Iran Ta Kara Shiri, Mojtaba Khamenei Ya Yi Wani Muhimmin Gyara ana cikin Yaki da Amurka

Iran Ta Kara Shiri, Mojtaba Khamenei Ya Yi Wani Muhimmin Gyara ana cikin Yaki da Amurka

  • Jagoran addini na kasar Iran, Ayatollah Mojtaba Khamenei ya nada Mohsen Rezaee da Mohammed Bagher Zolghadr manyan mukamai
  • Rezaee ya zama wakilin Mojtaba Khamenei a Majalisar Tsaron Jamhuriyar Musulunci ta Iran a daidai lokacin da ake yaki da Amurka
  • Zolghadr, tsohon mataimakin shugaban rundunar IRGC, ya zama mai ba Khamenei shawara kan harkokin siyasa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawonNshekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Iran - Jagoran addinin Iran, Ayatollah Mojtaba Khamenei, ya nada wasu fitattun mutanen da suka taka muhimmiyar rawa wajen kafuwar Rundunar Kare Juyin Juya Halin Musulunci ta Iran (IRGC) a wasu manyan mukaman siyasa.

Sanarwar nadin mutanen biyu, wadda aka danganta da Khamenei, ta fito ne ranar Lahadi, yayin da ake ci gaba da sauye-sauyen manyan mukamai a tsarin siyasar Iran.

Khamenei.
Jagoran addinin kassr Musulunci ta Iran, Ayatollah Mojtaba Khamenei Hoto: Anadolu
Source: Getty Images

Tashar Al-Jazeera ta ruwaito cewa daga cikin wadanda aka nada akwai Mohsen Rezaee, tsohon kwamandan IRGC, wanda yanzu zai wakilci Khamenei a Majalisar Tsaron Kasa ta Iran.

Kara karanta wannan

Mutuwa ta sake girgiza Najeriya, tsohon antoni janar ya riga mu gidan gaskiya

Mohsen Rezaee ya samu sabon mukami

Rezaee ya jagoranci IRGC daga shekarar 1981 zuwa 1997, lokacin da rundunar ke kara karfafa matsayinta a tsarin tsaro da siyasar Iran.

Baya ga aikinsa na soja, Rezaee ya taba shiga takarar shugaban kasar Iran sau uku amma bai samu nasara ba.

A zaben shugaban kasa na 2009, ya zo na uku da kashi 1.7 cikin 100 na kuri’un da aka kada. A shekarar 2013 kuma ya zo na hudu bayan samun sama da kuri’u miliyan 3.8 yayin da a 2021, Rezaee ya zo na biyu da kusan kuri’u miliyan 3.4.

Tun shekarar 1997 yake cikin membobin Expediency Discernment Council, wata babbar hukuma da ke taka rawa wajen sasanta sabanin da ka iya tasowa tsakanin hukumomin siyasar Iran.

A watan Maris din da ya gabata kuma Khamenei ya nada shi mai ba shi shawara kan harkokin soja.

Zolghadr ya zama mai ba da shawara

Kara karanta wannan

Saƙon da Bola Tinubu ya tura wa 'yan ɗariƙar Tijjaniyya a Najeriya da wasu ƙasashe

Khamenei ya kuma nada Mohammed Bagher Zolghadr a matsayin mai ba shi shawara kan harkokin siyasa.

Zolghadr ya rike mukamai daban-daban a manyan matakan IRGC tun bayan juyin juya halin Musulunci na Iran a shekarar 1979.

Daga shekarar 1997 zuwa 2006, ya kasance mataimakin shugaban IRGC, kafin daga bisani ya ci gaba da rike wasu manyan mukamai a tsarin tsaro da siyasar kasar.

Mohsen Rezaee.
Mohsen Rezaee tare da ministan harkokin wajen Iran, Abbas Araghchi Hoto: NurPhoto
Source: Getty Images

A watan Maris, an nada Zolghadr a matsayin sakataren Majalisar Tsaron Kasa ta Iran bayan kashe Ali Larijani da Isra’ila a wani samame.

BBC Hausa ta ce sanarwar ta kuma yaba da gudunmawar Mohammad Baqer Zolghadr, wanda zai sauka daga muƙaminsa na sakataren majalisar, tare da naɗa shi a matsayin mai ba da shawara kan harkokin siyasa.

Abin da Iran ta fada wa Amurka

An ji cewa mataimakin shugaban kasar Amurka, JD Vance, ya bayyana maganar da Iran ta sanar da Amurka kan mashigar ruwa ta Hormuz.

Vance ya bayyana cewa Iran ta sanar da Amurka cewa ba ta da wani shiri na kakaba kudin harajin wucewa kan jiragen ruwa da ke ratsa mashigar Hormuz.

Sai dai babban jami’in tsaron Iran ya ce Amurka dole ta sauya dabi’arta kafin a sake bude mashigar Hormuz.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262