Iran Ta Yi wa Trump Martani kan Neman Ganawa da Mojtab Khamenei

Iran Ta Yi wa Trump Martani kan Neman Ganawa da Mojtab Khamenei

  • Ministan harkokin wajen Iran, Abbas Araghchi, ya yi watsi da batun cewa jagoran ƙasar Iran zai gana da Donald Trump, bayan da Shugaban Amurka ya bayyana yiwuwar hakan
  • A ranar Laraba, Trump ya shaida cewa zai so ya gana da shi lokacin da aka tambaye shi game da yiwuwar ganawar, yana mai ƙarawa da cewa wataƙila za su gana a wani lokaci
  • Sai dai babban jami'in diflomasiyyar Iran ya nuna rashin yiwuwar hakan a wata hira da kafafen yaɗa labarai da aka watsa a daren Alhamis, yana mai cewa ba abu ne mai yiwuwa ba

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Iran - Kasar Iran ta yi martani ga shugaban Amurka Donald Trump kan neman ganawa da jagoran addinin kasar, Mojtaba Khamenei.

Trump ya nuna yiwuwar ganawa da Khamenei ne a lokacin da Iran da Amurka ke kai wa juna hare-hare duk da cewa sun tsagaita wuta.

Kara karanta wannan

Iran ta yi martani bayan Trump ya nuna sha'awar ganawa da Mojtaba Khamenei

Mojtaba Khamenei da Donald Trump
Donald Trump a gefen hagu da Mojtaba Khamenei a dama. Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Khamenei: Martanin kasar Iran ga Trump

Iran International ta rahoto cewa Ministan harkokin wajen Iran, Abbas Araghchi, ya yi watsi da kalaman Shugaba Donald Trump na cewa zai gana da Mojtaba Khamenei.

Ya ƙara da cewa ana ci gaba da magana da Khamenei ba tare da yankewa ba kuma ana karɓar umarninsa a lokacin da ya dace sannan a aiwatar da su yadda ya kamata.

"Mojtaba Khamenei yanzu shi ne jagoran Jamhuriyar Musulunci kuma yana da kusanci da tasiri sosai a ci gaban al'amuran ƙasar,"

In ji Araghchi kamar yadda CNN ta rahoto.

"Yana da cikakken iko a kan al'amura."

In ji shi.

Dalilin rashin bayyanar Mojtaba cikin jama'a

Ministan ya ce rashin ganin Mojtaba Khamenei a bainar jama'a tun bayan naɗinsa ya faru ne saboda dalilan tsaro da suka shafi yaƙin da aka dakatar tun ranar 8 ga Afrilun 2026 ta wata yarjejeniyar tsagaita wuta.

Kara karanta wannan

Farashin danyen mai ya ruguzo bayan Trump ya hana Isra'ila kai hari Lebanon

Sai dai duk da haka ya ce:

"Matakin biyayya da aminci da aka nuna wa jagoran da ya yi shahada yana nan daidai wa daida ga sabon jagoran juyin juya hali,"
Abbas Araghchi a yana magana a wajen wani taro.
Ministan harkokin wajen Iran, Abbas Araghchi Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Maganar da Trump ya ga Iran

Bayan maganar da ya yi a ranar Laraba, a ranar Alhamis, Trump ya nanata cewa a shirye ya ke ya gana da sabon jagoran Iran, Mojtaba Khamenei.

Ya ce za su gana idan hakan zai taimaka wajen cimma yarjejeniya da Iran:

"Ba wai ina son ganawa da shi ba, zan so mu ga ko za mu iya cimma yarjejeniya, kuma idan muka cimma yarjejeniya, yana yiwuwa in gana da shi. Ba ni da matsala da hakan,"

Iran ba kasar Venezuela ba ce

A wani labarin, kun ji cewa Shugaba Donald Trump ya ce ba zai tura dakarun musamman na Amurka domin kwaso tarin uranium daga Iran ba.

Ya bayyana cewa ya yi watsi da hakan ne saboda aikin zai buƙaci makonni a yankin da ake yaƙi kuma zai iya zama sanadin haifar da matsaloli.

Trump ya ce Iran ba kamar Venezuela ba ce, inda za a shiga, a ɗauki 'yan mintuna kaɗan sannan a fita lami lafiya ba tare da wani kalubale ba.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng