchill, wanda ya yaba da yadda ya bayar da rahotanni masu kyau game da Isra’ila a lokacin yakin kwanaki shida na shekarar 1967.
Daga baya a cikin shirin, Netanyahu ya yi magana kan wani furuci da mataimakin shugaban Amurka JD Vance ya yi a shekarar 2022, cewa Birtaniya na iya zama ƙasar Musulunci ta farko mai makaman nukiliya.
Sai Netanyahu ya ce cikin izgili:
“Ku je ku nemo irin wannan a Birtaniya a yau, wadda za ku iya kira Jamhuriyar Musulunci ta Birtaniya.
“Wani ya ce ƙasar Musulunci ta farko mai makaman nukiliya za ta kasance Jamhuriyar Musulunci ta Birtaniya, muna tabbatar da cewa ba za a samu wata irin wannan a nan, a Iran ba.”

Source: Getty Images
Sukar da kalaman Netanyahu suka jawo
Kalaman Netanyahu sun jawo suka daga wata ƙungiyar Yahudawa ta Birtaniya da Ireland, wadda ta bayyana su a matsayin kalamai masu cike da ƙiyayya da rarrabuwar kawuna.
Rabbi Charley Baginsky da Rabbi Josh Lev, shugabannin haɗin gwiwa na Movement for Progressive Judaism, sun ce irin waɗannan kalamai suna da haɗari da rashin ɗaukar nauyi.
Sun ce:
“Firaminista Netanyahu ba ya magana ne a madadin Yahudawan Birtaniya. Kalmominsa ba sa wakiltar mu.”
Duk da cewa Isra’ila da Birtaniya suna da dangantaka mai ƙarfi tun tarihi, alaƙar gwamnatocin ƙasashen biyu ta ƙara yin tsami tun bayan da jam’iyyar Labour mai ra’ayin ci gaba ta karɓi mulki a Birtaniya a shekarar 2024.
A lokacin tsohon Firaministan Birtaniya Keir Starmer, ƙasar ta dakatar da tattaunawar yarjejeniyar cinikayya cikin ’yanci da Isra’ila, tare da dakatar da wasu lasisin fitar da makamai zuwa ƙasar.
Birtaniya ta kuma kakaba takunkumi kan wasu ministocin Isra’ila masu tsattsauran ra’ayi, ciki har da Itamar Ben-Gvir da Bezalel Smotrich.
A shekarar da ta gabata, Birtaniya ta shiga cikin ƙasashe irin su Faransa da Kanada wajen amincewa da Falasɗinu a matsayin ƙasa, cewar Times of Israel.
Netanyahu na shan matsin lamba daga Trump
A baya, kun ji cewa Amurka ta matsa wa Firaministan Isra’ila Benjamin Netanyahu ya yi magana game da ‘yan share-fage a Falasdinawa.
Majalisar Dinkin Duniya ta ce Falasdinawa 15, ciki har da yara biyu, sun makale a gidajensu bayan an katse musu ruwa da wutar lantarki.
Rahotanni sun ce sojojin Isra’ila sun isa wurin tare da cire tantin da ‘yan share-fagen suka kafa, yayin da ake ci gaba da takaddama.
Asali: Legit.ng


