Babbar Magana: Trump Yana Son Ganawa da Mojtaba Khamenei na Iran
- Shugaban Amurka, Donald Trump, ya ce zai so ya gana da babban jagoran addini na Iran, Mojtaba Khamenei, a wata hira da aka wallafa ranar Laraba
- Trump ya ce yana son ganawa da shi, kuma mai yiwuwa za su gana a wani lokaci na gaba, inda ya ce ya danganta da yadda abubuwa za su kasance
- Trump ya ce Iran ta amince ba za ta mallaki makamin nukiliya ba, sannan ya ƙara da cewa Ayatollah na Iran yana da hannu a tattaunawar da ake yi tsakaninsu
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
America - Shugaba Trump ya ce yana sa ran zai gana da jagoran addinin Iran, Mojtaba Khamenei, kuma suna fahimtar juna sosai duk da cewa tattaunawar zaman lafiya tana fuskantar tsaiko.
Mojtaba, mai shekaru 56, bai fito bainar jama’a ba tun bayan fara yaƙi a ranar 28 ga Fabrairun 2026, bayan hare-haren sama na bazata da Amurka da Isra’ila suka kai.

Source: Getty Images
Maganar Donald Trump kan Mojtaba Khamenei
Shugaba Donald Trump ya yi magana kan yiwuwar ganawa da Mojtaba Khamenei ne a wata hira ta musamman da ya yi da jaridar New York Times.
“Yana da hannu sosai a lamuran kasar, babu shakka. Ina ganin suna girmama shi ƙwarai,”
In ji Trump game da Mojtaba, wanda rashin fitowarsa fili ta sa tattaunawar zaman lafiya ke tafiya a hankali ta hanyar saƙonnin jakadu.
Ya ce:
“Ban samu damar ganawa da shi ba... Idan za ka yarda da rahotannin da ake yadawa, an ce ya rasa sassa daban-daban na jikinsa,”
“Sun ce shi ne ke ba da amincewa, domin haka aka saba tun shekaru masu yawa. Amma da alama muna fahimtar juna sosai.”
Batun ganawar Trump da Mojtaba Khamenei
Da aka tambaye shi ko zai iya ganawa da Mojtaba, Anadolu Agency ta wallafa cewa Trump ya ce:
“Eh, ina son ganawa da shi. Ina son ganawa da kowa. Ina son ganawa da shi kuma mai yiwuwa za mu gana a wani lokaci, ya danganta da yadda komai zai kasance.”
Trump ya dade yana nuna goyon baya ga ganawa kai tsaye da shugabannin ƙasashen da Amurka ke saɓani da su, yana mai cewa irin wannan hanya na iya gina alaƙa da za ta sa ƙasar ta fi samun tsaro.

Source: Getty Images
A baya, shugaba Trump ya taɓa bayyana Mojtaba a matsayin “maras ƙarfi” kuma “wanda bai dace” ya jagoranci Iran ba.
Trump ya tsayar da yakin Iran
A wani labarin, kun ji cewa Shugaban Amurka Donald Trump ya sanar da manyan masu ba shi shawara a asirce cewa ba zai kawo ƙarshen yarjejeniyar tsagaita wuta da Iran ba.
Matsayar shugaban na nuna cewa yana iya jure ƙananan rikice-rikicen soja na makonni ko ma watanni domin kauce wa faɗaɗa rikici a Gabas ta Tsakiya.
Trump ya sha nanata cewa yana kusa da cimma cikakkiyar yarjejeniyar kawo ƙarshen yaƙi, wadda za ta sake buɗe mashigar Hormuz tare da rusa shirin nukiliyar Iran.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

